Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 85

Sponsored links

Yanda ya barta haka ya dawo ya sameta. Yanzun ma baiyi wani motsin da zata farka ba har ya kammala zame kayan jikinsa ya canja da ƙananu. Bathroom ya nufa ya haɗa ruwa na musamman sannan ya dawo gareta. Kai tsaye ya kunna wutar ɗakin da ta haske ko’ina ko allura kuwa ka yarda kaga abunka. A hankali yake bin ɗakin da kallo tamkar yau ne karo na farko da ya fara kasancewa a cikinsa. Ya ɗan saki murmushi yana mai lumshe idanunsa da sake buɗewa. Shi kansa ɗakin ya ƙara zama mai wata irin daraja da kima ta musamman a garesa, dan ya zamar masa ɗaki mafi zama ƙololuwar sirri sama da duk sauran sirrikansa. Dubansa ya kai ga gadon inda Iffah ke ƙudindine sai faman sauke ajiyar zuciya take yi cikin barcin wahalar da take yi. Magiya roƙo neman agajin da ta dinga jera masa na dawo masa daki-daki, da’ace gilashin ɗakin nan ba mai hana fitar sauti bane babu abinda zai hana a daren na jiya gaba ɗaya daular ruman su jiye masa sirrinsa, dan bakinta bai mutu ba sai da ta sume masa. Ya ɗan sake murmusawa da takawa sannu-sannu kamar wanda baya so zuwa gaban gadon ya zauna gefenta. Fuskarta da tai luɓu-luɓu na kukan data sha ya shafa yana kaima lips ɗinta da sukai bushewar wahala sumbata. A firgice ta farka tamkar ɗazun, ta saki wani irin wahallen kuka da jujjuya kanta tana mai jero masa roƙon ya barta, dan ALLAH ya barta karya kasheta bazata iyaba. Yanda take yi ɗin dole ne ya baka tausayi, dan a kallo ɗaya zaka fahimci har yanzu bata cikin hayyacinta. Shi baima san ta ina zai fara ba duk da ya jima da shiryama irin wannan ranar ba tun yau ba, amma a yanda yaje mata shi kansa yasan ya jigata ta, irin jigatawar da da’ace wani ne ya aikata aka kawo masa ƙara sai ya hukunta mutum. Sai gashi shi da kansa ne, shi da kansa ya kasa control ɗin kansa yay ma ƙaramar yarinya kamarta zuwa har uku a dare ɗaya duk da ta kasance tamkar jaririya a hannun uwa garesa.

 

“Shiiii!!” ya faɗa a hankali yatsansa kan lips ɗinta. Riƙeta yay da ƙyau tare da manna mata wata sumbar a goshi kafin ya miƙe cak ya ɗagata zuwa bathroom. Wata gigitacciyar ƙara ta saki jinta a ruwan zafi tana rirriƙesa azaba na ratsata, jikinta sai rawa yake shi kansa har abin ya bashi tsoro. Dole ya shiga cikin ruwan shima ya rungumeta a jikinsa. Kuka take matsananci da ƙoƙarin ganin tabar jikin nasa amma ya hanata damar hakan. Kansa ya dafe yana riƙota jikinsa da ƙyau cike da takaicin kansa, sai dai kuma shima ba laifinsa bane, gaba ɗaya idanunsa ne suka rufe, duk wani haƙurinsa da jarumtar da yake dannewa a tsahon shekaru sai da suka amayar da kansu. Tunfa yana da shekarun da basu haura ashirin ba yake dakon wannan matsalar, taya ma zai iya tuna abinda ya dace yayi a wannan gaɓar, ta yaya, ta yaya ake son ya tuna..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button