Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 42

Sponsored links

Tun fara faruwar al’amuran nan yau ne zuciyarta ta ɗan fara mata wasi-wasi, a karan kanta sai take ji tana son sanin wanene ya shugabanci yarinyar domin halaka mata gudan jininta. Dan tabbas akwai ƙamashin gaskiyar lauje cikin naɗi. Ba komai ya sata farga ba a yau sai kallon zancen ido data ga yana gudana tsakanin Malikat Ashwaq da Ameera Haifah a ɗazun sanda aka wuce da Iffah. Sai kuma kallon da taga shi kansa Tajwar Eshaan ɗin ya musu su dukansu kasancewar suna tsaye duk a waje guda ne. Ita ta haifesa, duk da bata rayu da shi na tsawon lokaci a zaman kwana da yini ba, tasan halin ɗanta ciki da bai, ta masa sanin da ko da ido yay magana tana fahimtarsa. Lallai kallon yana da manufa, manufa irin wadda ya kamata ace ta sani. Manufa irin wadda ya kamata ace ta farka daga nannauyan barcin dake neman tasiri a idanunta. Ta jima tana zargin Malikat Ashwaq a duk abinda ke faruwa ga tilon ɗanta, sai dai a yau zuciyarta na gaya mata akwai wasu bayan itan, a wasun kuwa har Mamma (Malikat Haseenat) bata cire a ciki ba, dan akwanakin nan take-taken tsohuwar na rikita mata yardar data mata a baya. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, gaba ɗaya ji take komai ya cinkushe mata, dole ne ma tana buƙatar yin nazari mai faɗi, ya kamata kuma ta gana da shi…

 

★ Zaune yake harɗe a ɗaya daga cikin lafiyayyun kujerun falon. Tun dawowarsa da ga sallar la’asar ya yada zango anan. Laptop ce a coffee table ɗin gaban kujerar da yake yana sarrafata sannu a hankali. Sai mug na shayi dake ta faman tururi ƙamshinsa mai daɗi daya gauraya dana turarensa na tashi sannu a hankali. Sosai siririn farin gilashin idonsa ya sake masa ƙyau. A yanda gaba ɗaya ya tattara hankalinsa ga screen ɗin computer ɗin zai tabbatar maka abu mai matukar muhimmanci yake yi. Dan sai lokaci-lokaci ya kan ɗan ɗauka mug ɗin ya kai bakinsa ya maida ya ajiye duk hankalinsa na kan abinda yake yin. Sayeed Fayzul-haq dake shigowa ya sake maimaita sallamarsa cikin nutsuwarsa, a hankali ya motsa lips ɗinsa ya amsa batare da ya ɗago ba. Sayeed ya ɗan ranƙwafa yana kai gaisuwa duk da basu jima da rabuwa ba. Kansa kawai ya jinjina masa alamar amsawar kenan.

“ALLAH ya ƙara maka lafiya da nisan kwana. Malikat ke neman izinin ganinka idan bata shiga lokacin da bai dace da ita ba”.

Shiru ya ɗan tsaya daga sarrafa system ɗin, sai dai kuma bai dagoba har shurewar wasu sakanni da suka zama mintoci biyu. Maida yatsunsa yay kan keyboard ɗin kamar bazai ce komai ba sai kuma ya motsa lips ɗin kamar an masa dole ya furta, “Zata iya shigowa”.

“Malikat na godiya, ALLAH ya cigaba da kare mana kai adalin shugabanmu. ALLAH ya gafartama magabata”.

Duk da addu’ar ƙarshe ta masa daɗi a cikin rai bai motsa ba balle ya amsa. Har cikin ransa yana masifar jin maɗaukakin daɗi a duk lokacin da wani yay ma mahaifansa da suka kwanta dama addu’a..

★Kallo yake mata irin na kewa da lumsassun idanunsa. Sai dai a zahirinsa baka isa fahimtar hakan ba kai tsaye. A hankali ya ɗan kauda idanunsa da ke binta da kallo yana rissinar da kansa dai-dai tana zama. Itama fuskarta da murmushi take dubansa saɓanin shi da tashi babu walwalar sosai. Sai dai ya motsa lips ɗinsa a hankali ya furta, “Barka da yamma Ammie.”

Murmushi ta sake saki da ke sake fidda ƙyawun da ALLAH ya mata. “Ina fatan kana lafiya Niger?”.

Maimakon amsa gajeren murmushin da ita kawai keda lasisin ganinsa ya ɗan saki yana kauda kansa, sai kuma ya sake maidowa yana mai zuba mata idanunsan nan masu kaifi. Dan ita kanta data haifesa a duk sanda ya tsareta da su tana jin tasirinsu sosai tattare da ita. Nata ta janye cike da ƙasaita ta furta, “Ya jikin Ibnati?”.

Kamar bazaice komai ba sai kuma a fisge ya amsata. “Alhamdullah”.

“Thanks God. ALLAH ya ƙara lafiya”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button