Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 159

Sponsored links

Tabbas hakane, yau kuma na kara tabbatarwa. Auran Ammarah da Zayyan abunne da bamu shirya masa ba, hakama samuwar wannan yarinya da rasata duk cikin tsarin UBANGIJN talikai ne. Baku aikata laifin komai a garemu ba face taimako. ALLAH kuma ya kaddara Zayyan matsayin miji ga Ammarah dan ya sanar damu abinda bamu da ilimin saninsa. Lallai jini ba karya bane ba. Dan tun a randa na fara ganin Fhareedah naji kaunarta mai karfi a raina, hakama mahaifiyarta. Komin kankantar al’amarin da ya shafeta Ammarah bata wasa da shi. Zuciyata ta fara rawa a kanta a lokacin da was al’amura nata ke kamanceceniya da Ammarah. Sai dai ban san ta ina zan kamo al’amarin ba balle na bashi fassarar da ya dace da shi. Dan ko’a randa mijinta yazomin da batun tambarin tawadar ALLAH dake jikinta irin na wannan zuri’a al’amarin ya jima yana mun kai kawo da kasa banbance makamar rikewa. Hakan yasa a cikin watan azumin nan dukkan addu’oina suka karkata ga al’amarinta. Sai gashi ya sake zuwa min da batun gwaji, yau kuma gashi kun tabbatar mana da komai ALLAH ya saka muku da alkairinsa, ya baku kariya fiye da wadda kuka zama sanadin bama wanna yarinya da ahalinmu bisa zartarwar UBANGIJINMU da ya sakaku zama sanadi. Yanda UBANGIJI ya hada jininmu a duniya, muna fatan ya hadamu a aljannarsa.Ina farin ciki matuka da kasancewar Fhareedah a cikin jikokina jinina, dan ita abar so ce ga kowa”.

 

 

A tare duk aka amsa da Amin kowa na sharar kwalla. Kafin kuma rikici ya balle tsakanin Ummu da Mammy (Daneen Ammarah) akan Iffah. Ummu ta tabbatar har yanzu Iffah bata sauya ba kuma bazata taba sauyata matsayin wadda ta haifaba a zuciyarta ba. Tana mata kauna irin wadda takema su Hanash, dan haka bafa zata barma Daneen Ammarah ba. Itako ta marairaice mata akan tunda ta dana na shekara goma sha tara itama ta barta tai goma sha tara sai a koma yar sati-sati. (Iffah mai iyaye da yawa😂) Dariya Kaka da Mammah da lyyani da Hanash, Daneen Waheeda suka dinga yi musu. Shi dai Babiy kansa a kasa yana murmushi kawai, lokaci-lokaci yakan saci kallon Mammy din kamar yanda itama take satar kallonsa. Ummu duk tana lure da su, amma sai bataji komai na jin zafi a ranta ba sai ma tausayi da suke bata. Hakama Malikat Haseenat tana lure da su. Sallar la’asar ce ta tada zaman. Fuskar Iffah murmushi da hawaye sun kasa tsayawa. Ana dawowa da ga salla sashen Tajwar Eshaan suka nufa gaba dayansu bisa umarninsa. Kallon Iffah da duk tayi wani sukuku yake ta kasa ido zuciyarsa cike da tausayinta. Tun dazu hankalinsa na kanta, ko abinci bai iya ci ba sai madara kawai da ya dan sha kadan, yata tsammanin shigowarta amma shiru, dan haka ma yama Malikat Haseenat aiken son ganinsu gaba daya. Yau dai kam gasu Baby ga Shahan-shan a zahirancensa dan ko eyeglasses babu a idanunsa ma. Sun mika gaisuwar girmamawa a garesa yayinda shi kuma ya amsa musu da mutuntawa. Sun kara tattaunawa sosai inda shi babu wata kwana-kwana ya bukaci jin ta bakin Babiy da Mamy (Daneen Ammarah) akan maida musu aurensu. Diri-diri sukai su dukansu kamar wanda suka shiga rudani da maganar. Yayinda Kaka da Malikat Haseenat ke murmushi, hakama Hanash da Iffah kallon juna sukai sai kuma suka saki murmushi. Jin kowa ya kasa cewa komai Ummu da tai shiru kanta a kasa ta dago fuskarta da murmushi. Cike da nutsuwarta ta ce, “ALLAH ya karama adalin shugabanmu lafiya da tsohon rai mai albarka. Idan akai hakan tabbas zamu kasance a cikin farin ciki, dan an mutuntamu da karamci mafi girma da ba’a tabama wani a wannan kasa ta ruman ba. Nima zanso kasancewa da yar uwata kodan karta kwacemin yarinyata, why zan shiga wani hali”. Ta juya ta kama hannun Baby dana Daneen Ammarah cikin roko tace, “Dan ALLAH karku bani kunya ku amince mu sake zama abu daya

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button