Hausa Novels and Stories

Idon Naira 12

Sponsored links

Alh Asad a lokacinda ya fahimci karatun Zainab din Yana rawa sbd tsallaken kwanakin zuwa saiya Dan tsaya Mata a wannan fannin ya saka dokar zuwanta makaranta duk kuwa aikin datakeyi ya soke Mata na lokutan zuwa makaranta dole Inna Karima tadawo yin wasu daga cikin aikin da ake biyan Dan tayi

Daga wannan lokacin tasamu Tana zuwa makaranta ba dauke Rana saida ayyukanta Kam Babu Wanda ya ragu suna nan yanda suke saidai kawai ace Allah ya kyauta

Alh Asad mijin Yar uwar tata ne kawai zatace yake kulawa da ita amatsayin Yar Adam Kuma jinin matarsa sbd duk wata kulawa da abubuwan buqata shine ya tsaya Mata kaman babban Yaya kokuma tace kamarma mahaifi sbd ya Isa haihuwarta.

Yanzu rayuwarta takeyi a natse cikin tawakkali da rungumar wannan rayuwar sbd ta Gama yarda da hakan shine tata rayuwar.

Sam Bata damuwa ko Jin takaicin yin Aiki ko daya yanzu haka zalika ma jikin nata ya saba da wahalar batajin komai yanzu saima sake nutsuwa datayi akan komai.

Sai da cikin maryamah ya shiga watanni shida sannan Maryamah din ta sama sauƙin laulayin da ta ke yi Dan haka yanzu wasu lokutan hidmar maryamah din da sauki

Cikin Maryamah Yana cika watanni bakwai haihuwar gaggawa tazo Mata qarshe aka haife cikin Babu rai

Babban tashin hankali suka shiga daga alha Asad din har maryamah da Yan uwansama musamman mahaifiyarsa Amma haka suka fawwala ubangiji suka dauki qaddara.

Bayan wata biyu takuma samun wani cikin ko wata biyu bai rufaba shima ya bare,

A qataice saida ta dauki ciki so hudu duk ana rasawa kafin takuma samun Wanda ko wata biyu be rufa da samuwaba mijinta ya tattarata suka tafi India acan tayi renon cikin qarqashin kulawar wani likita har saida cikin yakai wata bakwai suka dawo sbd dukansu sunfi shaawar haihuwa acin Yan uwansu.

Bayan tafiyarsu maryamah zainab ta kammala karatunta na secondary

Kuma tafiyar tasu wani nauyi ne me girma ya hau kanta Dan kuwa duk hidimar kula da gidan da duk Wanda yake gidan kanta dawo Dan kuwa Jin tayi kaman anbar Mata wata gagarumar Amana gashi Sam a duniya Bata kaunar abinda zaisa tayiwa ‘yar uwar tata laifi ko abinda zai Bata ranta sbd kaucewa damuwar abinda zaije ya dawo.

Lokacin da cikin Maryamah ya shiga watanni tara a lokacin ne Zainab haka kawai itama taji Ta kaunaci haihuwar anty Maryamah din da wuri musamman ganin yanda kusan kowa ya qwallafa rai a haihuwar da abinda zaa Haifa din.

Cikin na shiga wata Tara da sati biyu

Cikin dare naƙuda ya kama Maryamah Alh Asad ya wuce da ita zuwa asibiti bayan ta sha matuƙar wahala daf da asuba ta haifo yaronta me Kama da ita sosai kyakkyawa dashi Kuma lafiyayye babba dashi.

Ko kaɗan Zainab ba su san bikin da ake ba sai da safe da Maryamah ta kira wayarta ta shaida mata haihuwar tare da bata umurnin girka abincin breakfast da duk wani abinda ta ke buƙata ta sanar da ita cewa Alh Asad zai dawo su taho tare da ita zuwa asibitin sbd ba za a basu sallama sai zuwa can rana an sake tabbatar da lafiyarta da na Babynta.

Zainab sauke wayar daga kunninta tayi tana jin wani boyayyan farin cikin da tsawon wayonta batasan ta taba yinsaba

can ƙasan zuciyartata jin wani irin ɗokin son ganin yaron Maryamah tayi haka kawai duk da tasan ita dashi saidai hange Amma Zataso abata shi Koda so daya ne ta Dan dauka Dan tasan ba lallai tasamu nata rabonba kila Dan bataga alamar zata samu tata rayuwarba idan ba Allah ya riga ya nufa ba.

Aikin da Anty Maryamah din ta bada umarnin ayi tafara a tsanake kaman yanda tasan Anty Maryamah din na buqatar komai.

Tana gamawa ta harhada ta shirya komai tsaf taje tayi wanka ta shirya da sauri sbd kada ta saka megidan jira

Ta fito hanyar Palo dauke da kayan ta tsaya Tana jiransa har saida ya Gama komai ya fito daukeda wasu kayan na na babies cikin qatuwar paper bag.

Da sauri ta karba cikin girmamawa kanta a qasa aka saka mota tashiga gaban motar tareda driver a rakube kaman Yar Aiki shikuma maigidan Yana baya yanata amsa wayoyin Taya murna daga yan uwa da abokan arziki.

Isarsu asibitinma itace tayi ta kwasar kayan Tana kaiwa Tana dawowa ta dauki wasu ganin wahalar tai Mata yawa yasa Alh Asad din Karban Mata wasu kayan suka shigo ciki gabaki dayansu.

Yan uwan Alh Asad dinne cikeda dakin da Maryamah din take anata murna da farin cikin samun babyn

Bama kamar ‘yan dakinsu Alh Asad din dasuka fi kowa murna sai yawo suke da babyn a tsakanin junansu.

Daga nesa Zainab ta saukar da kyawawan idanuwanta akan babyn dake hannun mahaifinsa nade cikin farin tattausan bargon babys

Zuwan umma ko Maryamah kila batai farin cikin da Zainab tayiba saidai a iya zuciyarta ne Tunda batada kusancin dazata bayyanar Amma dai ita kanta umman taga murnar zuwanta a tattareda Zainab din

Itama Kuma ta yaba da yanda taga Zainab din na hidima sosai da kulawa da gidan Maryamah.

Haka dai ta ringa hidima Bata zaune Bata tsaye har saida akai suna aka watse kowa ya Kama gabansa.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button