Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 99

Sponsored links

Ya tambayi kansa batare da yasan ina zai kama ba har ya ƙaraso jikin motarsa ya shiga. Da ƙyar ya iya tuƙin zuwa waje, yana hawa titi ɗan nesa da gidan aka dakatar da shi akan cewar yay parking ta cikin bluetooth ɗin kunnensa. Hakan ba karamin taimako bane a garesa, dan a yanda yake jinsa tabbas zai iya kife kansa a titin ma gaba ɗaya……..

Babu kowa a ɗakin sai wani irin ƙamshi mai matuƙar saka jiki kasala da sanyin ac. Iffah ta lumshe manyan idanunta tana ambaton sunan ALLAH da sake buɗesu. (Kai kai kai duniya fa na inda take) ta ayyana a zuciya tana dire tray ɗin hannunta saman wani ɗan table dake gaban ƙyaƙyƙyawar kukera ta hutawa. (Dama ce fa wannan) ta zabura dalilin wancan furucin da zuciyarta ta ayyana. “Tabbas dama ce kam”. Ta maimaita a fili tana ɗan waige-waige a nutse cikin hikima kuma ɗan gudun kar ya zam akwai camara a ɗakin kamar yanda aka bazasu ta waje ko’ina a sashen. Adai iya dubanta babu kamar sauran ɗakunan data kwana, dan haka ta cire takalmanta cikin sanɗa ta nufi ƙofar toilet da zuciyarta ke raya mata yana ciki. Tabbas yana cikin kuwa dan jin motsin ruwa. Ta daga hannayenta sama alamar Alhamdullah sannan ta baro wajen. Da ma’ajiyar turarrukan sa ta fara, sai da ta gama ɗagasu ɗaya bayan ɗaya ta shinshina. Sam babu alamar irin wancan, cikin damuwa ta maida ta rufe badan zuciyarta ta wankesa da zargiba har yanzu. Dan ta gama haƙƙaƙewa aljanun tsafinsa ya tura suka ɗakkota a daren na jiya dan ya cika burinsa. Amma ALLAH ya hanashi sa’a shiyyasama taga ɗakin kaca-kaca kamar anyi dambe a cikinsa. Da alama sun gusar mata da hankaline shiyyasama bataji sanda aka ɗakkotan daga can ɗin ba.

 

Harta juya zata fita zuciyarta ta sake nata shawarar ta ɗan sake duddubawa ko zataga wani shaida da suke buƙata akansa. Cikin yanayin dai ɗan tsoro-tsoro na mara gaskiyar dake gudun a kamasa take ɗan buɗe-buɗen ta, sai dai abin mamaki idan ka cire turarrukan data gama dubawa, da wasu tarin books a cikin wata ƙyakykywan show glass, babu wani abu a ɗakin bayan kayan gado da na ƙawata adon ɗakin kuma. Sai kuma kayan barci kala-kala a cikin wani dogon gilashi shima alamar matsayin wadrub, sai dai kasancewar zallar gilashi komai ana gani fes dan duk rataye suke a jikin hanger ma.

Iffah da gaba ɗaya kanta ya kulle na mamakin ina kayan da yake sakawa? Da takalma? Su agogo dama duk wani nau’in kayan da yake ado dasu fa?. Dan acan ma sauran ɗakunan da ta kwana iya irin abinda ke anan ɗin kawai ta gani. Lallai dole akwai abinda yake buƙatar tayi nazari a kansa kenan? (Minene to?) Zuciyarta ta ayyana mata tare da katse tunaninta sakamakon jin wani masifaffen kamshin shower gel da tsumammun turarrukan wanka ƴan asali da bata taɓa shaƙar irinsu ba.

 

A ɗan firgice ta juyo, sai kuma ta sake juyawa da sauri tana mai rumtse idanunta da faɗin, “Wayyo ni Iffah” ta nufi ƙofar fita da matuƙar sassarfa tamkar zata kifa dan hatta da tsumar jikinta a bayyane take..

Shiko da komai ya faru dominsa babu alamar hakan ya damesa. Dan ko kallon inda take baiba tunda ya fito. Babu ma alamar yasan da ita a ɗakin tattare da shi. Amma abin mamaki sai gashi ya zauna a kujerar da table ɗin ke tare da ita, wanda kuma anan ne Iffah ta ajiye shayin nasa. banbancin ɗanɗano da wanda ya saba sha kamar ɗazun ya sakashi yin tsamm da tsurama shiyin ido tamkar a cikinsa yake neman amsar sanin yaya hakan wai ke faruwa?. A zahiri ko babu wani abu a fuskarsa sai ma glowing da take irin na mai lafiyayyar fatar data jiƙu da hutu da jin daɗi. Yatsunsa biyu ya ɗan kai saman goshinsa ya murza kusan tsahon sakanni arba’in, kafin kuma ya janye yana mai ajiye kofin ya miƙe batare da ya sha ba. Ta can wajen gilashin da kayan barcinsa suke ya taka, hannunsa ya daura akan gilashin sai gashi gaba ɗayan drawer ɗin ta zuge a hankali ƙofa ta bayyana. Takawa yay ya shige, ta maida kanta ta zuge…

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button