Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 37

Sponsored links

Tsantsar ƙasaita da izzar mulki dake yawo a jininsa na ƙara masa wani irin kwarjini mai cika ido da barazana. A hankali ta ƙara ƙasa da kanta jin kamar yana nufota. Gareta ɗin ko ya iso fuskar nan ɗam-ɗam babu alamar yasan minene murmushi ma balle a kai ga dariya. Mug ɗin hanunsa da keta faman tururi da tashin ƙamshin haɗaɗɗen shayi na musamman ya ajiye a side drawer ɗin batare da yayi magana ba. Shayin ta ɗan kalla da sake maida kallonta gareshi cike da mamaki, dan ya ajiye baice komai ba ya bar wajen, bathroom ya shige, ta ɗan lumshe idanu batare data iya cewa komai ba. Babu abinda take buƙata sama da shayin a yanzu, dan haka ta ɗauka ta fara sha lokaci-lokaci tana atshawa ɗin a wahalce da duban hanyar bathroom ɗin. Tsahon mintuna biyar sai gashi ya fito yana faman sake tsuke face. Da sauri ta ɗauke idonta kamar bata gansaba itama, ta ajiye mug ɗin hanunta data kammala shanye shayin da ya zuba matan tana yaye duvet ɗin da take a ciki jin zufa na karyo mata tako ina a jikinta. Yunkurin sakkowa take a gadon dai-dai yana isowa gab da ita, hakan yasa ta dakata da miƙewar ta ɗan dubesa ta kauda kai. Idanu ya tsura mata kamar mai tunanin ta yanda zaice wani abu, kusan minti ɗaya ya ɗan yamutsa fuska cikin motsa lips da ƙyar yace, “ki shiga ruwa a bath….” ya haɗiye sauran a maƙoshi batare da ya ƙarasa ba. Sake ɗago ido tai ta kallesa, ganin nasa idanun a kanta sai ta tura baki kawai ta kauda fuska gefe sai kace wata ƴar yarinya.

(Taɓara) ya ayyana a zuciyarsa shima yana ɓata fuskar. Ƴan jin kanne yau a kusa, wanda dama ita su ta sani a zahiri. Bama ta taɓa kallonsa a jerin mutane masu sauƙi ba. Batare da sake cewa uffan ba kawai taji ya ɗan duƙo kanta, zabura tai baya, sai dai kafin tai wani yunƙuri ya ɗagata cak kamar wata ƴar baby. Yo akansa micece wata Iffah. Tsayayyen namiji ne fa ingarma da duban damtsen hannunsa kawai ya iya saka mai tsoro zawayi a wando. Baka gane hakan sai yana sanye da ƙananun kaya. Gaba ɗaya ta waro idanunta sai cikin nasa, da sauri taso kauda natan ya hana hakan ta hanyar sarƙesu. Sai kawai taji zafin zazzaɓinta na ƙaruwa ma…

“Ni dai ka daina kallona”.

Furucin ya fito cikin suɓutar baki tana laɓe fuska kamar zatai kuka, dan da gaske idanun nan nasa tsoro suke bata. Ta ɗan so bashi dariya, sai dai a zahirinsa babu ko alamar hakan sai ma sake tsuke face ɗin da yay bai kuma janye idanun nasa ba. Sai ma tafiya da ya farayi da ita a hankali. Rumtse nata ta samu nasarar yi da ƙarfi dan gaba ɗaya jikinta yamutsawa yake har zuciyarta na zallo a cikin ƙirji. Zabura tai da buɗe idanun nata a lokaci guda jinta cikin ruwa mai ɗumi sosai. Taja ajiyar zuciya da faɗin, “Wayyo Ummuna”.

Bai kulata ba ya ida ajiyeta a ruwan dake ta faman tashin ƙamshi na masifa, ga wani ɗumi mai ratsa ƙashi da ɓargo. Fuska a ƙwaɓe take duban kanta da yanda ya sakata ita da kayan gaba ɗaya cikin ruwan. Sai taji kamarma ta saki kuka kawai ta huta. Wannan wane irin kalar walaƙanci ne. Idan yace mata taje tai wanka kawai ai ya wadatar, amma yanzu gashi ya jiƙa mata kaya duka al’halin bata da yaƙinin wasu dan ta fahimci a sashensa take. Bai dai san tanai ba, dan tuni ma shi ya fice abinsa. Haka ta cire kayan a jiƙe ta ajiye a gefe, nutsa kanta ta sakeyi a ruwan tana mai lushe idanu kamshin ruwan da ɗuminsa na ratsata, ga yanda kumfar tai a sama ful-ful na wani irin ƙayatar da ita.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button