Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 181

Sponsored links

Cikin matukar farin ciki na qyara zama, na shiga zayyano mata haihuwa nake so, dan ina son zama Malikat bawai Zawjata-almilk ko Ameera kawai ba. Ni wannan matsayin duk yamin kankanta. dariya sosai ta shiga babbagawa har sai da na koa dan haushi amma dai na hakura na shanye. (Lallai ke abokiyar tafiya ce). Ta fada tana nunani har lokacin fuskarta da sauran daiyar. Murmushi nai mata cike da jin dad. Ta cigaba da fadin, (Nice da kaina na hana Haysam haihuwa saboda abinda uwarsa ke mun, idan tana takama ita Malikat ce dan ta haifi Miran mai jiran gado na shirya tabbatar mata komai a gidan nan sai da karfin ikona yake tabbata). Hakuri na dinga bata nidai, dan babban burina kawai bukatata ta biya nidai. Cikin tabe baki ta furta, (Ai kin wanke komai yar gari, indai zaki iya bin sharadinmu ki dauka kece Malikat a wannan karnin). Babu wani tunani nace na amince da duk wani sharadin ta tunma kan ta fada min su. Nan ma dariya tayi sosai kafin ta ajiye min wata takarda da koko mai dauke da jini wai a saka hannu da wannan jinin, itama zata saka wannan itace yarjejeniyar mu ta farko, Banji ko wani dar ba na saka ta saka. Ta bani daya ta dauki daya tana fadin, (Daga yau sunanki a wajenmu shine *_Ta-kurya_” ta kurya sa maza kurya kenan). Yar dariya nai ta farin ciki itama tana tayani. Ta wuce a ranar batace dani komai ba acewarta sai zama na biyu. Na matukar nustuwa a sati na uku da babu ita babu labarinta, dan haka na shiga bulayin nema. Harma a fiddla rai ranar kawai sai gata ayam ta kawo min ziyarar dare kamar wancan lokacin. Kafin nace komai ta tabbatar min doka ta biyu bayan suna dolene a duk sanda ta bayyana a gareni zansa gwiwuna kasa dan girmamawa a gareta, sunan da zan dinga kiranta da shi shine uwa. Nan ma babu musu na amince mata. Nanma dariya tayi kafin ta ajiye min kullin garin magani guda biyu. (Wannan sune maganin matsalarki Ta-kurya, daya zaki sha daya ki shayar da Miran Haysam. Ina mai tabbatar miki kafin watan ya mutu zaki samu ciki) na matukar kasancewa a farin ciki, sai kuma nai sansarakwai da ga baya na jeho mata tambayar to amma idan ya kasance wata a cikinsu nada ciki fa ko kuma muka samu cikin tare na haifi mace ita namiji?

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button