Hausa Novels and Stories

Zafin Kai 6

Sponsored links

Anne data fisu jiqata sbd ba zato tana barci taji saukan masifar tako ina gashi daman bata da lafiya kasa kuka tayi sai wani wahalallen numfashi datake saukewa tana daga kwance kanta na juyawa,

Sumayyah ma kusan kaman a sume take dan bata iya jan numfashi daidai cikin tsananin firgici da azaba take koina nata rawa yake ta qame guri daya idanuwanta a kafe da tsananin tsoron da tashin Hankali ina safnah ta gudu ta tafi tabarsu cikin masifar barnar data aikata dan kuwa har ranar da Allah zai yanke musu wannan wahalar sune zasu ringa azabtuwa da hukuncin wannan abin data aikata.

Benazir kuwa data fi sumayyah da Anne dakuwa sbd kusan itace ta ringa hawa samansu sbd dukan ya fi sauka akanta,bakinta jini yakeyi sosai ga gefen fuskarta ya kumbura a take kaman wadda mashin ya kade,

Wasu hawaye ne masu dumi da bayyanarda radadi da ciwon dayake cikin zuciyarta suka gangaro daga cikin idanuwanta ta rintse idanuwan a hankali tana kasa cewa komai dan kuwa a yanzu qaddararsu ita da ‘yar uwarta da mahaifiyarsu ta sauya ne zuwa wani yankin azabar da zatace safnah itace mummunar sanadin sauya musu rayuwa zuwa wata sabuwar wahalar da basusan inda zata kaisu ba.

Shiru dakin yayi tsit babu motsin kowannensu sbd babu mai iya maganar ko abin cewar,

Rawar da kakkarwan da jikin Annensu keyi sosai yasa Benazir da jikinta yayi tsananin tsami motsawa ta isa gurinta da qarfin hali sbd bakinta itama ya kumbura ya sauya kamanni sosai,

Kamo Annen tayi taji jikinta yayi wani irin zafi mai tsanani

Numfashi ta sauke a kasalance sbd rashin sanin abin yi amma kuma ko yayane dole zata rage mata ko zafin jikin ne dan haka ta miqe da qyar ta dafe cikinta dayasha harbi da qafafun Ababa din tana takawa ahankali ba kuzari ta fito ta debo ruwa a roba ta dawo ta zauna gefen Annen tafara goge mata jikinta da fuskarta da itama yaji mata ciwo gurin dukan.

Sai data gama goge jikin Annen taji sumayyah itama jikinta yayi zafi sosai har taja jijjiga dan haka itama ta dawo kanta ta ringa goge mata jikinta tana rungumeta sbd sumayyar tafi Anne jigata gashi daman rauninta yafi na Annen.

Daqyar benazir din tasamu jikin sumayyah ya dena fizga tana neman sumewa,

 

Kwantar dash tayi ta rufe kowannensu sbd baccin wahala dasuka samu ya daukesu.

 

Ajiyar zuciya mai zafi ta sauke a hankali tareda jinginar da bayanta jikin bango taba cusa kanta cikin qafafunta daga zaunen tana rintse idanuwanta sbd itama wani azababben zazzabi da tsamin jiki takeji mai radadi amma batada mai dubata bare bata kulawa dan haka a hakan baccin wahala ya dauketa.

Da sassafe itace tafara tashi tafara duba jikin nasu kafin ta miqe daqyar sbd jiki daya qara tsami ta fito tayi alwala tazo tayi sallah tana idarwa ta tada Sumayyah da itama jikinta ke tsananin ciwo da tsami ta fito daqyar tayo alwala tazo tayi sallar suna idarwa suka fito dan ayyukan dasuke dole akansu.

Da Ababa suka fara cin karo ya fito cikin farin yadi fuskarsa a hade tsaf babu sakewa bare rahama,

Da sauri dukkaninsu sukai qasa suka gaishesa cikin girmamawa da ‘da,a mai tsanani kansu a qasa.

Ko kallonsu baiyiba ya wuce kai tsaye dakinsu ya fada bai tsaya komaiba ya damqo Annensu dake zaune tana rarraba ido cikin azaba ya fara janta ya fito da ita yana cewa

“Zamanki a nan ya qare sbd daman na fada muku tana bayyanarda haukarta ta gama zama a nan bolar mahaukata zan kaita tabi mahaukata yan uwanta can su qarata a bola bola”

A tare Benazir da sumayyah suka zube qasa gabansu suna wani irin hawayen mafi munin tashin hankali suna rokonsa akan karya rabasu da mahaifiyarsu.

 

Ko sauraronsu baiyiba sbd basu kai matsayin da zaiji ko rokonsuba, sake jan uwar tasu yakeyi wadda take riqe Benazir da qarfi kaman ranta duk da hankalinta bai gama dawowa daidaiba dika tasan su din yayanta ne da bazata iya rabuwa dasuba ba koda zaa rabata da ranta ne tafison a rabata dashi a tana tare da su.

Sumayyah kuwa a neman rasa kanta takeyi sbd itama qwaqwalwan tata neman juyewa takeyi da uwa da ake kokarin rabasu da ita dan haka ta dunqule guri daya tana kasa motsawa sai fizga da kanta keyi.

Benazir data ke neman zaucewa itama kuka ta fasa mai qarfi tareda rarrafawa ta riqe qafafunsa tana rokonsa cikin qasqantar da kai tana masa Alqawarin yin duk abinda yakeso na ‘yan uwanta dasuka tafi samirah da safnah indai zai bar musu Annensu koda bangaren dabbobinsa ne sun yarda zasuyi duk abinda yakeson harda nasu safnah data gudu da samirah data rasu.

A yanzu daya dauki wannan tsarin sai haukarta dake hawa tana sauka tayi masa daidai,

Ya zauna ya tsara sabon lale ga rayuwarsu gabaki daya ta hanyar miqasu ga auren jari ga wasu dilolin miyagun qwaya da masu safarar mutane da ya samu amma sam hadin bazaiyi ba saiya wadatar dasu da ilimin boko mai dan zurfi dan haka kai tsaye ya fidda kudi aka nemar musu gurbin karatun diploma wanda yafi wata yana lissafin kudin dazai kashe kafin yakai ga maida kudinsa yana jinjina maqudan dukiyar da zai samu daga manyan dealers din na qwayoyi da akace suna sakarwa matayensu da iyayen matansu.

Ita benazir kai tsaye Wani hamshaqin drugs dealer dake zaune a lagos da qasar Germany ana tallata masa hotonta yace ya amsa aurenta sbd dari bisa dari tayi masa dan haka ita take yafara yiwa Ababa barin kudi dan haka koda Ababan ya dawo dag lagos ita take aka sauya mata karatun da zatayi zuwa degree.

Cikin saa Tana rubuta jamb taci Admission dinta bai wani zama wahala ba sbd komai acikin saa ta rubuta taci.

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button