Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 22

Sponsored links

A tare aka amsa da amin har lokacin kawunansu dai a ƙasa. Ƙoƙarin hana idanunsa da ke fusga gareta yay. Sayeed Hanifud-Din ya cigaba da faɗin, Muna buƙatar sake ji da ga bakin masu ƙara. Muna fatan abinda ke a zukatansu ne zai fita a harsunansu, kuskuren hakan na nufin ɗaukar mataki takowace fuska da shari’a a ta koyar damu”.

Kawuna suka shiga gyaɗawa da ambaton (Insha ALLAHU) alamar tabbatar da abinda ya bukata ne zai tabbatan. Miran Arshaan ya sake rissinar da kansa da gyara zama na tsantsar nutsuwa da duba ladabi. “Ni sunana Miran Arshaan ibn Abdul-majeed Aliy. Zan kasance mai wakiltar ahalina dangane da guba da Zawjata-almilk ta zuba ga ɗanmu a yunƙurinta na kasheshi ranar 21/2/2022. Muna roƙon adalin shugabanmu mai albarka daya yanke mata hukunci dai-dai da laifinta dan ya zama izina ga ƴan baya. Ngd.”

Babu wanda ya motsa a falon, tsahon mintuna biyu Shahan-shan ya nisa yana mai ɗauke dubansa ga Miran Arshaan ya maida ga sauran ahalinsa. A karon farko ya motsa lips ɗinsa a hankali, “Ko masu ƙara nada sauran wani ƙarin bayanin bayan wannan?”.

Kawunansu suka shiga girgiza wa alamar a’a. Komai baice ba ya ɗauke kansa ya maida ga Iffah da tun da aka shigo da su a falon bata ɗago ta kalla kowa ba. “Ko wadda ake tuhuma tana da ja akan abinda ake tuhumarta da shi? Ko abin cewa?”……..

Iffah da ke ƙoƙarin danne kukanta ta girgiza kanta alamar a’a. Idanunsa dake mata kallon ƙasa-ƙasa ya ɗauke ya maida ga Sayeed Hanifud-Din dake riƙe da takardar tuhume-tuhumen da akema Iffah. Miƙewa Sayeed.. yayi yana mai risinawar girmamawa ga Shahan-shan. Kafin ya sake gyara tsaiwarsa ya maida kan Iffah. “Ranki ya daɗe wannan kotu mai adalci na son ji daga bakinki dangane da waɗan nan laifuka da ake zargin kin aikata su. Shin kin aikata da gaske? Ko kuwa dai abin ba haka bane……”

 

“Ba haka bane? Kenan ma ƙazafi mukai mata bayan da bakinta ta furt…..” Jasrah ce mai maganar rai ɓace. Sai dai muƙut ta haɗiye batare da ta ƙarasa faɗar ba sakamakon kallon da Tajwar Eshaan yay mata, dan a yanzu sarkinta ne shi ba ɗan yayarta ba. Idanun nasa ya juya kan Sayeed.. alamar ya cigaba. Sayeed ya sake rissinar da kansa da ɗan rankwafawa sannan ya sake maida hankalinsa ga Iffah.

Tayi matuƙar jarumta da ƙoƙarin danne hawayen domin hanasu cigaba da zuba. Sai dai tanajin raɗaɗinsu a ƙarƙashin zuciyarta, har hucinsu na rige-rigen fita da numfashinta. Ta sani basai Jasrah tace komai ba, su dukansu zafinta sukeji, dan dukansu taga hakan a fuskokinsu, Daneen Ammarah ce mai ɗan sassauci, bakuma tada abinda za tace a kanta itakam…..

“Kotu na sauraren Zawjata-almilk”.

Sayeed Hanifud-Din ya faɗa a girmame duk da kuwa ya haifeta. Murmushin da ya bama kowa mamaki Iffah ta saki, tare da ɗago fuskarta a karo na farko yanda zata iya duban kowa. Sai dai bata aminta ta haɗa idonta da kowan ba. Tsaiwarta ta gyara idonta na kallon sashen su Miran Jasim ƙasa-ƙasa, murmushi ta sake saki a karo na biyu dan ganin yanda duk suka shiga yanayin firgici sai mazurai suke, duk da suna ƙoƙarin dannewa kuma. (Ku kwantar da hankalinku ai ba’a zo wajen ba) ta faɗa a zuciyarta tana ɗauke kanta. A zahiri kam natsuwarta ta sake tabbatarwa tana fuskantar kotu da ƙyau. “Ni Fareedah bint Zayyan zan fara da bada haƙuri kafin cewar da kowa ke buƙata da ga baki na. Nasan ko ba’a kawoni nan an gurfanar ba na can-can-ci acema bana numfashi a dalilin taɓa rayuwar mutum mai girman iko kamar Shahan-shan. Basai na wahal da Shari’a ba tabbas nice da kaina na bashi madarar da ya sha mai ɗauke da dafin macizai….”

Babu wanda bai zaro idanu ba a mutanen falon dan mamakin ƙarfin halinta. Shiko uban gayyar da furucin nata yazo masa a bazata kafeta kawai yay da idanu zuciyarsa na matuƙar mamakin ƙarfin halin takife ɗin yarinyar…

 

 

Cikin ɗan taɓe baki Iffah ta ɗage kafaɗu tamkar bataga yanayin da duk suka shigaba ta cigaba da faɗin. “Sai dai ba bashi madarar bace ya kamata ya zama abin mamaki ga wannan kotu mai adalci, sannan kuma ba itace ya dace ta zama abin tuhuma ba ko burin ganin an hukunta nin da kowa ke faman haƙilo da kai kawo sai kace kunajin tsoron numfashina barazanace gareku. Ni inda nice ku, tushen samuwar madarar zan maida hankali sani. Amma duk da haka ina so mai girma Shugabana da ku ahalinsa ku duƙufa wajen bincikowa, ba kuma dan inajin tsoro ko shakkar hukuncin da za’a min bane. Ba kuma dan zan kasa kama sunan wani bane wajen bayyana yanda akai madarar tazo hannuna ba. Ku da kanku nake son ku gano kafin ku sami dukkan amsoshin da kuke buƙata daga gareni dan ko numfashina zai tsaya sai na fesar da su ne tun daga tushe, ku kanku masu kisan Zawjata-almilk na baya sai ku shirya ranar tonon silili na tunkaro ku in har numfashina na harbawa daga gangar jikinna. Da ga ƙarshe ina roƙon wannan kotu mai adalci data sallami amintaccen hadimin shugabana tare da masu dafa masa abinci dan basu da laifin komai, su kuma masu ganin sun binne Iffah ne su shirya akwai sauran wasan dan ko filin ba’a share ba. Dan sai sun biya fansar jinin ƴan uwana uku da na iyayena koda zasu sami nasarar shafe nawa babin a doron wannan ƙasar”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button