Hausa Novels and Stories

Zamani Complete Hausa Novel

Sponsored links

“ _Ashe burika basa qare ba indai kana da rai!_😭

 

_Ance me nema na tare da samu ya zan fidda rai!!_

 

_Wata tsoka tanamin ciwo cikin jikina!!!_

 

_Ba abin naje a yanke ba kuma na rasa Raina!!!_

 

_Yanayi na sone ne kamar yake shigana!!!_

 

_Naga ko yaushe inna ganki sai na kasa komai!!!_

 

_Na zamo kamar gashin daya fada cikin mai!!!_

 

_Inna kalli fuskarki zanso na qara maima!!!_

 

_Tsigar jiki takan tashi bana qyanqyami ba!!!_

 

_In dingajin gabana na faduwa bana matsorata ba!!!_

 

_Wata qila Ina alhinine zakibar gurin….”_

 

Ɗala masa duka akayi tare dayin tsaki me dukan yace “gaskiya Safwan ka gamu da wahala kawai kazo ka tisa TV a gaba ka sanya stop kana waqe majigi Anya kuwa baka samu matsala da sanyin nan ba?”

 

Wata qaqqarfar ajiyar zuciya ya sauke ya miqe ya kashe TV ya dafa kafadar abokin nasa yace “bazaka ganeba Sulaiman ka share kawai” zama sukayi suna kallon juna ya share gumin da yake tsattafo masa duk da sanyin A.C dake ratsa dakin yace “zan iyayin komai saboda Harmdan Abu daya yake damuna rashin sanin taqamaiman inda zan sameta Sman inajinta a cikin jinina ne kawai”

 

Dariya Sman ya kwashe da ita yace “shiyasa kullum nake cewa ka haukace Safwan karasa wacce zakaso sai wannan fitsararriyar yarinyar yar Film wacce batasan ciwo da mutuncin kanta ba haba haba kaikam meye ma yake neman rudarka har tunaninka ya kwance”

Bai katseshi ba har saida ya ida sannan yayi tsalle ya fada gadonsa yace “ _ke na riqa a zuciyata har yau ban sanya wata ba kuka na rashin ganinki har yau bai barni ba!_”

 

Yana gama rera wannan baitin ya dauki wayarsa ya fara duba istagram ya saki wani ihu yace “zo kagani ta saka sabbin hotuna wlh yauma nine zan zama na farko da zanyi comment” da sauri ya rubuta “you are beautiful” cikin saa tana online taga dm dinsa ta bude tayi smiling tace “tnks dear” wani ihu yayi yace “am a lucky man Sman tayimin mgn wayyoh momsy ta kulani wayyoh Harmdan a like you”

 

Gabadaya abokan nasa guda biyu suka kwashe da dariya Hussain yace “zautacce wlh haushi kake bani anya ma kuwa bakada matsala bansan meye yake burgeka da banzar…..” Zabura yayi ya miqe yayo kansa ya shaqesa yace “wlh ka zagi Harmdan a gabana saina zubar maka da haqora naga uban daya tsaya maka” tsaki yayi ya koma ya zauna ya fara downloading din hotunan ya dora wani a wallpaper dinsa wasu a status cikin 30 seconds friend suka fara yimasa comments da maganganu mabambamta comment din salis yafi kowanne daukar hankalinsa da yake cewa.

“ _aboki Allah yabaka Harmdan_” wani murmushi yayi daya sanya kyawawan haqoransa bayyana yace “amin abokina inason Harmdan baso irin na kasancewarta Celebrated ba so na aure, zan iyayin komai a duniya domin Harmdan don Allah ka tayani binciken inda zanga Harmdan”

 

Sanin cewa idan ba hirar Harmdan yajashi da itaba bazai bashi lkc ba yasa Salis yayita janshi da Hira sai gashi ya sake sunata Hira harda dariya kafin su tsayar da cewa zasuje Senimer yau da dare zaa haska sabon film din jarumarsa tashi yayi ya sauko ya ishe Mom da qannensa biyu suna zaune a parlour ya matsa tsakiyarsu ya zauna kusa da Mom yana shafa Kai tayi tsaki tace “Idan naganka kana murmushi nasan da mgn Safwan ya akayi ne?”

Sake shafa kansa yayi yace “kinga Mom yau ma tasa sabon hoto har nayi Mata comment ta amsamin….” Wata dariya qannensa suka fashe da ita harda Dad dinsu da ya tsinkayi shirmen dannasa yana saukowa yace “duk mgnrka bata wucce ta wannan yarinyar Safwan kana wahalar da kanka please tashi muje ka kaini airport zan tafi Abuja daganan zan wucce Saudi nayi umara”

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tsuke fuska yayi ya miqe yana qunquni yace “haba Dad don Allah ya zaka batamin burget dina Senimer fah zamuje nan da 30 minutes zaa haska sabon film din Harmdan….”

Daquwa uban yayi masa yace “saboda zuwa Senimar ne bazaka kaini ba banson sakarci maza je ka shirya ka fito mu tafi” tuni ya rikide ya zama kalar tausayi ya kalli Mom dinsa don yasa ita kadai zata iya canzawa Dad raayi itama ta kawar dakai hakan tasashi hayewa saman cikin sanyin jiki yana qudurta a ransa shifa yau bazaije airport dinnan ba,

 

Haka kuwa akayi tun Alh Barau yana tsaye har saida ya zauna jiran Safwan Amma Shiru bai fitoba ya dubi Mom yace “Sakina Kinga danki yaqi bazai kaini ba da gaske” dariya sukayi tace “ai garama kasa yarannan su kaika don wlh indai Safwan ne akan wannan fitsararriyar yarinyar ba kaika zaiyi ba nifa so nake sanyi ya wucce idan naga bai nutsu ba asibiti zankaishi a bincikamin qwaqwalwarsa

Jinjina Kai Alh Barau yayi ya kalli Safiyyah da Nafeesah yace “ku tashi ki kaini airport” daidai lkcn daya sauko cikin shirinsa yana maqale da Bluetooth headphones a kunnensa yana daura agogo yana cewa “ok Salis kawai ka jirani a bayan park ganinan inaso a fara haskawa a gabanmu….”

 

Hankalinsa yayi gaba yama manta da mgnr Kai Alh Barau airport ya fice da sauri yayiwa mota key ya figeta a guje ya rigasu ficewa, tsaki Safeeyyah tayi tace “maloho kawai ko ubanme yake burgeshi a wannan yar iskar yarinyar” tabe baki Nafeesah tayi tace “kema dai kya fada Amma nifa lamarin Bros ya fara bani tsoro kinsan jiya dana shiga dakinsa ko Ina hotunanta ne ya kafesu baitin waqa kuwa yayi mata yafi kala dubu yananan a wani littafi idan mun dawo zan dauko Miki ki gani”

Alh Barau ne yayi gyaran murya yace “wai budurwa yayi ne?” Zaro ido sukayi Safeeyyah tace “tabdi Dad inafa budurwa wata sabuwar celebraty ce Hamdan Ghana itace duk ta rudashi zancensa aikinsa baccinsa komansa itane idan kaji suna musu akanta da abokansa abin sai yabaka haushi hotuna kuwa duk Wanda ta dora a IG dinta ko Twit shine mutum na farko da yake Mata like ko comment”

Miqewa yayi zaune yace “zan ajiye komai da kowa zan bar kowa da komai saboda Harmdan zan nemeta tsakanin duniyar mutane da aljanu koda zatace bata sona indai zan ganta saina furta Mata na kasa samun farin ciki saboda ita Salis qaddarar ta wahalar dani ne yasata shiga harkar film tabbas zanyi duk abinda zai kusantani da i

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button