Hausa Novels and Stories

Bakon Lamari 8

Sponsored links

“Amatuna mijin ki yaron kirki ne, Ki haƙuri ki zaman ki agidan ki, Allah ya ƙara muku zaman lafiya”

Gabanta ya faɗi Imran ya siye baba kenan da idan tazo gida da maganar zaman auren ta baba yana ƙoƙarin fahimtarta to shima yau Ga shi nan yana yabon Imran fiye da zaton ta.

Hawaye masu zafi suka Zubo mata a saman Kuncin ta bata bar kowa ya gani ba ta share su, Ta sunkuyar da kanta Baba ya cigaba da yi mata Nasiha mai ratsa Jiki.

Har wajan taran dare suna Gidan Kafin ta miƙe tace wa Ummah zata Leƙa sashin Matan Kawun nan ta su gaisa.

Ta Dubi Nana ƙanwarta wadda Daman su biyu ne mata ita da Nana sai Ƴan Biyu maza dake binta, Nana take bi musu, Tace mata tazo ta rakata Ɓarin su Ameerah su gaisa da sauran sashin Nana ta Tura baki tana cewa.

Ga Mamakin Amatullah Ummah batai wa Nana magana ba, Sai ma kuma jan hirar da tayi da Imran kamar ba surukinta ba.

Amatullah ta yi waje tana Jinjina halin ummanta na son abin duniya wanda shine jagora ga halin Ummah na farko.

Sashin Su Ameerah ta soma zuwa sukai gaisa da Anty babar su Ameerah sama sama.

Ta fito Ameerah ce ta rakata Sauran sassan ƙannan mahaifinta Guda Huɗu, Sannan suka Nufi sashin Su Yaya Ahmad wanda shine na farko ma daga ka shiga Gidan.

Mamaki sosai Amatullahi tayi yadda taga an ƙere sashin kamar ba’a cikin Gidanba ga hasken ƙwan sola kota Ina bata sha mamaki ba sai da ta shiga falon Mama wanda yaci uban saitin Kujeru masu kyau ga ƙatuwar Tv sai faman aiki take Iskar fanka kota ina.

Sallama sukai Ƙannen shi ƴammata Su Biyu Waɗanda basuyi aure ba suka amsa musu cikin sakin fuska Zama sukai a ɗaya daga cikin kujerun Sannan Surayyah autar su ta nufi Bedroom ta gayawa Mama.

Minti kaɗan Mama ta fito Cikin wata dakakkiyar shadda tana tafe tana taƙama.

A ran Amatullah tace ashe har yau Izzar tana nan.

Ba yabo babu fallasa suka gaisa sannan suka baro sashin wanda Naja’atu ƙanwar shi wadda suke sa’anni ta rakosu hanya.

Anan suka haɗu da Ƙanin Ahmad Kamal suka gaisa yana ƙoƙarin Shiga ɗakin shi.

Sai da su Ameerah da Naja suka rakata har bakin sashin su, sannan suka koma Ɓangarorin su.

Koda ta koma ma Imran har ya miƙe suna sallama da Ummah wanda ya ɗauko damin Kuɗi ya bata ta saka hannu ta amsa Jikinta har yana Ɓari Takaici Baƙin ciki sune suka wa Amatullah ca a zuciyarta.

Haka suka Nufi Mota yaja suka tafi ya biya Ta wani super market yayi mata uwar siyayyah.

A hankali Imran ya shigo ɗakin Jikinsa sanye da Guntun wando da singlet ya raɓa Jikinta ya kwanta aran shi yana ayyana tabbas Yau Burin sa zai cika Tabbas sai ya fitar da maitar shi ta san Neman ta tabayan ta.

A hankali ya haɗe jikinsa da nata yana shafo mazaunanta ta baya yana fitar da wani Irin nishi.

Cikin Baccin daya kwasheta taji yana shafa mata jikinta.

Tsoro fargaba tashin hankali sune suka dirar mata a zuciyarta mai Imran yake Nufi tsayin wata tara tana rayuwar gidan shi bai taɓa kusantarta ba sai sau ɗaya Tun daran farkon su, Kullum burin shi ya nemeta ta bayanta Allah bai bashi Iko ba shine yau ya ritsa ta a wannan daran zai ƙara far mata Innalillahi wa’innah ilaihirraju’un rana zafi Inuwa Ƙuna ta faɗa a ranta kafin da sauri kuma ta Miƙe zaune……..

*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za’a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button