Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 118

Sponsored links

Ƙarfe goma da rabi na dare agogon ƙasar Iffah zaune gaban laptop ɗin ta, sanye take cikin suturar ta mai sirrinta jiki, iya zagayen ƙyaƙykywar fuskarta kawai ake iya gani. Tayi fayau ga mai kallo baka iya ganin komai sai damuwa da tsantsar ƙuruciyarta. Cikin girmamawa ta gaida dattijan guda biyu dake a fuskar lap-top ɗin tata. Miran Jasim da Miran Arshaan suka amsa mata da kulawa da nuna tausayawa tsantsa a fuskokinsu. Ita dai idanunta a rissine, dan tun kallo ɗaya datai musu bata sake yarda ta ƙara ba.

 

Miran Jasim yay ƴar gyaran murya da fara magana bayan gaisuwar tasu. “Ibnati mu mun sauke nauyin dake kammu naki, abinda kika yanke kawai muke buƙatar ji domin tsallakar da rayuwarki data ƴan baya. Dan a yanzu mun shirya tsaf ba tsafi ba ko bataliyar ifiritai Eshaan zai sauke a kammu domin danne cewarmu bazamu taɓa yin shiru ba”.

 

Iffah ta jinjina kai a hankali da faɗin, “Uncles naji daɗin hakan, kuma tun farko dama haka ya kamata ku kasance, duk da dai nasan bai zama lallai kuji irin zafin da iyayenmu sukaji ba. Amma a yanzu daya fara taɓaku gashi kun zaburo. Duk da haka bazamu ƙi karɓar taimakonku ba, dan a yanzu bani da wani abu dana tsana sama da shi, a shirye nake kuma na zama ajalinsa koda nima zan rasa nawa ranne. Sai dai ina son dan ALLAH uncle ka faɗamin gaskiya taya ka samu wannan videon? Ta ya kuma kasan na cikin videon nada alaƙa da ni ne? Miyasa kuke son taimaka mini? Miyasa duk da kun san yana kan rashin dai-dai baku taɓa wani yunƙuri ba a baya sai yanzu?”.

 

 

Kallon juna Miran Arshaan da Miran Jasim sukai kowanne ransa na susa da mamakin tsaurin idon wannan yarinya da sukema kallon hatsabibiya. Amma a zahiri sai Miran Jasim yaja ajiyar zuciya ya fesar cikin ƙoƙarin danne razanin da tambayoyinta suke neman jefasa. “Ibnati duk wannan ai na abin mamaki bane da har zai saka miki shakku, amma tunda kina son sani yanzu zakiji komai. Wannan video ɗin da kike gani na samosa ne a system ɗin Eshaan, bakuna shi kaɗai bane ba. Akwai ire-irensa da yawa harma dana yanda aka hallaka matansa na baya. Ina haɗasu ne domin miƙasa kotu a kwatarma masu hakki hakkinsu duk da ina fargabar ƙarfin iko irin na Shahan-shan bazai bari a hukunta shin ba kasancewar komai sai da say ɗinsa ke gudana a ƙasar ruman baki ɗaya. Sanin alaƙarki da wannan video kuwa ta samune duk a dalilin bibiyar tasa, sai dai bamu tabbatar ke bace ba sai a ranar da kika samesa tare da Arshaan Akh suna wasan takkubba. Sannan kasa tunkararsa a baya Ibnati bazaki gane ba, ƙarfin ikon Shahan-shan fa bana wasa bane ga kowa….”

“Tabbas hakane” Miran Arshaan ya amshe zancen. Batare daya jira cewar Iffah ba ya cigaba da faɗin, “Idan baki manta ba bayan kin basa shayi ya koma gefene yana kallo cikin masarauta, nima kina bani kuma na koma kusa da shi ina mai yabama tarbiyyarki da tabbatar masa yayi dace mace tagari data dace da shi a yanzu. Buɗar bakinsa sai ya sake tsaki da faɗin, “Tukunna dai, ai shi har yanzu matar da zai rayu da ita bata iso ba. Naji mamaki harna tambayesa ba’asin hakan amma sai bai tankani ba kin sanshi da girman kai. Zancen ya tsaya min a rai nazo na sami Jasim Akh da maganar, shine fa ya duƙufa bincike harya samu ganawa da kakanki da ke a ƙauyen Jumna”

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button