Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 166

Sponsored links

Shine karshen shigowa. A take kotun ta sake nustuwa kayin kowa a kasa har sai da ya kai zaune.Kamar ko yaushe Sayeed Hanifud-Din ya fito hannunsa rike da takardu. Bayan yay gaisuwar girmamawa da Shahan-shan aka fara gabatar da Shariar.

“Bayan jiya kotu ta gama sauraren bayani da ga bakin Arshaan wata shari’ar mai alaka da juna ta sake shigowa a cikin zaman. Inda muka saurari babban al’ararin da ya rikita kowa har sai da aka yanke wannan zama da alkawarin yau za’a kawo karshen komai. To Alhamdullah domin tabbatar da abinda muka ji a bakin Arshaan. Da wanda muka ji a bakin dattijon nan gamu yau rike da hujjoji. Hujja ta farko zamu saurari recording din da aka shirya saurara a tun farkon shari’ar ta jiya hakan bai faru ba. To a yanzu zamu ji domin sake tabbatarwa. Sannan zamu gabatar da hadiman da sukai aikin kisan gilla ga Sayeed Khairul-Bashar bisa sawar su Jasim, da kuma bokansu mai suna Barbushi dorin jin karin bayani da ga garesu. Hakama bayanan wanna dattijo duk da a jiya Daneen Ammarah ta tabbatar mana da abinda mukaji itama wanna kotu mai adalci ta saka anvi gwaje-gwaje da zasu sake tabbatar mana da komai.,

Shugaban jami’ai bismillah”

Bayan shugaban jami’ ai yay gaisuwa ga Shahan- shan shima ya cika umarnin kotu na saka recording din da aka nada a zaman su Miran Jasim cikin kurkuku batare da sun sani ba. Kotu tai tsit kowa na sauraren kasancewar an saka speaker mai karfi a kowacce kusurwa kowa radam yake ji. Rikicin Miran Jasim da Miran Arshaan tun da ga ranar farkon kasancewar tare a cikin kurkuku daki-daki suna fallashe kansu da zagin juna da tsinema juna har zuwa jiya da safe. Tiryan-tiryan sai ga abinda Arshaan ya fada na fitowa harma da wanda bai fada ba. Jikin kowa da ke kotun duk sai ya kara sanyi. Yayinda aketa la’antarsu da ALLAH wadi da mummunar hallayar tasu duk da fa suma yan zaman kotun akwai masu wasu boyayyun al’amuran a cikinsu suma. Sai dai tunda tasu bata fitoba mai sauki ce. An fito da boka Barbushi shima da tunda aka kawosa masarautar aka rabashi da duk kayan tsafinsa aka aske masa kai da basa kaya bayan an sashi wanka. Gaba daya sai kamanin nasa suka canja kamar bashi ba. Sai faman sinne kai yake kuwa da satar kallon su Miran Jasim kamar yanda suma suke masa kallon mamaki. Shima yay gaisuwa ga Shahan-shan sannan Sayeed Hanifud-Din ya fara jefa masa tambayoyi.

Sayeed Hanifud-Din ya cigaba da fadin, “Kotu na bukatar jin duk tsiyatakun daka jagorancesu aikatawa”.

Cikin rawar murya data baki ya shiga zayyane komai. Da ga karshe ya dora da fadin, “Naki fada musu gaskiya ne tun farko saboda karsu daina bani kudin da suke bani. Amma ni nasan anfi karfinsu a duk inda suke kai hari. Bakuma zasu samu cikar burinsu ba har abada”.

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button