Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 24

Sponsored links

Sameer yafi 30mins yana dialing number Deen amma no answer yake ta cewa,daga bisani aka kashe wayar gabadaya… Sosai yaji hankalinsa ya kasa kwanciya da rashin daga wayarsa da Deen yakeyi,a take ya yanke shawarar dole ya tafi Nigeria a yau dinnan,tuno da yawan ayyukan dayake dashi a office kuma yasa yajisa in dilemma,toh wanne zeyi wanne ze bari?…. Bin shawarar zuciyarsa kawai yayi ya yanke barin komai ya tafi Nigeria,abu daya ne ze hanashi tafiya a yau that’s if there’s no available flight.. Luckily yana duba online yasamu flight din 2pm,ba tareda bata lokaci ba ya siya ticket.. Tada motar yayi ya nufi gidansa domin ya shirya…

Tinda sameer ya fita khaleel yaji komai na duniyar nan ya tsaya masa chak,idan wani zai fadamasa sameer can do this for him cewa zeyi karyane amma a gaban idonsa sameer ya kallesa yake fadamasa shima yanason mahadin rayuwarsa?,oh no! This is something he can’t take! Kuma ko shakka bayayi in game zasuyi shi zaici barema bazai bari abun ya zama game ba dan yafi karfin yayi game da sameer…. Sam bayajin fatima zainab dan yasan bazata kula sameer ba,audacity din sameer ne ya bata masa rai…. Girgiza kai yayi yana fadin “Kafi kowa sanin yanda nake sonta amma ka zabi kamin haka,I’ll make sure the game gets over even before it’s started,dani kake zancen!”……

8:30pm ya sauka a Nnamdi Azikiwe Airport ,Abuja… Number Deen ya sake trying ko Allah zaisa ya shiga but still switched off…. Bolt yayi ordering ya shiga suka nufi Transcorp Hilton kasancewar few days back da sukayi magana da Deen ya fadamasa yana chan, har room number dinsa ya sanarmasa,sannan ya fadamasa he’s not going back to kano anytime soon….. Shiga cikin hotel din yayi ya nufi room numbern Deen ya shiga knocking,yafi 20mins a tsaye kafin ya koma reception to make enquiry….. Sundai tabbatar masa da Deen bayanan tin safe,daganan kuma basu karaba dan basa bada information akan mutum…..

Sameer ji yayi gabadaya abin duniya ya ishesa na rashin samun deen,ya tawo nanma still be gansa ba?,he has high hope akan Deen kasancewarsa very smart person so yana ganin Deen yasan everything is solved,toh shi yanzu ta ina ze fara neman Deen?….

 

Lodging yayi shima a hotel din saboda yanda yakejin gajiya sosai….. Wanka da sallah yayi sannan yayi ordering abinci daga hotel restaurant… Koda aka kawo abincin sai yaji duk baya shiga,turewa yayi ya sake dialing number Deen,yanzu kam not available ma yake cewa…. “Shit!” Ya fada indai Deen baya abuja he can be in Kano,bama can be bane indai Deen baya Transcorp to lallai yana kano,wai ya akayi ya mantane? Shida yakamata ya tafi gidansu Deen na kano sai ya tsaya tinanin ze gansa a abuja?…. Mikewa da sauri yayi yana hada kayansa daya dan bude… Airport ya nufa straightly,ko tinanin zai samu flight ko bazai samu beyi ba?….

 

Kamar yayi kuka haka yaji da yaje gaban canter akace there’s no available flight for abuja to kano,hakanan ya hakura ya siya ticket na gobe sannan ya koma Transcorp……….

 

Tin bayan sun fesa masa wannan abun be kara sanin inda kansa yakeba… Bude ido yayi kawai yagansa a wani makeken daki na alfarma,da salati a bakinsa ya tashi ya zauna,kalle kalle ya shigayi yana bin dakin da kallo,wani dariya ya saki yace “Wai ni zaayi kidnapping,lallai mutuminnan!”…. Murmushi ya sakeyi sanin wanda ze iya masa haka,dole kuma ya dau mataki saboda an fara wuce gona da iri,but before then he has to leave this house dan haduwarsu da wanda yasa akayi kidnapping dinsa a yanzu kam hadari ne,sannan zaa lalata masa budget,be manta da itaba,be kuma manta da san sanin WACECE ITA ba,saboda hakan nema yasa bayasan haduwa da kidnapper dinsa a yanzu,yafiso ya gama da ita sannan yayi facing koma wani consequences ne ze biyo baya tsakanin shi da wanda yayi kidnapping dinshi…

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button