Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 66

Sponsored links

Komai ya tsaya cak a ɓangaren su Kaka a kwanakin nan da suka gabata dangane da neman inda su Babiy suke. Barrister ya sake bin duk hanyar da yake da yaƙinin samu koda na ƙarfin iko ne amma sai ya risketa a toshe. Zuwa yanzu kam su duka ukun sun fahimci komai shiri ne bisa la’akari da labarin da suka bama juna na gargaɗin da akai musu. Sai dai abu mafi ɗaure kai da ban mamaki, wanene mai shirin? A wane dalili yay shirin kuma? Miyasa zaiyi shirin akansu Babiy ɗin?.

 

 

Waɗan nan tambayoyi sune suka zama abun tattaunawa tsakanin Kaka da Barrister dama Abu Zainab daya saudaukar da dukkan lokacinsa domin ganin komai ya daidaita. Bisa shawarar Barrister Kaka yay shirin komawa Jimna, dan a cewarsa suna buƙatar bada ƙafa kodan harar rayukansu da aka farayi suma. Saboda a kwanaki biyun da suka gabata da ƙyar Barrister yasha a hanun wasu tankunan mai da suka sakashi tsakkiya bisa titi lokacin da yake tashi aiki. Haka yaron Abu Zainab a jiya anyi wuff da shi daga hanyarsu ta zuwa makaranta a cikin ƴan uwansa. Ba kuma a sakesa ba sai a daren jiya bayan sallar isha’i lokacin kowa ya gama jigata da nema da hasashen inda ya shiga. Rubutacciyar wasiƙar da aka haɗosa da shi yayin maidosa ya basu tabbacin daga inda tsiyar take.

Kaka ya kammala kulle ko’ina na gidan sannan yay sammala da su Abu Zainab tare da godiya ya ɗauki hanyar inda zai samu motar ƙauyen Jumna. Harya sauka a mototaxi aka dakatar da shi, da mamaki yake duban mai mototaxi ɗin dake miƙa masa ƙaramar jakkar hannunsa. “Baba kayi mantuwa, ALLAH yasa na farga da wuri”.

Kafin Kaka ya samu damar cewa wani abu saurayin ya ajiye jakkar gabansa ya koma cikin mototaxi ɗin da baiko waiwayo ya dubi Kaka dake yunƙurin dakatar da shi ba.

“Kar kai jayayya tsoho, ka ɗauka dan naka ne”.

Aka faɗa ta bayansa dai-dai yana kaiwa duƙe zai ajiye jakar. Ɗagowa kaka yayi, sai dai bayan mutumin kawai ya gani sai ƙurar motarsa. Ran Kaka ya sosu, har fuskarsa ta nuna haka. Alamar ƙosawa da wasan kwaikwayon waɗan nan mutane ya fara tunzura kawaicinsa da son bin doka a yanda tazo. Amma ya fuskanci burinsu kawai su kaisa maƙurar da sai ya gwada ƙwanjinsa akansu. Yay ƙwafa tare da ɗaukar jakar…….

Wani matashin saurayi siriri dake zaune cikin taxi nesa kaɗan da Kaka ya faɗa yana ɗan kai hannu a kunensa ya dafe bluetooth ɗin dake manne a ciki.

 

“Tabbas akwai alamar ɓacin rai tattare da shi a yau, dan fuskarsa harta kasa ɓoyewa”.

 

Saurayin ya sake faɗa da alamar amsawa wanda ya kira da Boss ɗin a farko idonsa ƙyam akan Kaka da har yanzu ke tsaye jikin wata mota. Kai ya gyaɗa alamar an sake masa magana daga wayar, sai kuma ya gyara baƙar facing cap ɗin kansa da faɗin, “Eh da alama bai samu motar garin nasu bane. Amma gani ina tunkararsa, komi kenan zan cigaba da riƙe wayar dan kaji komai”.

Kaka na shirin ɗaukar jakar da mai mototaxi ya barsa da ita zai bar wajen saurayin ya katsesa ta hanyar masa sallama. A ɗan daƙile ya amsa dan ransa babu daɗi har yanzun. A yanda ya kafe saurayin da idanunsa masu kaifi duk sai yaji ya tsargu. Ya haɗiye yawu da ƙyar cikin ɗan harɗewar harshe yace, “Baba tafiya ne?”.

Kaka dake nazartarsa ya ƙyabe baki cikin masa kallon sama da ƙasa yace, “Kaima nasun ne?”.

Sai da gaban saurayin ya faɗi, amma yay jarumtar ƙwaɓe fuska da faɗin, “Nasuwa kuma Baba? Ni fa mai taxi ne, na hangokane kawai na iso”.

Kaka ya cigaba da masa kallon nazari, sai kuma ya furzar da isaka da kauda kansa yana kallon mutanen daketa faman kai kawo a titin cikin son watsar da lamarin saurayin…

“Bar wajen kamar kayi fushi”.

Aka faɗa daga cikin bluetooth ɗin dake manne a kunensa…..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button