Hausa Novels and Stories

Hamrah Hausa Novel Page 4

Sponsored links

a meeting hall d’in kuwa kowa shiru yayi yana jin yadda hamrah take zazzaga masifa “who the hell did he think he is? Ya ma isa duk abuja akwai wadda ya isa ja da ni, lallai se ya d’and’ana kud’ar shi se yay da na sanin wulakanta ni, se nayi sanadiyar barin shi aiki” gani tayi dukkan board of trustee d’in ba wadda ya iya magana kowa kanshi a qasa……..

Cikin jin haushi ta fice daga hall d’in ta nufi office d’in da babanta ke yawan zama sbd ya riga ya bar aiki taimakon ta kawai yake yawan zuwa yi, tana zuwa ta banka kofan ta shiga da sauri ya mike yace “daddy’s princess” ranta a ‘bace tace “daddy who the heck is that? Daddy he spoiled my mood”………

A natse daddyn yace “where is he?” Tace “he’s gone ko meeting d’in bamuyi ba” zaro ido yayi da sauri yace “kina nufin a meeting hall mutumin yake? Ya kamanninshi?” Cikin jin haushin yadda daddynta yayi sbd mutumin da kuma tunanin kyakywar fuskanshi da ya fado mata tace “I don’t know” da sauri ya d’auki landline ya danna wasu numbers……..

Yace “what happened at the meeting hall?” Bayani wadda ya kiran ya mishi da karfi ya kifa wayan tare da runtse idonshi yana bud’ewa har sun chanza kala ya kalli hamrah yace “Kin kashe ni hamrah” da sauri ta rike hannunshi hawaye na taruwa a idonta tana mugun son mahaifin ta sam bata had’a sonshi da kowa ba, sossai mamaki ya kama ta sanin mahaifin ta be ta’ba kiranta da ainihin sunanta ba se yau kafin tayi wani magana ya sake cewa……..

“Hamrah kin san kuwa waye Haisam mas’ood sa’ood? You ruined me hamrah innalillahi wa’innailaihi raji’un” tari ya fara sossai se jini ya biyo baya sossai hankalin hamrah ya tashi me ta aikata? Waye shi? Me yasa hankalin mahaifinta ya tashi haka? Hawaye ne suka gangaro mata kafin kace kobo mahaifinta ya fad’i kasa ba numfashi ihu ta kurma tana qiran “dad daddy no plz daddy” da gudu ta fita ta kira securities suka d’auke shi cikin gaggawa suka nufi “HMS specialist hospital, dake nan suke da NHIS d’insu”………..

Da sauri aka kar’be su aka wuce dashi emergency kuka sossai hamrah ke yi da sauri ta d’aga waya ta kira mommynta tana d’agawa ta kara karfin kukanta tana cewa “mo….. mmy……… M…. om…… my” ta kasa magana cikin tashin hankali mommyn tace “baby where are yhu, what happen where is your inhaler?” Numfashin hamrah ne ya fara tafiya duk kokarin da tayi na daidaitawa abun ya ci tura tun tana jaa a tsaye har ta fad’i da sauri securities d’inta sukayi kanta kowa na tambayar inhaler d’inta amma babu………

Kan kace kobo ta sume a take nurses suka nufe ta suka d’aga ta zuwa wani d’aki tare da kiran doctor don yi mata allura momynta jin yadda suke hayaniya yasa cikin tashin hankali ta kashe wayan ta kira d’aya daga cikin securities d’in yana dagawa ya mata bayanin abunda ke faruwa cikin mintuna se gata a asibitin a lokacin har asthman hamrahn ya sauka se kuka takeyi………

Da sauri momy ta karasa d’akin ta rungume ta tana lallashi da kyar tayi shiru tare da mata bayanin abunda ya faru ba tare da damuwa ba tace “ya sunan wadda kukayi hakan?” Shiru tayi alamun tunani tukun tace “wai haisam mas’ood sa’ood ne ko wa” zaro ido momy tayi tukun tace “hamrah ya ilahi” dafe kanta tayi cikin fusata tace “momy wai ni kam waye wannan guy d’in ne da kuke ta damuwa don na wulakanta shi? Haba dan Allah”……..

Jan hannunta momy tayi zuwa d’akin da aka kwantar da mahaifinta bayan fitowansu emergency se bacci yake yi cikin kwanciyar hankali zama sukayi kowa da abunda yake tunani…………….

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button