Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 148

Sponsored links

A yanda zaman shari’ar ma ya cika yau sai ya baka maraki. Dan tarin matasan nan a yanzu da Iffah ta dunkule waje daya bisa jagorancin Sayeed Fayzul- haq kaf dinsu sai da sukazo. Abinda basu taba yi ba tunda ake zaman shari’ar. Hakama wasu a mata da mazan masarautar sun karu. Kotu dai ta cika tai hani’an masha ALLAH.

Tsabar yau Iffah da jin kai ta shigo da yafi na kullum ma Shahan-shan ya rigata zuwa. Dan kusan itacema karshen shigowa da hadimanta. Nana kowa ya zuba mata ido harda uban gayyar ta cikin glasses din da ya boye idanunsa. A ransa kam kara jinjina fitinar yarinyar nan yake. Tafa rigashi kammala shiryawa amma tsabar taso neman magana sai ta gudu sashenta har sai da ya rigata zuwa kotun. Yau ma sai da taje ta gaida Malikat Haseenat da su Daneen Ammarah. Hakama Malikat Bushirat da tai wani irin ramar fita hayyaci da mai lurane kawai zai fahimta, dan abin dariya yau harda eyeglasses a idonta itama, da alama akwai abinda take boyewa. Hannu kawai ta dagama Iffah a maimakon amsa mata gaisuwa, ko a kwalar jikin Iffah tama mike abinta tana takun nan nata na neman magana.

Bayan nutsuwa kotu yanda ya kamata aka shigo da su Miran Arshaan. Sunyi duhu sosai sun rame. Ba duka ba zagi babu harara zaman duhun nan kawai da suka saka Iffah ciki a wancan karon da bakin cikin kamar su a cikin kurkuku ya maida su haka. Yan kananan magana ne suka fara tashi a kotun har sai da aka tsawatar. Ameera Haifah dai sai faman rufe fuska take da mayafi, gashi yau kuma harda iyayenta itama a kotun dan habanta yazo akan maganarta tun washe garin rufesu amma bai samu gain Tajwar Eshaan ba

Bayan kotu ta sake nutsuwa Sayeed Hanifud-Din ya karanto karar haka. “Har yanzu dai muna kan zaman shari’a ne akan Miran Jasim da ya bada madara mai dafi ga Zawjata-almilk ta shayar da wanda suke son halakawa. A wancan zaman kotu ta bada damar kawo bokansu a zama na gaba, sai kuma aka samu wani al’amarin akan Miran Arshaan da Ameera Haitah, wanda yay dalilin kaisu kurkuku suma, zaman makwaftakar Miran Jasim da Miran Arshaan ta zakulo wasu sabbin abubuwa masu ban mamaki da ya karata ace an fara saurare a wannan shari’a kafin a cigaba da yinta. Idan adalin shugabanmu ya bada damar hakan to”.

Hannu Shahan-shan ya daga a hankali da yin alamar an baka dama. Godiya Sayeed Hanifud-Din yayi sannan ya kalla shugaban jami’ an tsaron. Mikewa shugaban jami ‘an tsaro yayi, yayinda Miran Arshaan da Miran Jasim ke kallon juna a rikice, dan sun dai san karn kalar tabargazar da sukaira juna da tone-tonen tsiyatakunsu a cikin kurkukun. A hankali Iffah ta

 

saki wan irin sassanyan murmushi. Cikin Sa’a kuwa sai a idon su Miran Jasim din kamar an kirawosu su dubeta.

Kallon da Iffah ta musu shi ya kara girgiza zukatansu, sun kuma tabbatar akwai abinda shegiyar ke kullawa. Sannan recording din nan da akai musu

 

batare da sanin su ba in fa har aka budeshi kowa yaji anan akwai matsala. Dan basa raba dayan biyu zama a iya kashesu a cikin kotun nan kuwa. Saboda basa

 

tantamar duk abinda suka yi na tsiyatakunsu a cikin masarautar za’a samesa a ciki. Miran Jasim da yasan kwabarsa sai tafi ta kowa ruwa ya fashe da kuka yana

 

girgiza kai. Ya fahimci idan har ya mika wuya da kansa zai iya samun tausayawar mutane ma. llai kuwa tsitt kotun tayi, yayinda Shahan-shan ya dan jin jinama

 

Sayeed Hanifud-Din kai. Ya fahimci mi yake nufi, dan haka yay saurin dakatar da shugaban jami’ai da ke shirin playing recording din. Dakatawar kuwa yay cikin nuna girmamawa. Kotun tai shiru aka zubama Miran Jasim idanu. Shi kansa Miran Arshaan sakare yay kawai yana kallonsa dan ya kasa fahimtar ma’anar

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button