Hausa Novels and Stories

Idon Naira 36

Sponsored links

Da mamaki haj maryamah takalli umman sbd sanin asibitin ta kudine sosai Dan basuda ko irin dogayen dakunan ward haka

Duka dakunansu daddaya ne Amenity rooms dai Kai tsaye.

Atoh, ai danki ne ya kawota

Allah ne kawai yasan uban kudin daya kashe daga haihuwarta zuwa yanzu,

Ko kudin haihuwar ba qananu bane gana jinyar ‘yar Kuma acan wani dakin daban..,ai wlh maryamah kinyi sake sosai,.

Ace ‘danki da Kika Haifa Yana hada kainarki data wata

Duk laifinki ne Dan kece Kika barwa zainab ‘dan gashinan yanzu bake kadaiba munata fama dashi

Ga shegiyar kafiyar tsiya agunsa

Shi ala dole yasan Allah baya qarya baya magana biyu.

Numfashi haj maryamah ta sauke tana kasa cewa komai sbd tarasa abin fada.

Dakin da zainab din take suka nufa tunda umma tasan dakin dasukazo tareda aqeel kafin wucewar tasa.

Koda sukaje tana kwance idanuwanta a rufe tana tunanin mijinta da ‘yarta datazo ta zauna tsakiyar ranta,

Sam Bata qarar da hakan da yake zaunuwa Aran mahaifiyarsa ba sai yanzu data sake qararwa duk da har lokacin kaunar aqeel mai girma tana cikeda ran nata sai takejinsu su biyun sun cike mata zuciya tako Ina.

A tsawon shekarun datayi tana wankin wasu daga cikin kayan haj maryamah da gyaran dakinta tareda wankin toilet dinsa to tariga ta haddace qamshinta ras acikin hancinta Dan haka suna shogowa dakin tun kafin ta bude ido hancinta ya tabbatar mata da ‘yar uwartace ta shigo

Ahankali ta bude idanuwanta dasukai jajir a kumbure ta kallesu tareda sauke Kai tana sake gaida umma kafin ta gaida haj maryamah din.

Dukkaninsu kusan atare suka amsa gaisuwar sai haj maryamah data gyara tsayuwarta tana kallonta tayi mata gaisuwar rasuwar Mijinta kafin daga baya ta tambaya baby.

Amsawa zainab tayi tareda cewa ta gode Allah yabada ladan gaisuwar malam din.

Shiru sukai dukkaninsu saidai umma ce tafara maganar zainab din idan ansallameta taje gidanta tafara tattara kayanta tasan yanda zatayi dasu tukuna saita wuce can gidan haj maryamah din.

Gyada kai tayi kawai batareda ta iya bude Baki tai maganaba Dan batajin zata iya.

Basu wani jimaba suka tafi bayan haj maryamah din ta Ciro 10k daga handbag dinta ta ajiye mata a gefe

na dubiyane ko sadaka ne tabata oho.

Bayan tafiyarsu tashi tayi ta nufi toilet din dakin tasake Dan kamo ruwa ta fito Takoma ta zauna tana zubawa 10k din da itace alkhairin farko dazatace Yar uwarta tayi mata na kudi dai.

Da daddare Saida aka Kuma zuwa aka matsa nononta still har lokacin ba komai dayake Acikin siyayyar da aka rubutawa Aqeel ya siyo harda Madara Kuma kaman yasani ya siyo musu da yawa.

Washe gari da yamma tayi tunanin Kiran aqeel din sbd tasan Kila ya Isa a time din,

Tunaninta tsayawa yayi data tuno da batada waya yanzu tun rasuwar malam ta rasa wayar da rikicinta dasu umma.

Wani nannauyan numfashi ta sauke sbd shima Aqeel ya manta da batada wayar saiya nemeta yajita babu.

Sanyi jikinta Yakuma Yi sai kawai ta cire ran jinsa sai Randa Allah yabada iko.

Cikin kwanaki hudu ita kam ta warke sumul batada ciwo ko damuwar komai a jikinta Dan haka hankalinta gabaki daya nakan ‘yarta MARYAMAH da itama tana Dan samun kuzari da kulawa sosai Dan kuwa Aqeel babu abinda bai tanadarba ya biya kafin ya wuce din.

Baa kawo mata abinci daga gida Dan haka itace take siyan abincinta taci anan duk da nata jegon dakuma damuwar rashin miji duk yasa cikinta a bushe yake batason cin abincin,

Wanda ma take nace tana siya tanaci sbd tanason tasamu Nononta ya taru MARYAMAH tasamu nono.

Wasu daga cikin maqotanta sunzo har asibitin sun dubata da yarta duk da baa bada babyn

Kuma dazasuzo kusan duka sun kawo mata abici wasu kudi harda kunun haihuwa mai kyau suka kawo mata Tasha kuma taji dadinsa sbd ya taimaka mata gurin samun nonon Dan ajiyewa tai tana shansa kwana biyu kafin yaqare dayake dakin akwai fridge harma da heater ta ruwan zafi.

Samun ruwan Nononta yasa babynta tafara samun kuzari da lafiya sosai Dan haka takesan nono sosai gashi Daman ba laifi babyn tanada Dan girma kadan ba irin sosai takeda rashin girman Nan ba ko kadan.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button