Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 61

Sponsored links

Karo na biyu kenan da ta sake dawowa ɗakin ta samesa yana kai kawo rai a ɓace. So take taji miye damuwarsa, sai dai tana matuƙar shakkar hakan. Dan mijin nasu wani irin bahagon mutum ne da sam baida daɗin zama. Su dake tare da shine kuma kawai suka san hakan. Amma ga al’ummar masarautar kowa yabonsa yake, shiyyasa a lokuta da yawa idan suka kai ƙararsa ga Shahan-shan tun ma zamanin Tajwar Haysam sai kiga ana ganin laifinsu na gajen haƙuri da rashin godiyar UBANGIJI.

 

Hayaƙin Shishar da ya bulbule ɗakin da shi ta ɗan saka hannu ta kore, dan shi kansa ma da ƙyar take iya hangosa. Ƙundunbalar shiga tayi dan so take ta sanar masa kiran da aka aiko ana masa da ga Shahan-shan, amma tsoro takeji ganin yanayin da yake ciki. Muryarta na ɗan rawa ta risina da ga tsakkiyar ɗakin tana shaƙar hayaƙin madadin iska da ƙyar. “Barka da wannan lokaci Abu Husam”.

Cak ya tsaya da ga zuƙar Shishar, yay wani masifar bulbulo hayaƙin bakinsa da ya sake turniƙe ɗakin zuciyarsa na wani irin kumburowa da takaicin wace ƴar ƙunar baƙin waken ce a matan nasa data manta da dokarsa. Sai da hayaƙin ya lafa sannan ya iya ganinta da ƙyau, e ai ya sani sai ita ɗin, dan babu mai yawan shiga masa hanci kamarta. Tsawa ya daka mata yana miƙewa a fusace. “Buhaysah! Ban ce bana buƙatar ganin wani a sashe na ba da ga nan har sai idan nine na nema mutum?!!”.

 

A ɗan firgice ta zabura baya, sai kuma ta shiga girgiza masa kai jikinta na ƙyarma. “Hakane, amma Ka gafarce ni Abu Husam, wlhy bada son raina na karya maka doka ba. Saƙone da ga Shahan-shan ana buƙatar ganinka. Naga kada kai laifi ne shiyyas….”

“Tasss!!”

Kakejin saukar wani lafiyayyen mari akan ƙyaƙyƙyawar fuskar ta. Dan mace ce zankaɗeɗiyar gaske dirarriya. Duk da shekaru sunja gareta ƙyawunta a bayyane yake gata ƴar gayu. Ba yau ta saba shan mari a wajensa ba, amma sai na yau ɗin yay mata ciwo fiye da ko yaushe. A hankali ta ɗaga jajayen idanunta ta kallesa, fuskarta na nuna alamar ɓacin rai, abune kuma da bai taɓa gani da ga gareta ba.

“Abu Husam minene laifina anan da har na cancanci mari dan ALLAH?”..

“Ƙari kike buƙata kenan?”. Ya faɗa a zafafe da sake yunƙurowa zai sauke mata wani duk da jin wani shakkarta a yau ɗin da yaji ta shigesa.. Abin mamaki da firgici ga Miran Jasim, sai ga Buhaysah kam ta riƙe hannunsa caraf……Abune da bai taɓa faruwa ba a tsakaninsu, a tsahon shekarun da suka kwashe tare na aure talatin da ɗaya cif. Cikin ido take dubansa da wani irin kallo mai gigita zuciya “Jasim tsahon shekaru talatin da ɗaya kenan nake zaune a ƙarƙashin mulkin mallakarka. Nayi juriyar nayi kawaicin

amma na fahimci kai ɗin gafalalle ne da baya gane komai a rayuwarsa sai son zuciyarsa. A da dai na haƙurce maka na shanye, amma a yanzu zan tabbatar maka dai-dai nake da kai asararre kawai da ya girma bai san ya girma ba!”. Ta yarfar da hannunsa gefe da wulla masa wani irin mugun kallo ta juya zata fice. Wata irin zabura yay da ga sumar wucin gadin mamakinta daya riskesa, ya wani shaƙo wuyan rigarta ta baya ya fizgita jikinsa na rawa. Kiyyyyy rigar ta shiga kecewa, hakan yasata yin gaba. Tsabar shi cikakken mugune yasa ƙafa ya taɗeta. Mummunar buguwar da ta sakata ƙwalla wahalalliyar ƙara tai a ƙasan wajen. Cikin rufewar idanu yasa ƙafar ya taka mata gadon baya sai ga ƙashi na bada sauti.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button