Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 49

Sponsored links

Bayan wasu ƴan mintuna Malikat Bushirat taci serious tana maida dukkan hankalinta kansa. Murya cike da kulawa ta ce, “Baka da lafiya ne?”. Kai ya juya mata alamar a’a. Sai kuma ya motsa lips ɗinsa kaɗan ya furta “Ina missing ɗinki ne my first luv”. Ji tai wani daɗi na ratsata, kanta na sake kumbura da alfaharin kasancewarta mahaifiya ga wannan ƙasaitaccen bajimin ƙyaƙyƙyawan sarkin. Ta sake shafa fuskarsa da kulawa matuƙa. “ALLAH yay maka albarka, ya cigaba da kulamin da kai da baka kariya”.

“Amin”.

Ya furta a saman lips, Jasrah kam a zahiri tana murmushi. Idanunsa ya maida kan Jasrah, fuskarsa babu alamar wasa ya furta “Mi kikeyi anan da safen nan kika bar mijinki?”.

Murmushi ta masa ganin a serious yay maganar babu wasa a ciki. Tana ɗan wasa da yatsunta dan bazata iya kallonsa ba tai maganar dake bakinta duk da a shekaru itace sama da shi, sai dai ALLAH ya kwace girman ya bashi matsayinsa na namiji kuma sarkinta, a hankali ta ce, “Maganace mai muhimmanci ta kawoni”. Ta ƙare maganar tana ɗan ɗagowa ta dubi Malikat Bushirat. Shima kallonsa ya maida ga Ammien tasa. Malikat Bushirat ta sauke sassanyar ajiyar zuciya tana ɗan shafa kansa, “Magana ce muhimmiya Jasrah tazo da ita a kanka Saiful-malik”.

 

 

Kaifafan idanunsa ya ɗan tsura ma Jasrahn ganin yaƙi yarda ta kallesa ya janye su ya sake maidawa ga Ammien sa. “Wani abu ya faru ne?”.

 

Kai Malikat Bushirat ta girgiza masa, “Komai bai faruba, na baya ne dai da suka faru musamman akan abinda yarinyar nan ta aikata. Ba kowa ne zai fahimci irin abin da naji ba a lokacin da na fahimci zan iya rasa tilon ɗan dana mallaka a duniya. Amma sai na danne zuciyata wajen maida hankali na maka addu’ar samun lafiya fiye da ɗaukar mataki. Bani da jayayya akan hukuncinka, sai dai ƴar uwata tazo da shawarar dana gamsu da ita nima”.

Kansa dake a kafaɗarta ya ɗago a hankali jin yanda take maganar a serious, sai dai baice komai ba. Itama batare data kallesa ba ta cigaba da faɗin, “A nawa ra’ayin ka rabu da yarinyar nan, sai dai bazan tirsasaka kan hakan ba zan jira har lokacin da za’a yanke mata hukunci bisa abinda ta aikata. Amma kamar yanda Jasrah ta faɗa ya kamata ka ƙara aure. Ina son ka samu farin ciki kaima kamar kowane namiji mai irin shekarunka.

 

Ina son naga zuri’arka Eshaan. Na kuma shirya fito-na-fito da duk mai son daƙile waɗan nan zaren farin cikin namu ta hanyar kashe yaran da basu ji ba basu gani ba dan kawai kasancewarsu matanka. Nima a wannan karon na shirya, na shirya tarar kowa Eshaan…”

 

Kuka mai tsuma zuciya ya sarƙe ta. Har cikin ransa yake jin kukan nata, sai dai babu alamar zaice wani abu. Jasrah da itama ke hawayen ta miƙe a hankali zuwa gabansa, zama tai ta kamo hanunsa cikin nata cike da kulawa ta kira sunansa. Ɗagowa yay a hankali ya zuba mata idanunsa da baka isa gane yanayin da yake ciki ba koda a cikinsu. Hawayen da ke cigaba da zubo mata ta share tana ɗan kauda idanunta zuwa ƙasa, dan kaifin nasa sun mata yawa. “Kayi haƙuri ka fahimcemu Abni, muna tsananin jin zafin abubuwan da ke faruwa da gaba ɗaya sun ta’allaka da kai ne matsayinka na shugaba sama da kowa na ƙasar nan. Lokaci yayi da zamu tashi yin fito na fito da kowa a wannan gaɓar. Ba zai yiwu mu cigaba da zuba ido ba kuma. Kafin yau mun tattara hope ɗin mu gaba ɗaya kan yarinyar nan, amma daga ƙarshe itama tai shirin halaka ka ma. Shiyyasa nai tunanin ya kamata a nema maka wata matar dan nasan kai dai baka da wannan lokacin, mu kuma Insha ALLAHU zamuyi duk shirin da ya dace don ganin mun kamo bakin zaren. Fatanmu mu dai kawai amincewar ka, dan wannan al’amarin baya buƙatar cigaba da zuba idanu kuma”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button