Hausa Novels and Stories

King Zaid Complete Hausa Novel 1

Sponsored links

Magic club hadadden club ne dake birnin London, yawanci bakaken fata ne (Africa) suke zuwa club din……waka mai sanyi ke tashi, mata da maza suna rawa…wasu kuma suna aikin shan barasa da wiwi da shisha, daga gefe kuwa dandalin chacha ne….Laila matashiyar budurwa ‘yar shekara ashirin da hudu ‘kwararriyar ‘yar chacha ce, a tarihin chacha na magic club babu wanda ya taba cinta, hakan yasa a kullum take alfahari da jin kanta ita din wata ce ta musamman……

Haka yau ma ya kasance ta biga chacha da mutane uku ta cinyesu, yanzu bigawa take yi da mutum na hudu, ‘Kawarta Chuchu na zaune gefenta tana kallon yadda wasan yake kasancewa

“I checked” Laila ta fada sannan ta biga katin ‘karshe…cikin tsananin farin ciki Chuchu ta ce wow, that is good my gal

Cikin alfahari Laila ta shiga fadin “waye kuma zai iya ja dani, Ko baku da zarra ne?”

Shuru babu wanda ya tankata yasa Laila ta mike tana tattara kudin data ci a chacha tana zubawa a jaka “Kawata tashi mu tafi, babu wanda yake da zarran biga chacha dani”

Tashi Chuchu ta yi…suna ‘kokarin barin wurin suka dakata

“Ki dawo mu biga wasa”

A hankali Laila ta juyo ta sauke kallonta a kan wani dan matashin saurayi da bai wuce shekara talatin ba, ya yi matukar haduwa fiye da tunanin mai karatu, dogo ne sosai, farine sosai kamar ka taba jini ya fito, bai da ‘kiba amma yana da kakkaurar ‘kirji, idanunsa masu dauke hankali, komai na Zaid na musamman ne

Sun kai wani lokaci suna biga wasa Zaid ya ce Check…sannan ya biga katin ‘karshe

Cak Laila ta sha jinin jikinta ganin Zaid ya ci chacha

Kowa a wurin mamaki ya shiga yi, nan aka shiga tafawa Zaid…. Zaid juyawa ya yi ya tafa da abokinshi Yusuf suna dariya

A take idanun Laila suka canza launi zuwa ja, ranta ya yi matukar ‘baci sosai

Kallonta Zaid ya yi yana smile sannan ya ce kin ga abinda nake fada miki ko, Zaid ba sa’anki bane, wasa ya ‘kare

A take Laila ta shiga cire tsarkarta na diamonds da dankunnayenta na diamonds ta zuba a tebirin chacha tana magana “Ka dakata, wasa bai ‘kare ba, ni kadai ce mai nasara a koda yaushe, babu wanda ya isa ya yi nasara a kaina”

Smile Zaid ya yi sannan ya ce Ina son mutum mai confidence, to muje zuwa

Nan suka shiga biga chacha a Karo na biyu….abin mamaki Zaid ya ‘kara lashe wannan wasan, Laila ji ta yi kamar ta hadiye rai ta mutu tsabar bakin ciki amma bata karaya ba, yanzu wayar hannunta ‘kirar IPhone15 ta saka inda a wannan karon ma Zaid ne ya ‘kara cinyewa

Yanzu aje makullin motarta ta yi tana kallon Zaid dake kallonta yana smile ta ce na fada maka ni ce mai nasara a koda yaushe, na saka mota ta, muje zuwa

Nan suka shiga biga wasa inda a wannan karon ma Zaid ne ya ‘kara yin nasara

Chuchu kallon Laila ta yi ta ce Laila ki bar wannan wasan, yau nasara bata tare dake, mu tafi kawai

Laila zubawa Chuchu idanunta da suka canza launi ta yi ta ce ban yarda da fadiwa ba, ba zan taba fadi ba, nasara na tare dani

Zaid ya ce yanzu me zaki saka, ta ‘kare miki, baki da wani abin daya rage miki, bari nasa a kawo miki barasa ki sha ko zaki ji sanyi a ranki

Cikin ‘bacin rai Laila ta ce akwai abin daya rage min na saka

“Na saka kaina, idan har a wannan karon ka yi nasara, na mallaka maka jikina, ka yi duk abinda ka ga dama dani”

Zaro ido Chuchu ta yi cikin tsoro tana kallon Laila ta ce kinsan me kika ce kuwa? Magana kike yi a kan jikinki….

“Eh na sani, Ina sane da abinda na ce”

Smile din mugunta Zaid ya yi yana ‘kara kallon Laila, sai yanzu ya fara tantancen yanayin halittarta…..ta hadu sosai, ‘karamin bakinta yake kallo mai matukar jan hankali sannan ya dawo kan ‘kirjinta, tsayayyun nonuwanta sunyi dai dai a cikin blouse din jikinta, lasar lebansa ya yi na ‘kasa, a lokacin wani sha’awarta ya shiga fisganshi

Nan suka shiga biga wasa, a wannan karon Laila ta dage sosai tana son ta yi nasara amma Zaid ya nuna mata bata kai inda yake ba a duniyar chacha

Zumbur Laila ta mike, hawayen da suka cika a idanunta suka shiga bin kan kumatunta, girgiza Kai ta shiga yi tana fadin “impossible, impossible”

Chuchu rike Laila ta yi tana fadin “Laila mu gudu”

Zaid na kallon Laila cikin tsananin sha’awa ya ce relax ‘yan mata, Karki tayar da hankalinki

‘Kokarin juyawa Laila ta yi zata gudu Zaid ya yi saurin rike mata hannu yana fadin “Ina zaki je kuma?”

‘Kokarin fisge hannunta ta shiga yi tana fadin “ni ka ‘kyaleni, an ce maka ni shasha ce da zan baka jikina?”

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button