Hausa Novels and Stories

Rabi Danja

Sponsored links

Kaiiiiiii Malam Ubanka”, ta faɗa tare da rugawa a guje har zanin dake jikinta yana niyyar kwancewa, shima wannan mutum bai ƙasa a gwiwa ba ya rufa mata baya suka bawa hammata iska, gudu take sosai dan ganin ta ƙarasa mafakarta, shima gudu yake domin ganin ya kamota ya hukunta ta, abinda zai baku mamaki babba ne shi sosai dan sosai zaiyi jika da wannan ƴar ƙaramar Yarinya, sai hanya ake basu dan kaucewa bangaza daga gare su dan kowa yasan halin wannan Yarinya wajen tsokana da neman tashin hankali ga al’ummar gari, sai dai kowa yasha mamakin ganin magidancin da suka kaso tsere da wanga Ƴar jaririyar Yarinya.

Cikin ikon Allah ta iso wani madaidaicin gida ta afka, shima wannan mutum bai ƙasa a gwiwa ba ya rufa mata baya har ciki,.

“Ni Saratu ina wannan Yarinyar ta shiga tin sha ɗaya na safe har yanzu shuru, kuma na aika ko ina bata nan, ni dai Allah yasa tana cikin ƙoshin lafiya ya kare mana ita a duk inda take”, cewar wata matashiyar mata da baza ta wuce shekara Arba’in ba, tana zaune tana shirya Carbi, ga sunan a gaban ta da yawa da alama sana’arta ce, wani matashin mutum ne ya fito daga bayan gida da alama ruwa ya kama, ya kurkure bakinsa ya zubar ya aje butar yana gyaran murya, “ai Innar Rabi kema dai kinfi kowa sanin tana lafiya, tinda batin yanzu ba hakan take faruwa idan ta fice sai sanda hali yayi zaki ganta Allah dai ya shir……”, bai ƙarasa faɗa ba yaji anyi tafiyar yaji da shi har wularsa na faɗuwa a ƙasa, Innar Rabi kuwa da take shirin Carbi gaba ɗaya ya kelaye a ƙasan siminti ya watse, ɗaki ta shige ta banko ƙofa, basu gama tsaida hankalinsu ba suka ga ƙaton magidanci a tsakiyar tsakar gidan su yana huci da numfarfashi, Baban Rabi da ya ɗakko hularsa a ƙasa yana kallon ikon Allah da rana tsaka, “lafiya Malam me haka ka shigo gidan mutane da girmanka da komai”, cewar Baban Rabi

“Wallahi bamai hana ni cin uwar wannan Yarinyar, harni zata kira ta zaga wai Ubana, yana ƙasa ƙasa ta rufe masa ido, to wallahi ku fito da ita na dake ta dan kutumar ubanta”, cewar wannan mutum.

Cikin mamaki Baban Rabi yake kallon wannan mutum, dan shi mamakin abin yake na wannan mutum, “Amma malam bakada hankali, ka keto hanya da girmanka da komai ka biyo ƴar tatsitsiyar Yarinya ka kuma keta shari’a ka shigo har gidan mutane kace kuma mu fito maka da Ƴa ka daka, harda zaginta, to ka fice min da gani kona tara maka mutane wallahi”.

“A’a Baban Rabi kayi haƙuri kayi masa uzuri na tabbata bashida lafiya, dan da lafiyayye ne bazai shigo mana gida kuma yace mu kawo masa ƴar mu ya daka ba gashi geme-geme da shi”, cewar Innar Rabi da lamarin mutumin yasa take tunanin ya kwance.

Wannan mutum jin za’a tara masa mutane yasa ya ce “Wallahi ku rubuta ku ajiye duk inda naga Yarinyar nan saina mata mugun dukan da saita dena ganewa”, yana faɗa ya ja tsummar babbar rigarsa ya fice.

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button