Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 147

Sponsored links

Suka fada cikin hada baki da hun murna. ALLAH ma ya sosu hadimai yau an basu freedom din kansu sai dai-daiku dakan dan shigo dan an bukaci ganinsu. To su sunama a falon Malikat Bushirat din nacan ciki ne iya su dan yau ranar baje kolin hirar zuminci ce. Wani irin diff-diff kirjin Malikat Bushirat keyi, zuciyarta kamar zata faso ta fito. Ga kanta da yay wani irin azababben sarawa, sai ta fara ganin falon na juya mata da su da ke ciki. Tashi tai da sauri ta nufi daki ta kulle kanta. Tana gama sakama kotar key ta daura goshinta jikin kofar tai wani irin fashewa da kuka mai tahowa irin gaba dayan nan mutum yaji kamar numfashinsa zai bar gangar jikinsa.

Bama su fahimci halin da take cikiba su balle tashinta, sunata murnarsu, sai da mai bima Malikat Bushirat din ta juyo tana magana idonta ya sauka a wajen zamanta wayam. Bata kawo komai a ranta ba a tunaninta duk murnarce ta kebe yin abunta dan sun san yar war tasu da shegen kasaitar son mulki kamar itace Shahan-shan din ba matarsa ko uwa ba

*A bangaren Iffah kam tana sashan Malikat Haseenat, taso ta samu Iftihal dan yau tayo mata tanaji sai dai aka samu rashin sa’a wai ta fita ita da Husam babban dan Miran Jasim. Anan ma Iffah ta jima sai bayan sallar la’asar ta baro, sunata shan hirarsu ita da Mammah da Mammy. Daneen Waheeda dai bata saka baki sai lokaci-lokaci

Tattauna zancen cikin Iffah ga zuri’ ar Malikat Bushirat ya sa ya fito har ya fara yawo a cikin masarautar. Dan danan fa aka fara wani karamin bikin murna da sam Iffah da Tajwar Eshaan da sai da akai sallar la’asar ya samu kansa basu sani ba. Hasalima suna can manne da juna abinsu hankalinsu kwance da jin tamkar suma kadaine a cikin duniyar (Su bily duk an mutu ashe 😏🤔👹). A kankanin lokaci zancen ya cigaba da shiga lungu da sako. Da ga masu shiga farin ciki sai masu shiga rudani da tashin hankali dan abune da basuyi zato ba…

“Aiko lokaci yayi da zaki bijiro da zancen auren nan Waheeda”.

Malikat Ashwag ta fada cikin tashin hankali bayan gama sauraren Daneen Waheeda. Daneen Waheeda da gaba daya ita tasan kunar da zuciyarta ke mata ga rikicin Iftihal taja numfashi mai matukar zafi. “Hakane Ashwaq, amma kin san kafiyar Mammah, ga shi Ammarah sam nunawa ma take tafi son yarinyar nan sama da Iftihal din, taya kike ganin hakan zai yiwu cikin sauki?”

“Yuwuwarsa daya ce, mu nema su Sayeed Tasaddug-Husain da zancen shi da su Sayeed Hifzur-rahaman, da Sayeed Fayzul-haq tunda sune dai iyaye a gidan nan, duk da yake shugaba suma ai sama suke da shi, kuma dama a duk aure-auren nasa ai sune dai Mammah ke sakawa gaba ko da su Jasim”.

“Eh hakane, kema kin kawo shawara mai kyau.Yaushe kike gain zamu samesu?”.

“Ko zuwa anjima dan ba’a bori da sanyin jiki. Bara na kiga mu nema ganawar sirri da su, da ani ishan’i insha ALLAHU sai kawai mu zauna”…

Su Malikat Ashwaq sun gana dasu Sayeed Fayzul. haq, sun kuma tattauna sosai da sauraren abinda Daneen Waheeda tazo da shi, shi dai Sayeed Fayzul- haq ma baice komal ba. Garama Sayeed Hifzur- rahaman yace su basu lokaci zasuyi magana da Mammah a kuma jira Sayeed Tasaddug-Husain ya dawo daga Umrah gobe insha ALLAHU. Daga haka suka rabu.

A lokacin da suke tasu tattaunawar Iffah na can taima yan wan Malikat Bushirat rakkiya ga Shahan- shan da ya sakko hawa na biyu. Ya nuna farin cikin ganinsu shima, dan bai taba zama irin wanna dasu ba tunda yasan kansa, ballema yanzu da yake a shugaba. Suma duk wanda ka kalla zaka fahimci tsantsar farin ciki a tare da shi. Sun kuma ji dadin yanda ya dan sake dasu yay hira duk da maganar daya biyu ce dai. Sai dai abu mafi kayatar da su yanda ya girmamasu ya mutunta su. Sai kuma komi yake idonsa aka matarsa Iffah. Kusan zaman awa daya da rabi sannan sukai masa sallama…

Bikin sallah ya cigaba da gudana masu ziyara nata zuwa gaishe da Shahan-shan. Yayinda Malikat Bushirat ke a birkice, gaba daya Jasrah tama kasa gane kanta. Tayi kiranyen uwa har ta gaji amma taki zuwa. Sai taji komai ya karasa kwace mata. A kwana na uku da salla sai da doctor ya dubata. Jasrah dai tai

shiru da bakinta babu wanda ya sani gudun kananun maganganu. A washe garin cikar sallar kwana hudu Maganar komawa zaman kotu taje kunnen kowa, dan haka wasu suka kasance cikin zullumi da tsoron karfa garin tone-tone ga su Miran Jasim suma tasu allurar ta tone galma..

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button