Hausa Novels and Stories

Nihad Chapter 11

Sponsored links

 

Juyawa Nihad tayi daga karshe ta koma cikin gidan don ko kallon inda take Khalil bai yi ba, to wai wa ya dau jakarta? lkci daya jikinta yayi sanyi hankalinta ya tashi fiye da da, haka nan ta shiga gida jiki ba kwari ta koma dakinta ta shirya, Hijab har kasa ta saka ko powder bata shafa a fuskar ba, ta fito ta tafi bangaren Mumy, xaunawa tayi saman kujera ta gaisheta sannan tace “Mumy xan tafi makaranta ina da lectures karfe takwas” Mumy ta kalli agogo ganin bakwai da rabi tace “Kinyi breakfast ne?” Tace “Xan yi idan na sauka” Mumy tace “To ko ke fa da kika sa Hijab yau, kinga yanda yayi maki kyau, amma kullum in ta maki magana daya a kan shegun mayafan nan da kike sawa ba kya ji” Nihad ta ɗan kirkiri murmushi ta mike tace “Sae na dawo” Mumy tace “Toh Allah ya tsare, kiyi addu’a kafin ki fita” Nihad ta amsa da “Toh” sannan ta fita. Gaba daya Nihad neman appetite dinta tayi ta rasa, daga karshe nan ta bar abincin tayi ma Umma dake parlor sallama ta fita gidan, mai gadi kadai ta samu xaune bakin gate, ta nufesa tana tsaye dab da shi tace “Aminu don Allah baka ga min jaka a bakin gate ba? Kamar a nan na yar jiya da daddare, ko da safe nan don Allah baka gani ba??” Yace “Subhanallahi jaka Hajiya? ae ko wllh tllh ban gani ba, kema kin san da na gani ae xan adana maki” Nihad ta rasa abun cewa tayi shiru, iphone dinta fa na jakar yanxu ta ina xata fara? Wani xufa ta ji na keto mata, can ta dake tace “Ina driver din?” Aminu yace “Ya tafi yayi wanka” Tace “Sae kaje kace masa ya fito ya kai ni makaranta ni dai”

 

Aminu ya mike da sauri yace “Toh Hajiya” daga nan ya nufi chalet din. Bayan Aminu ya shiga har dakin da khalil ke ciki ya sanar masa abinda Nihad tace, khalil dake zaune gefen gado yana combing kansa yace “Ta saba xuwa makaranta karfe bakwai da rabi dama?” Aminu yace “Atoh dae, nima ban ta6a ganin ta fita da safe xuwa makaranta ba wai kuma ran asabar, amma kai dai kawai ka fito kaje ka kai ta kar ta kara maka wani fitsarar” Khalil ya kallesa bai dae ce komai ba yana ci gaba da combing din kansa, Aminu ya bi dakin da kallo yace “Wai!!! amma kana kokarin gyara dakin nan, dubi fa dakin kamar a can daya bangaren, ba dauda ba wari ba tarkace, wannan ai idan na kwanta a nan sai in makara al-qur’an….” Khalil ya mike yace “Mu je…” Aminu ya kasa kunne yace “Ba waya bace ke wannan rurin?” Khalil yace “Mu dai je” Aminu ya mike ya fita dakin, Khalil ya bi sa da kallo kafin ya dage duvet din da ya lullube jakar Nihad da shi a saman gado sannan ya bude jakar ya ciro wayarta dake ta vibrate alamar kira, Husnah ya kara gani for the fourth time a jikin screen din wayar, tun daxu take kira, nannade wayar yayi da duvet don baxae iya silencing dinsa ba sbda security dake jiki, ya dau makullin mota ya fita daga dakin ya kulle sannan ya fita compound. Yanda xaka san abun duniya ya taran ma Nihad xama tayi a kan bench da mai gadi da Khalil ke xama, ita dai tana da yakinin dole Khalil xai hango jakar a bayan flowers kuma ai a bude ma ta bar karfen wajen, wai to don bashi da kunya sai kawai ya kama ya dau mata jaka, yaushe ta sake masa har xai kai hannunsa kan jakarta, wato yanxu jira yake sai ta tambayesa kenan? Cabdi…

 

tana hangosu tayi maza ta mike ta sha kunu, Khalil dai ko kallon direction dinta bai yi ba ya tafi gun motar ya bude ya shiga, bayan yayi warming mai gadi ya bude masa gate, Sai da ya fita compound sannan Nihad ta fita ita ma tana tafiya a hankali ta bude back seat ta shiga ta xauna, Aminu ya dinga daga mata hannu alamar a dawo lafiya, ko kallonsa bata yi ba, Khalil ya ja motar suka bar layin, tunani take to yanxu dai tambayarsa jakarta xata yi? Cab gaskiya baxata yi hakan ba, m ta saci kallonsa ta madubi suka yi ido hudu, da sauri ta dauke kanta ta wani daure fuska ta zuge zip din wani jakar da ta dauko ta fiddo chewing gum ta bude ta jefa baki, shi dai driving kawai yake, sai da suka kusa makarantar tayi gyaran murya tace “Malam ka bude min Ac xafi ya dameni….” A takaice yace “Ke kika san meye shi” Tayi masa wani kallo tace “kace me??” Bai tanka ta ba, ta masa wani shegen harara ta ja tsaki kasa kasa ta ci gaba da taunar chewing gum dinta, suna isa makarantar dai dai department din nasu yayi parking, tana ta sauraron ta ji ko xai yi maganar jakar amma shiru, gabansa kawai yake kallo, ganin bata sauka ba, kuma kamar bata da niyyar saukan yace “Ko yau ma xa a bar maki makullin ne?” Ta galla masa wani harara tace “Ai ba ni na kawo motar ba balle ka bar min makullin” tana gama fadin haka ta bude motar ta sauka ta ki kulle door din tayi tafiyarta, ya bi ta da wani kallo, sai kuma ya sauka ya kulle sannan ya hau motar ya tafi…. Husnah na ganin Nihad tace “Shine nake ta kiranki kike danna min busy Nihad?” Nihad ta sauke ajiyar xuciya amma ta ki bata amsa, ta nemi seat ta xauna, wato dai a takaice drivern nan ne ya dau jakar tunda gashi har Husnah ta kira ana ta danna mata busy, lallai mutumin nan raini me karfi ya shiga tsakaninsu, bayan dauke mata jaka sbda guts har bude jakar ma yayi kenan, muryar Husnah ya dawo da ita daga tunanin da take, tace “Ina magana kin min shiru, dama ba komai bane ce maki xanyi ki taho da jakar da kika je birthday jiya da shi, don akwai abubuwana a ciki” Nihad ta kalleta tace “Abubuwanki kamar me?” Husnah tace “Kwalban Codeine dina da Naff na ciki, sai prophylactics, ni ina jin kamar ma har da lingerie dina a jakar, don na duba ban gani ba….” Nihad ta zaro manyan idonta tace “Duk a cikin ina???” Husnah tace “Jakarki mana, kinsan yana da girma” Nihad bata san sanda ta mike ta dafe kirjinta ba tace “Na shiga uku….” Da mamaki Husnah tace “Kin shiga uku kuma? Me ya faru?” Nihad tayi narai narai da tace “Wayyo Allah na, Me yasa xa ki min haka ki ajiye abubuwan nan a cikin jakata Husnah? Me yasa xa ki min haka? Gashi yanxu jakar ta fadi a bakin gate ban san wanda ya dauke min ba” Husnah ta gwalo ido tace “Kaiii, garin yaya kika yarda jaka a bakin gate Nihad?” Nihad da abun duniya ya isheta ta koma ta xauna ta cije yatsa tace “Na shiga uku” Husnah ta sauke ajiyar xuciya tace “Toh kinsan wa ya dau jakar ne?” Ta kalli Husnah tace “Wallahi wannan driver din nake zargi don shi kadai ya gan ni sanda na dawo da asuba don a bayan flowers dake kofar gida na fara buya as a result of people coming out from the mosque after subhi prayer” Husnah ta rike ha6a tace “Ji tsiya, Driver kuma?” Nihad ta kasa cewa komai tayi tagumi, Husnah tace “Tabb shine kika yi shiru, to me kike jira da har yanxu baki tambayesa ba?” Nihad tace “Toh me xan ce masa? Bayan ban ga sanda ya dauka ba, Har wayata fa na cikin jakar, idan ba sata yake son yi ba ai xai ba Aminu ya ajiye min” Husnah tace “Ehh lallai wannan mutumin ya rika, shi ke ta ja min busy kenan? Wato dai har ya bude jakar” Nihad ta xaro ido tace “Na shiga uku, gashi kin xuba abubuwa kika ce cikin jakar” Husnah ta mata wani kallo tace “Ke dalla to meye, koma me ya gani cikin jakar ba shi ya ga duhu ba, kuma ma bansan uban me kike jira da har yanxu baki tambayesa jakarki ba, ko tsoronsa kika fara ji? ai ba ma tambayarsa xa ki yi ba wai ko ya ga jaka ko bai gani ba, kawai ce masa xa ki yi ya baki jakar ki da ya dauka kar kiyi masa rashin mutunci, kuma kada ya sake ta6a maki kayanki ko da kuwa a titi kika yar don baki aikesa ba”

 

Nihad dai ta rasa abun cewa tunani iri iri ke yawo a ranta, Husnah ta kyabe baki tace “Ni dai ki adana min prophylactics din nan foreign ne ba na kasar nan bane kuma tsada ke garesu, Codeine din kuma shi ma nasan ba kya sha, kar ki je ki xubar ki adana mana gaskiya” Tashi Nihad tayi ta bar mata wajen ta koma seat din baya abun duniya ya isheta, yanxu mutumin nan duk ya ga abinda Husnah ta saka mata a jaka? To amma ya ma yi mugun rainata gaskiya, waye shi da har xai bincika mata jakarta?? A daddafe Nihad ta yi lectures daya tace xata tafi gida, Husnah tace “Ke don Allah ki saki ranki, ko Abba ne ya ga jakar nan ya dauka ya bincika ai sai haka, me xai dameki akan wani shegen driver dinku ya bude jakar ki? Ae rashin mutunci mafi muni xaki masa idan kin koma gida anjima, ni abinda ya fi damu na ma wayarki ne wllh, don matsiyacin sai ya iya dauka yace xai je ya siyar bai san wayar nan sai ta siye duk yan kauyensu ba, yanxu kawai ki xo mu je police station, cikin lokaci kalilan xa ayi tracking” Nihad ta zaro ido tace “In tona ma kaina asiri kenan, kin zata na gaya ma kowa cewar na yarda jaka da waya a ciki? To har Nihal bata sani ba” Husnah tace “In kince ayi cikin sirri babu tonon asiri ai sai ayi hakan, duk fa mutanena ne, amma wllh so nake a walakanta sa idan aka ga wayar a wajensa, a nakada masa shegen duka” Nihad tace “Husnah bari in je gida ko xan ji saukin abinda ke damuna, i can’t endure anymore” Husnah ta ta6e baki tace “Wllh kina da sa ma kai damuwa, duk ki bada space din da lamarin driver xai dinga damunki haka, to wai shi wannan driver din daga ina ya xo yake abu isa isa da gadara haka?” Mikewa Nihad tayi tace “Duk yanda ake ciki xan kiraki da wayar Nihal ai tana da number ki” Daga haka ta fice daga hall din, tun da ta fara school din bata ta6a trekking da kafafuwanta har bakin titi ba sai yau, haka nan ta tsayar da adaidaita shi ma xata iya kirga iya sau nawa ta hau sa a rayuwarta, suna isa gida ta sauka ta bude jakarta ta basa kudi sannan ta shiga gidan, Aminu ne kawai bakin gate, ta ɗan bi compound din da kallo sai kuma tayi kasa da murya tace “Aminu baka tambayar min driver din can ko ya ga jakata ba kuma?” Aminu yace “Anya, don ina da yakini da ya gani xai nuna min, ai shi mutum ne me gaskiya da amana” Ta wani galla masa harara tace “Dallah Malam rufe min baki, duka duka kwananku nawa tare xaka san yana da gaskiya da amana, ashe kai dolo ne ma ban sani ba? To bari ka ji wayata ce ta kusan miliyan daya da rabi a jakar nan” Driver ya gwalo ido yace “Subhanallahi, subhanallahi….”

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button