Hausa Novels and Stories

Idon Naira 2

Sponsored links

Ajiyar zuciya ta sauke a boye sbd takasa sabawa da wannan yanayin na Maryamah sbd rashin ko inkulan Maryamah yafi damunta akan na kishiyarta sbd ganin Maryamah itace Yar uwa kuma jinin abinda Zata haifa zatafi son kome Zata Haifa yasamu kauna da kulawa daga Yar uwarsu wadda Zata iya Zama kaman uwa a garesu tunda babban Yaya kaman uwa ko ubane.

Ta mayar da dubanta kan uwargidarta wacce sam ba ma asalin ƴar ƙasar bace daga can Cameron ya aurota shekaru ashirin da biyu da suka wuce, kuma Maryama kaɗai ta haifa masa bayan ita ba ta kuma haihuwa ba sai yanzu ne da ya aurota ita za ta sake haifa masa wata ƴar ko ɗan.

“Bismillah Hafsatu zuba abincin mana.”

Malam Adamu ya yi maganar idanunsa akanta waccce yasan ta kasance shiru shiru mara son haniya kyakykyawa bafulatanar asali da ya aurota daga jihar Adamawa Marainiya ce da ta rasa uwa da uba tun tana tsummar goyo a yanzu bata da wani cikakken dangi ko gata da ya wuce Malam Adamu dayake mijinta Kuma zai zamo uban yayanta.

Hafsah ta zuba tuwan ɗanyar shinkafa miyar kuɓewa ɗanya da Hadeeza ta yi (Wato Uwargidarta) Ta sanya hannu cikin robar ruwan da Malam ɗin ya wanke hannunsa a ciki ita ma ta wanke nata hannun tare da sanyashi cikin plate ɗin tuwan ta fara ci.

Shiru ya ratsa falon daga ƙaran fankar da ya fara gajiya da ya cika falon ba ka jin sautin komi sun yi tsit suna cin abincin babu me kallon kowa a tsakanin junansu sai Malam Adamu kaɗai da ya kan bi matan nasa da kallo yana takaicin yadda har yau gidansa ya rasa walwala da farin ciki kaman kowane gida sbd Hadeeza ta kasa haɗa kanta da Hafsatu domin duk irin kallon rashin Inkula da suke gwada mata yana sane da shi.

Maida kallonsa yayi kan Maryamah wacce zuwa yanzu ta ke matakin kammala karatun diploma ɗinta akan harkan kasuwanci da ta ke karanta wato (Business Administration)

Ya ɗauke idanunsa daga gareta yana jinjina kai ganin yadda gaba ki ɗaya ta juya musu baya tana cin abincinta a natse ko kaɗan bata so ma ta kalli direction ɗin da Abban nata suke zaune sabida kada ta damu kanta ta Kuma damesu,

Ta kasa gane dalilin rashin son kula da matar duk irin sanyin halinta da rashin kwaramniyarta da hakurinta duk da ko so daya gidan Basu taba ko gardamaba bare hayaniya sai dai tana yawan bai wa kanta amsa da cewa jininta ne bai haɗu da matar ba.

Maryamah ita ce ta fara tashi ta shige ɗakinta bayan ta kammala cin abincin Abbanta ya rakata da ido yana jinjina kai ba tare da ya ce komi ba Hafsatu ta miƙe da ƙyar sabida nauyin da jikinta ya fara sosai ta dubi su Malam Adamu da matarsa ta ce

“To Allah ya bamu alkhairy zan shiga daga ciki Malam,

Anty Hadiza Saida safe.

Malam Adamu ya bi ta da kallon ƙauna yana tausayin yadda ta riski rayuwarta a cikin gidansa ba tare da ta samu walwala da sakewa cikin iyalinsa ba ya ɗaga sautin muryarsa ya ce,

” To Allah ba mu alkhairy Hafsatu, Allah Ya tashe mu lafiya.”

Hadeeza kuwa da qaramin sauti itama ta amsa Tai Mata Saida safen kafin ta Dan daga murya ta kira Maryama don ta zo ta kwashe kayan zuwa kitchen.,

Abbanta ma kaman yanda ya saba Saida yakuma Yi Mata ‘yar nasiha akan su yaqi shedan su tsarkake zuciyoyinsu duk da yasan tana taimakon hafsatu da wasu ayyukan kamar yadda ta ke wa uwarta duk ranar girkinta,Zata tayata ayyuka da dama Amma Babu wata doguwar magana shiyasa itama hafsatu Bata takurawa Maryamah din da magana sbd tasan ko ahakan yarinyar tanada tarbiya sosai tunda ko kallon wulaqanci bare rashin kunya batai taba mataba.

Tana kwashe kayan ta kai madafin ta aje ta dawo ta wuce ɗan ƙaramin ɗakinta ta kwanta ba bacci za ta yi ba wayarta ta ɗauka Android me arhar kuɗi wanda Abban nata ya siya mata ta hau chatting sai wajen 11:30pm ta kashe wayar ta kwanta don tana da lactures ɗin safe 8 za ta bar gida.

Washe gari karfe takwas daidai Maryama ta fito cikin shirin fita makaranta tana sanye da riga da zani da suka amsa jikinta ta yafa mayafi me Dan girma sbd Maryamah ba laifi tanada ilimin addini sosai hakama tanada irin yanayi na rayuwar uztazan Yan mata.,

Baƙace Maryamah amma kyakykywace sosai tanada jiki Mai kyau da kyakkyawar fuskar Mai kyau itama.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button