Hausa Novels and Stories

Zafin Kai 3

Sponsored links

Sam Hande bata wani tsoro kaman ‘dan nata take duk shi kam na musamman ne a fagen taurin zuciyar da batada tausayi ko taushi ko kadan akan komai da kowa sai akan

 

qaruwarsa,dan haka kai tsaye hande ta fito tsakar gidan idanuwanta a kofa tana qwala kiran Ababa din da karfi sbd ya fito cikin sauri da shirin harbe kafar koma wane shegen ne ya shigo musu gidan…..bakinta kasa qarasa magana yayi lokacinda ta haske kofar da fitilarta me tsananin haske taga samirah dake dukan kofar cikin tashin hankali da neman mutuwa ta dauketa a lokacin idan bazata zamu kubutar tserewaba a daidai wannan mummunan lokacin.

 

Sam Hande bata wani tsoro kaman ‘dan nata take duk shi kam na musamman ne a fagen taurin zuciyar da batada tausayi ko taushi ko kadan akan komai da kowa sai akan

qaruwarsa,dan haka kai tsaye hande ta fito tsakar gidan idanuwanta a kofa tana qwala kiran Ababa din da karfi sbd ya fito cikin sauri da shirin harbe kafar koma wane shegen ne ya shigo musu gidan…..bakinta kasa qarasa magana yayi lokacinda ta haske kofar da fitilarta me tsananin haske taga samirah dake dukan kofar cikin tashin hankali da neman mutuwa ta dauketa a lokacin idan bazata zamu kubutar tserewaba a daidai wannan mummunan lokacin.

 

 

Cikin sauri idanuwa a rufe Ababa din ya fito yana saita doguwar bindigarsa da kofar ba wata wata ya harba da karfi ko ita handen bai tsaya cewa ta matsa daga gurinba saida qarar bindigar yasata zubewa qasa sbd babu abinda yake rabata da nutsuwarta da hankalinta ita kuma sai bindiga sanin aikinta ba wasa lahira take.

Safnah dake daki tun fitowar hande daga daki ta yanke jiki a gurin ta zube sbd mummunan tsoro da firgici mara misalin daya tsayar da bugun zuciyarta duk da ita a daki take boye dan haka kwatanta halinda samirah take ciki zaiyi wuya sbd fitowar mahaifinsu kafin ya harba bindingar zuciyarta ta tsaya cak qafafunta suka sare dan haka koda ya harba bindigar kofar gidan yayiwa mummunar fasawa sbd bullet dinta na fulogon mashin ne.

Cikin wani irin firgitaccen tsoro dukkaninsu dakin suka farka suna tashi zaune idanuwansu na rarrabuwa akan junansu sbd duk irin haka tafari junansu suke fara tabbatarda suna tare guri daya saisu nutsu basa fitowa matuqar ba cewa yayi su fito ba.

Benazir ce tafara bude baki tana rarraba idanuwanta dake wartsakewa daga bacci cikin tashin hankali da tsoro tace,

 

Shaqota yayi da wani irin karfi da zafi ya buga kanta da jikin kofar yana take qafafunta da nasa da karaji ya kira sunan Hande yace ina ta samu mukullan bude gidan?

Kallonta hande tayi cikin baqin ciki da takaicin tado musu da hauka da tashin hankalin Ababan ta miqe tsaye daga zubewar datayi rai bace tace,

 

Anne dake kusa da benazir qasa daukanta kafafunta ke kokarin yi amma benazir ta riqeta tana kokarin hanata bayyanarda masifar dake ragargaza zuciyarta akan ‘yarta datake kallo ana hallakawa amma babu abinda zata iyayi ko ikon dagowa ta kalla batada dashi dan haka takejin kaman ana zare naman jikinta ne daga qashinta,

 

Sumayyah da rauninta baya dauka tini ta zube qasa da rarrafe cikin tashin hankali da ficewa hayyaci ta koma dakinsu ta zube kusada safnah da har lokacin bata dawo daidaiba jikinta kerma yakeyi duk da babu qarar ihu ko kuka ko kadan dayake tashi sbd azabar datayiwa samirah din yawa gakuma daman horan daya musu duk tsananin azaba basa masa ihu ko kuka dan haka suka taso da iya riqe ciwo a zuciya da ciki.

 

Benazir ce kawai a tsaye kanta a qasa harya gama yiwa samirah din dukan mutuwa wanda ko hannunta bata iya motsawa bare wani sassan na jikinta

Sai alokacin safnah da sumayya suka fashe da wani irin kuka mai ciwo da radadi ba sauti,

 

Anne hawayenta bushewa sukai bayan ido data zubawa samirah din babu abinda take iyawa,

Benazir ma datake da jarumtar batada iyawa bayan hawayenta dake gangara da gudu masu tsananin zafi.

Haka suka zuba mata ido bayan jinin dasuka goge mata a jiki da ruwan zafi komai basida nayi mata dan haka suka ringa binta da addua har gari ya waye.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button