Hausa Novels and Stories

Nihad Chapter 12 Hausa Novel

Sponsored links

Tsaye Khalil yayi bakin kofa yana kallonta with a weird facial expression, bata sake yarda sun hada ido ba banda faduwa babu abinda gabanta yake, sai kuma ta hade rai xata durkusa ta dau wayarta da ya fada saman jakar, yayi hanzarin shiga cikin dakin ya sa kafa yayi changing position din jakar yana kallonta, tana ganin haka ta bi jakar cike da tsiwa tace “Wai kai yaushe na fara wasa da kai a gidan nan ne da xaka dinga raina ni haka? ina ruwanka da kayana ko a saman titi na jefar da xaka ta6a min, how dare you?” Tana fadin haka ta ja tsaki ta kara dukawa zata dau wayar, ya dauke jakar a wajen, buda baki tayi tana kallonsa da mamaki, sai kuma ta nufesa da nufin cakumosa yanda ta saba amma ganin kallon da yake mata sai kawai ta tsaya tana harararsa, cike da rashin kunya tace “Wallahi idan baka mika min wayata a dakin nan ba xan maka sharrin da har abada baxa ka mance ba, ka bani wayata nace…”

cikin kakkausar murya yace “Idan kin fasa…” Ta kankance ido tana kallonsa da mamaki jin abinda yace, ji take kamar ta kifa masa mari, da a waje ne wllh ba abinda xai hanata marin sa, Yana mata wani kallo ya ajiye jakar a gabanta yace “Idan kin isa ki ta6a” A fusace tace “Toh wai kai idan kana sata sai ka rasa wayar warce xaka sata sai tawa a gidan nan? A kaina satarka xai kare? Idan na ta6a uban me ka isa ka min? Wllh sai na ma sharrin da baxaka ta6a mantawa da ni ba” Duk wannan babatun da take bata yarda ta ta6a jakar ba, banda faduwa kuma babu abinda gabanta yake barin da ta ga irin kallon da yake mata, jakarta dake gefen gado ya nufa ya dauka ya dawo inda take ya jefa mata a gabanta yace “Dauki ki fita… Abubuwanki dake ciki xa su fi wayar muhimmanci gare ki” Kamar xata yi kuka tace “Ni wllh ka bani wayata kar in hadaka da Abbana da yayana” Da Husky voice yace “Dauka jakar ki nace ki fita” Bata ce masa komai ba ta tafi ta dau jakarta tana jin kamar ta fashe da kuka, ta nufi kofar tana tafiya a hankali, ta gefen ido ta saci kallonsa sae kuma ta dawo da gudu ta fixgo jakarsa ta nufi kofa a guje kamar an aikota, tana shiga parlorn plate din da su Isiya suka ci abinci suka bari a wajen ta take sai da ta tafi tsuuu kamar xata tashi sama sae ga ta a kasa timm, jakarsa kuma yayi can hanyar kofar fita, nata kuma yayi wajen Tv, gwalo ido tayi tana numfashin wahala da kyar tace “Wayyoo Abbana, wayyo bayana ya karye” tsaye yayi bakin corridor din dakunan ya rungume hannunsa ya jingina da pillar din wajen yana kallonta irin dai dai kenan, ta fashe da matsanancin kuka tana jujjuya kanta tace “Wayyo Allah na a zo a taimakeni bayana ya karye, baxan iya tashi ba” karasowa cikin parlon yayi zai tafi ya dau jakarsa, tana ganin haka ta yunkura ta tashi ta nufi kofar da gudu ta figi jakar tasa, a dari da sittin ta fice ko bin ta kan nata jakar bata yi ba a parlon, bai san sanda ya bi ta ba, tuni har ta dau hanyar kitchen yace “Keeeee dau wayarki ki ajiye min jakata” haba da ya kara tuna valuable dinsa dake jakar kawai ya bi ta, tana isa kofar kitchen ta murda ta ji sa a kulle, ta gwalo ido tace “Na shiga uku, Hafsahhhh uban wa yace ki kulle” tana ganin ya nufota kawai ta ajiye jakar a kasa tana kallonsa xuciyarta na bugawa, yana isa gabanta ya duka ya dau jakarsa sannan ya bar wajen.

 

Nihad bata san sanda ta fashe da kuka ta sulale wajen ba tana cewa “Wallahi sai na maka rashin mutunci a gidan nan, kawai mutum kamar maye ya sa min ido a gidan ubana duk ya bi ya takura ni” Sai kuma ta mike ta xaga ta shiga cikin gidan, Umma dake parlor ta kalleta daga sama har kasa tace “Lafiya?” Nihad tace “Ina Hafsah?” Sai ga Hafsah ta fito daga bangaren Mumy, Nihad ta nufeta tana huci tace “Ke mahaukaciyar wace gari ce da xaki rufe min kofa bayan kinsan na fita?” Hafsah tace “Ayya kiyi hakuri wllh ban san baki shigo ba, na xata kin bi ta gaba kin shigo” Nihad ta mata tsawa tace “Aa ta hancinki na bi na shigo” Tsaki ta ja ta juya ta bar wajen kamar xata tashi sama. Umma dai ta bi ta da ido, direct dakin Nihal ta tafi, Nihal har ta gama shiryawa tana kallon Nihad tace “Ohk baxa ki rakani din ba” Nihad tace “Nihal idan na fara yi ma wancan driver din rashin mutunci ke ce ta farko da ke fara jin haushi, wllh duk abinda na masa kar ki ga laifi na, don haka tun wuri ki je ki samesa ki amso min wayata da jakata dake wajensa” Nihal dake kallonta with confusion tace “Me ya kai jakarki da waya wajensa kuma?” Nihad tace “How will i even know?? I mistakenly dropped my bag at the gate jiya, ko sani ma ban yi ba….” Nihal ta katseta tace “How will u mistakenly drop a whole bag not even purse Nihad?” Nihad ta hade rai tace “And that is none of ur concern, kawai abinda nace maki shine ki amsar min kayana a wajensa kar in fara rashin mutunci na, don wllh idan bai yi hankali ba sai na gaura masa mari kuma ba abinda xai faru” Dariya ta ba Nihal, sai dai bata yi ba, tace “Ke yanxu wa yace maki shi ya dau maki jaka?”

 

Nihad tayi saurin cewa “Aminu ne ya gaya min, kuma don’t forget wayana na ciki” Nihal tace “Amma ai ba yaki bane, xa ki iya samunsa politely ki tambayesa jakar, na tabbata xai baki” Nihad ta yi wani dariyar rainin hankali tace “Koh? To sannu, shi drivern xan je in sama politely sbda ina tsoronsa ko? To abinda baki sani ba, Aminu ce min yayi satar jakar yayi niyyarsa yayi shiru, bai kuma san Aminun ya gansa ba, to idan yana sata sai ya fara ta kan kayana a gidan nan? Kaii amma mutumin nan ya kara bani tsoro wllh” Nihal ta dau karamin handbag dinta tace “Yamma na yi, xan tafi shopping” Nihad ta hade rai tace “Ohk baxan raka ki ba kenan?” Nihal tace “Oh na xata kince ai baxa ki ba” Nihad ta harareta tace “Yaushe nace maki haka?” Nihal tace “Toh dauko hijab dinki mu tafi” Nihad bata ce komai ba ta juya ta fita, Nihal ta bi bayanta, babban dalilin da yasa Nihad xata shopping din nan kawai don Nihal ta amsar mata jakarta da wayanta gun khalil, Nihal na fitowa parlor Umma tace “Har kin shirya auta?” Nihal tace “Eh na shirya” Umma tace “To kar dai ki manta turarena” Nihal tace “Toh baxan manta ba” Umma tace “To ya kika tsaya, ga yamma na yi” Nihal tace “Ina jiran Nihad” Umma ta kalleta tace “Nihad? ita tace maki xata?” Nihal tace “Eh” Umma tace “Ke da xaki yi maza kije kiyi abinda xai kai ki ki dawo, meye kuma sai kun yi zuga kamar yan matan amare Nihal”

 

Nihal tace “Aa nafi son mu je tare” Umma tayi shiru bata kuma cewa komai ba, Nihad ta fito sanye da Hijab ita ma, Tana kallon Nihal tace “Mu je” Nihal ta kalli Umma tace “Sai mun dawo” Umma tace “Allah ya tsare” Nihad tace “Umma xa a taho maki da wani abu ne?” Umma tace “Aa babu komai, Allahj ya tsare” Fita suka yi daga parlon, Nihad ta hade rai ganin khalil da Aminu, Nihal ta nufesu tana kallon khalil tace “Idan baka yin komai xa mu iya tafiya yanxu?” Ya mike yace “Ohk” Motar ya nufa, Nihad ta bi sa da wani shegen kallon tsana, duk Aminu na lura da ita, Nihal ta bude front seat xata shiga Nihad tayi saurin cewa “Me xa ki yi a gaba ke kuma?” Nihal tace “I prefer seating here” Nihad ta ja tsaki ta bude back seat ta xauna, Tuni mai gadi ya bude gate din suka fita compound din, Khalil yace “Wani supermarket din xa mu Hajiya?” Nihal tace “Ko wanda ya fi kusa” Nihad tace “Kai Malam mu tafi Sufi Mart” Khalil dai driving dinsa kawai yake, next thing kawai Nihad taga ya dau hanyar wani store din daban, ta kankance ido tace “Wai kai kurma ne baka ji inda nace ka kai mu bane?” Driving dinsa kawai yake kamar bai san da shi take ba, Nihal ta juya ta kalleta tace “But ai duk daya ne Nihad” Nihad ta galla mata harara tace “To da ke nake ke kuma?” Nihal ta dauke kai bata ce mata komai ba, A Danja Khalil ya sauke glass din motar ya amshi facemask hannun wani yaro sannan ya basa kudi ya kulle glass din, Nihad ta kyabe baki, sai kuma ta ja tsaki ba dai wanda yace mata komai a motar. Parking Khalil yayi a inda aka tanadar don parking a harabar Supermarket din, ya kashe motar yana kallon Nihal, tace “Baxa mu dade ba in sha Allah” Nihad tace “Toh da kike cewa haka wa xai dauko kayan idan mun gama siyayyan? Ai sauka shi ma xae yi daga motar ya kwaso kaya ba wai zama xae yi a driver seat ba” Nihal ta kalleta tace “But the staff in there will do that, it’s not necessary” Nihad tace “Wallahi u have a very big problem, what is then the use of him?

 

Why then did he have to drive us here if he can’t come out and help? Sannu good Samaritan” Nihal ta kalli khalil tace “Sae mun fito” Yace “Toh a fito lafiya” Ta bude motar xata sauka yace “Amma bari in sa maki number ta idan kin gama sae ki kirani in dau maki kayan” Tace “Akwai masu daukan kayan a ciki kar ka damu” yace “Toh idan da wani abun sae ki kirani” Tace “Toh” wayarta ta mika masa yayi dialing number din sa sannan ya mika mata, amsa tayi ta kira number, karamar wayar dake aljihunsa ya fara ring, tace “Nagode” daga haka ta bude motar ta sauka, Nihad dake ta kallon ikon Allah ta ja tsaki me tsayi sannan ta sauka, ko barin wajen motar basu yi ba tace “Me ye na wani exchanging digit da driver idan ba kaskantar da kai ba Nihal? Me yasa ke kin fiye over sabi a rayuwarki? Ni ban san me yasa ke da Mumy ku ke yin haka ba wllh” Nihal taki tanka mata, Nihad tace “Though wannan ba damuwata bace, my problem is ban ji kin masa maganar jakata da wayana ba?” Nihal tace “Xan yi” Suna shiga mall din, Nihal ta fara daukan abubuwan da ta xo siya tana xubawa a cart Nihad na tura mata cart din, duk inda suka gifta sae an kallesu don babu wanda bazai ce su ba yan biyu bane, they look so cute, beautiful and adorable, kawai dai Nihad ta fi Nihal haske da tsayin hanci with more cute lips, ita kuma Nihal ta fi Nihad cika, though she isn’t chubby but ta fi Nihad warce iska me karfi idan aka yi xae iya tafiya da ita… Lol, tsayinsu daya haka ma shape din large eyes dinsu, sae dai kana kallonsu kasan Nihad tafi Nihal wayewa nesa ba kusa ba, ganin Nihad isn’t taking anything Nihal tace “But kince kema xa kiyi shopping kin fasa ne?” Nihad ta yatsina fuska tace “I won’t shop here” Nihal bata kuma ce mata komai ba, har ta gama daukan duk abinda xata bukata a makaranta, sannan ta dau ma Umma turarurrukan da tace, wani tsadadden turare da ta san Nihad na so ta daukar mata, Nihad ta amsa tace “Thank you” Daga haka ta saka shi cikin cart din, Nihal ta dau wayarta tayi dialing number da Khalil ya sa mata with the intention of asking him a question, can kuma dae kawai ta katse ta fasa kiran nasa sbda Nihad dake ta kallonta, wasu turarurrukan biyu ta deba ta sa a cart sannan tace “Shikenan na gama” Nihad ta tura cart din suka nufi counter. Suna tsaye counter din Nihad tace “Na manta xan dau Sanitary Napkin” Daga haka ta juya zuwa in da zata dauka, khalil ya shigo cikin mall din with facemask, yana hango Nihal a counter ya nufi wajen yana kallonta yace “Naga kiran ki…” Nihal tace “Oh bansan ya shiga ba” Yace “Ohk, sun gama in dau kayan?” Xata yi magana kawai wata yarinya kamar balarabiya ta nufosu tana kallon Khalil closely tace “KJay?” Juyawa yayi da sauri, Ta wara ido kafin ta ce komai yace “Ohh Nadiya, daga ina haka?” Ta kyalkyale da dariya tace “How wonderful i recognized u upon the nose mask KJay…” Ya kalli Nihal da sauri yace “erm, yi hakuri don Allah minti daya…” kawai yace “Mu yi magana a waje Nadiya” yana fadin haka ya bar wajen da sauri, Sai a sannan Nadiyar ta kalli Nihal dake ta kallonta daga sama har kasa, Nadiya ta daga mata hannu tace “Hi” Nihal tayi murmushi ta daga mata hannu ita ma, juyawa tayi ta bi bayan khalil da har ya fita mall din, Nihal ta bi ta da kallo, har gadon baya ta saki dogon baƙin gashin kanta, daga ganinta kasan half cast ce, sae ga Nihad ta ajiye Sanitary Napkin din a kan counter, tana kallon Nihal sai kuma ta kalli inda take ta kallo amma tuni Nadiya ta fita daga mall din, Nihad tace “What are u staring at?” Nihal ta dauke kanta da sauri tace “Nothing” ma’aikatan wajen ne suka kwasar masu kayan xuwa mota bayan an biya kudin kayan, Khalil na jingine jikin mota ya rungume hannunsa, ganin sun fito ya xaga ya bude booth din motar, wanda ya tayasu fito da kayan ya shigar cikin booth, Nihal ta bude handbag dinta ta dau dari biyar ta basa, yayi mata godiya sannan ya wuce, tuni Nihad ta shige bayan mota, Nihal ta xauna gaban motar, ya tada motar suka bar shopping mall din.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button