Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 50

Sponsored links

Uffan bashi da alamar cewa, bai kuma canja da ga kallon da yake musu ba a zahiri. Suma sai duk sukai shiru, dan sun san halinsa sarai..

Bayan barowarsa daga sashen Malikat Bushirat ƙayataccen Gym ɗinsa mai ɗauke da nau’ikan machines na zamani ya nufa. Tuni hadimai masu tsaron wajen suka zube kan gwiyawunsu suna miƙa gaisuwa. Idanunsa kawai ya lumshe yay shigewarsa batare da yako kallesu ba. Da alama dai yau ƴan mulki ne bisa kai da miskilancin, ko kuwa maganar da yay da su Ammien tasa ne ke tsikarar masa rai oho dai. Sosai Gym ɗin ya ƙayatu ga mai kallo, dan hatta kaya motsa jikin an musu wadrube ne na musamman gasu nan iri-iri. Tattausar jallabiyar jikinsa ya cire ya ajiye, sannan ya fiddo set ɗaya na kayan ya ɗauka dogon wandon kawai ya saka. Sosai mutum ne buɗaɗɗe da baka gane hakan kai tsaye idan baya cikin riga. Cikin zafi-zafin da ke nuna kamar yana cikin fushi ya fara sarrafa machine ɗin gudun idanunsa a rufe ruf. Ya kwashe tsawon lokaci yanayi dan sai da yay sharkaf da zufa kafin ya kashe ya koma wajen ɗaga ƙananan ƙarfe irin na riƙewa a hannun nan ko kana daga zaune zaka ɗaga, duk da dai a zahiri kallon kitse akema rogo suna da matuƙar nauyi. Nan ma kusan mintuna goma sha biyar ya ajiye ya koma ɗaga ainahin ƙarfe daga kwance rigingine. Haka ya dinga caccanjawa har ya shafe tsahon awa biyu da wasu mintuna a ciki. Kafin yaja rigar wandon ya saka tare da ɗaukar goran ruwa ya kwankwaɗa yana sauke numfashi, dan shi ɗaya ke zuwa nan kawai bayan hadiman dake tsaren wajen. Ko amintaccen hadiminsa baya zuwa da shi.

 

Kamar yanda aka saba ya samu shayinsa na ƙa’ida a ɗakin da ya kwana, dan masu aikin girka abincinsa sun cigaba da aikinsu tare da amintacen hadiminsa. Zaman shan shayin yay yana mai shaƙar daddaɗan kamshin da ɗakin keyi na gyaran da ya sha harya kammala. Da ga haka ya nufi bayi tsaftace jikinsa. Ya kwashe lokaci mai tsayi anan ma kafin ya fito ya shige inda kayansa suke domin shiryawa

Masha ALLAH na ambata lokacin da yake fitowa cikin wata irin shiga ta alfarma. Ga wani ni’imtaccen ƙamshi na musamman da ya sake gauraye ɗakin cikin ƙanƙanin lokaci. Dubansa ya kai ga agogon ɗakin yana ɗan ɓata fuska. Yana da buƙatar zuwa ya duba yaya ta kwana. Ga shi kuma ya makara, dan yanada shari’ar da zai gudanar a fada yau. Batare da ya yanke hukuncin abinda ya dace yay ba ya fito cike da takun nan nasa na izza da ƙasaita tamkar mai tafiya a saman iska tsabar yanda yake wani ɗaga ƙafafun da sauke su a nutse. Fuskar nan tsam babu alamar yama san minene yaran murmushi. Har ya nufi hanyar da zata sada shi kai tsaye da falo ya ɗan dakata, gajeren tsaki ya ja da juyowa sannu a hankali ya doshi ɗakin da Iffah ta kwana.

Ƙamshinsa da sautin takun sawayensa da ke alamta isowarsa waje ya sata ɗan ɗago idanunta ta zubama ƙofar, sai kuma ta kauda da sauri ta cigaba da tsamar dabinon da aka zuba cikin zuma a wani ɗan farin bowl da ke a cinyarta. Kamar yanda yay sallamarsa ciki-ciki haka itama ta amsa masa can ƙasan maƙoshi batare da ta motsa da ga yanda take ba har ya iso tsakkiyar ɗakin.

“Barka da safiya”.

Ta faɗa kanta tsaye batare da ta ɗago ta kallesa ba, duk da kuwa tana matuƙar buƙatar hakan amma ta kwaɓi kanta. Maimakon amsa gaisuwar da tai masa sai ya jeho mata tambaya a bazata yana wani shanye idanunsa da ke binta da kallon ƙurilla.

“Kina jin wani ciwon ne a yanzu?”.

Idanunta ta ɗago sannu a hankali ta zubasu a kansa karo na farko. Gabanta yay wata irin mummunar faɗuwa ganin exactly kayan da tai mafarki da shi dai sune a jikinsa daren jiya da asubahin yau ne dai abin kamar wani almara. Sai dai kwarjinsa da wata barazanar cikar haiba ta cika mata idanun. Babu shiri ta maida nata ta rissinar zuciyarta na wani irin bugawa da sauri-sauri. Amma a zahiri ta wani sake tsuke fuskar ne kamar yanda tashi ke’a tsuke. Kanta ta girgiza masa maimakon amsa masa da baki.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button