Hausa Novels and Stories

Idon Naira 17

Sponsored links

Wannan rigimar itace babban qalubalen daya fara samun rayuwar maryamah Wanda kusan tashin hankalinta sabo yadawo Dan kuwa tasan badan Allah sukeson karban Aqeel dinba su rabata dashi sai Dan kawai su cinye dukiyar da mijinta yayi wahalar Tarawa iyalinsa karshe ‘danta yayi wulaqantacciyar rayuwa.

Wannan qalubalen shine yafara juya rayuwar maryamah datayi alqawari tareda sadaukar da kanta gurin tsare haqqinta Dana ‘danta Dan kuwa bazata Bari ‘danta yayi wulaqantacciyar rayuwaba indai har Allah yabarta da ranta da lafiyarta da ikonsa insha Allah zatayi yaqi ta kare haqqinsu.

Ahankali Maryamah tafara yawon duk garuruwa da inda dukiyarsu take Tana duddubawa da kanta sai personal assistant dinta da aka kawo Mata Dan kuwa dukiya ake magana a manyan gurare…

Tun lamarin na zuwar Mata da sauki har kanta yafara neman bugawa sbd Takoma ko sati hudu Bata iyayi a gidanta kullum Tana hanya a mota ko a jirgi musamman Lagos Wanda kusan can cibiyar kasuwancin Alh Asad din yake sbd acan yayi karatu Kuma yayi rayuwa.

Duk yanda take tsananin so da kaunar ‘danta Aqeel haka tanaji Tana gani ta hakura tabarwa Zainab shi Dan kuwa Shi Kansa Bata ganin kaunarta a idonsa irin yanda yakewa Zainab…

Batayi aureba bare tasan Yaya daukar cikin yake Amma takai stage dinda zata daki kirji ta sanar cewa daukar cikin da haihuwa ne kawai bataiba Amma Babu abinda kowace uwa zata nuna Mata akan rainon ‘da tun Yana zaninsa har girmansa.

Tayi bautar mahaifiyar maryamah,

Tayi ta maryamah da mijinta

Yanzuma gashi tanayin ta ‘danta Wanda shi tasa bautar ta yarda ta sadaukar da rayuwarta agurin wahalta Masa har tsufanta sbd tsananin son datakewa Aqeel din jinsa takeyi tamkar ‘dan data Haifa jininta.

Ba Aqeel kawai maryamah tabarwa Zainab ba hatta gidanta Dan kuwa kusan komai a hannun Zainab yake na kula da komai Amma a fannin wahala sbd kusan wani nauyi ne dayafi qarfinta aka Dora Mata.

Bata taba saurayi ko wani Wanda zai ganta yayi shaawar aurenta ko soyayya da ita sbd Bata wani fita tamkar a prison take Idan ta fita ko dai wani aikin wahalar aka aiketa taje tayi.

Zainab kuwa tuni tafara wuce tsarin ‘yan Mata budurwai sbd shekarunta dasuke gaba da baya ba Amma Babu wani cigaban dayazo Mata koda na barin bautane saima abubuwan dake sake cabewa rayuwarta Dan yanzu maryamah Sam Bata zama tayi dedicating rayuwarta itama gurin aikinta Dan kuwa yanzu tazama babbar mace Haj MARYAMAH ADAM ASADULLAH.

Aqeel bai taba Jin kaunar Mamin tasa (Zainab) ta ragu a ransaba duk girman dayakeyi.

Kullum shaquwa da kaunarta yake qatawa tareda dibbin tausayinta,

Tun baiyi girmaba lokuta da Dama idan yaga yada take figewa Tana fita hayyacinta agurin aikin wahalar gidan kullum alqawarinsa akanta shine”

“Mami idan na girma nayi Miki Alqawarin zan daukeki daga Nan na Gina Miki babban gida da mota da komaima da kikeso”

Murmushi kawai takeyi Mai ciwo aduk lokacinda ya fada Mata Hakan sbd batasan me kaddararsu ta tanadar musu a gaba ba Amma Zataso hakan ace Aqeel dinta ya girma suna tare,taga aurensa da ‘yayansa Dan ba lallai ita tanada nata rabon ‘yayanba da zataga nasu auren da yayan.

Shin meyasa ba shaquwa da kauna tsakaninsa da ita tabarwa Zainab komai nasa Wanda hakan yasa Zainab tamaye gurbin uwa agaresa batareda dukkaninsu sun Ankara da hakan ba.

Kwata kwata Hankalinta a kwance ya ke akan ɗan ta AQEEL din don zuwa yanzu ta gama yarda cewa duk duniya Babu Wanda zai iya so da kaunarsa da kulawa dashi sai Zainab

Wanda su Zainab da ‘danta Aqeel din har mantawa sukeyi da Bayan junansu sunada wasu ‘yan uwan ko mahaifiyar.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button