Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 25

Sponsored links

Ya faɗa a hankali da ƙara sakin ɗan wani murmushin da kauda fuska kai kace bayan shi akwai wani a ɗakin. Ƙoƙarin ture komai yake sai dai hakan kamar da wahala dan komai kokawar sake maimaita kansa yake tamkar a yau ne ranar ke faruwa (Idan hanunka ya sake gigin taɓa koda hijjab ɗin jikina ne sai na karyashi, Sannan koda Shahan-shan ne yay wannan aikin bai isa barin wajen nan ba balle kai shashasha driver”) (“Daga yau ko daga nesa kuka hangoni to ku canja hanya koda a jirgi kuke kuwa”). Idanunsa ya lumshe da kai hannu ya shafi tattausar baƙar sumar kansa. Sai kuma ya miƙe cike da ƙasaita yana mai ɗan sakin murmushin gefen baki da faɗin, “Drama queen”.

(☺️Da alama su Shanshani an shiga lambun fulawoyi🥱🚶)

“Mammah wlhy yarinyar nan ta fara bani tsoro nikam”. Daneen Ammarah ta faɗa da alamar tsoron da gaske a kan fuskarta. Murmushi Malikat Haseenat tayi har haƙoranta na bayyana. Sai kuma ta dubi Daneen Ammarah ɗin da ƙyau cikin ido. “Banda abin Ammarah minene abin tsoron anan to?…”

 

“Mammah akwai wlhy, ki dubi fa furucin da yarinyar nan keyi, ni gaba ɗaya komai ma neman ƙwacemin yakeyi. Ga shi tun ɗazu nake neman sister (Daneen Waheeda. Ƴar uwarta dake aure a yankin larabawa) amma wayan yaƙi shiga.”

 

 

Sosai Malikat Haseenat ta tsareta da idanu, sai kuma ta ɗan muskuta kamar mai son bada gargaɗi “Badai sanar mata zakiyi ba? Kirki ma fara wannan gamgancin, kin san dai halinta ko, fitinanniya ce ta gaske. Bata haɗa al’amarin duk wani jininta da kowa ba. Kuma kin san yanda ta nuna adawarta akan auran yarinyar nan da janta da mukai jikinmu tun farko saboda ƙin bata haɗin kai taƙi zuwa ko dubashi duk da labarin abinda ya samesa babu inda bai karaɗe ba”.

 

A sanyaye Daneen Ammarah ta jinjina kanta. “Hakane kuma Mamma, kiyi haƙuri wlhy abinne duk ya ɗaure mun kai. Ita waccan (Malikat Bushirat) da zamu iya tattaunawa kuma an riga an birkita al’amarin ta da zuga gaba ɗaya. Amma gaskiya furucin yarinyar nan ya matuƙar gigitani. Mita sani haka akan abinda kowa bai sani ba? Ta yaya ma ta sani ɗin bayan bata da alaƙa da wannan masarautar a lokacin da abubuwan ke faruwa. Anya kuwa Iffah ba aljana bace Mamma”.

 

Dariya sosai Malikat Haseenat keyi, sai da tai mai isarta ta tsagaita tana mai duban Daneen Ammarah da tai kasaƙe tana kallonta. “Babu wani aljana Ammarah. Mutumce kamar kowa. Kuma duk abinda kike tunanin ta sani ɗin a ɗan zaman nan nata ta fahimceshi. Ni kaina na san yarinyar hatsabibiya ce, sannan akwai wani ɓoyayyen al’amari tattare da ita mai girman gaske da ita kanta bana tunanin tasan akwaishi tare da ita”.

“Mamma kema fa kin fara bani tsoro”.

“To ko nima na zama aljanar?”. Malikat Haseenat ta faɗa cike da zolaya tana murmushi.

“Wayyo Mamma ni dai bance ba kar kisa jikanki ya tsireni a tsakkiyar masarautar sa. Kinga tafiyata”.

Da kallo kawai Malikat Haseenat ta bita tana murmushi. Tana matuƙar ƙaunar ɗiyar tata da tausayinta. Ammarah itace ɗiya mafi soyuwa a ranta. Dan ta haɗa abubuwa da yawa da ƴan uwanta basu da shi. Ga kuma ƙaddarar da ta sameta wadda har yanzu sun kasa fahimtar tushenta, duk da dai zuciyarsu na karkata musu wani abu daya shuɗe a rayuwarsu mara daɗin tunawa. Taja siririn tsaki da kauda al’amarin a ranta cike da ƙunar zuciya……

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button