Hausa Novels and Stories

Fulani Page 6 Hausa Novel

Sponsored links

Wata babbar kofa ya nufa mai kyau da kyalle kamar an am mata ado da zinari, ya kai farin hannunsa ya tura kofar ya shiga, sai ya tsinci kansa a wani matsakaicin corridor mai kama da karamin falo an cika ko’ina da na gurin da manyan fulawoyin na kasko da jan carpet.

 

Mikewa yai straight zuwa katon stairs din da ke gabansa, gabansa kawai yake kallo har ya haye sama, kofar farko ya fara turawa tun kan ta karasa budewa ya jiyo kukan dansa, hakan yasa shi hanzarin cira kafa ya shiga cikin falon mai kama da da wata karamar fadar turawa, a wannan falon kam komai na cikinsa blue ne idan ka cire farin fentin mai kawata ko’ina na gidan, ta bangare daya kuma wani gini ne akai a cikin gurin mai kamar swimming pool sai dai wannan anyi shi da dan yi tsayi, an masa kwalliya da kwaryar da kuma rudayi sai dawusu a samansu yana furzo ruwa gwanin sha’awa, a iya cikin gilashin ruwan ke tsawa ko kadan basa digowa kasa balle har su sauka.

 

Falo ne mai dauke da set din kujeru uku kujerun farko kanana ne an jerasu kamar kujerun dinning wato a zagaye, sai dan karamin tebur a tsakiya da kuma wani karamin carpet blue, na biyun su kuma manyan turkish ne masu daukar hankali, sai wasu daga can karshen falon su ma blue kamar dai sauran an zagaye gefen da su, su ma kuma suna da karamin carpet da center table.

 

A gaban falon kuma wani katon kirsten tv stand ne fari mai gloss fronts da haske blue, left and right na tv stand din matsakaicin show glass ne mai haske a ciki blue color an masa kwaliya da turaruka na alfarma masu kyau da tsada gwanin burgewa.

Ga wani katon plasma da aka kawata tv stand da shi kamar matanen ciki za su fito waje.

 

A dayan gefen kuma wani karamin madubi ne na aka manna mai dauke da gurin wanke hannu, yamma da falon kuma matattarar cin abinci ce mai zamam kanta wacce aka ware mata kofarta dabam kusa da wani katon freezer mai kofa biyu, a dinning area din ma akwai madaidaicin plasma wanda zai bawa duk wanda yake zaune a dinning din damar kallo.

 

 

Kofar da Umar ya shigo ce kawai gini a cikin falon sauran duka glass ne gwanin burgewa.

 

A dayan bangaren kusa da dinning akwai wata karamar kofar glass, shiga cikinta na sadarda mutum da wani kebantaccen guri mai dauke da set din karamin dinning har biyar an rarrabasu an jera ko wane set dabam da wani.

 

 

 

Ta backyard din mutum zai iya hango wanda ke tafe da kuma abunda ke gudana a harabar Masarautar sai dai ba zai bawa mutum damar hango bangaren mai Martaba ba, dama da shi kuma wanda ke tsaye a gurin zai iya hangon garden din dake bangaren Momy, shi ma kuma ganin mai shiga ko mai fitowa ne kawai mutum ke da damar yi ba wai komai da komai na cikin ba kasancewar garden din na da manyan itatuwa da katon Swimming pool a gafe na dutse…..

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button