Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 69

Sponsored links

A ɓangaren Daneen Ammarah ma dai a rikicen take. Sai dai ita nata lissafin yasha banban da nasu Malikat Haseenat. Daga ɗakin taro bedroom ɗin Malikat Haseenat ta wuce zaman jiranta. A zaman da bai wuce mintuna arba’in ba kuwa sai gata. Kallo ɗaya taimata ta ɗauke kai. Hadimar dake biye da ita ta ajiye madarar hanunta da zubewa ƙasa tana gaida Daneen Ammarah. Hannu kawai ta ɗaga mata….

“Na matuƙar gajiya, kwanciya kawai nafi buƙata”. Malikat Haseenat ta faɗa tana wulla kekenta hanyar bathroom ɗinta batare data sake kallon Daneen Ammarah ba. Da kallo ta bita cikin shakku da shan jinin jiki. Dan duk da a dunƙule tai magana tana nufin bata bukatarta a ɗakin kenan. Jiki a sanyaye ta miƙe ta fice zuciyarta na faman tsalle-tsalle…

Duk yanda taso kwanciya ta kasa hakan, fargaba da tausayin Iffah ne ke matukar ɗawainiya da ita. Har cikin zuciya bata son rasa yarinyar dan ta matuƙar shiga ranta. Soyayya take mata irin ta ƴa da uwa. Ita kanta har takanyi mamakin yanda takejin Iffah a rai matuƙa, amma tasan wannan ƙaunar daga ALLAH ne kawai. Wayar dake a hannunta ta ƙara rumtsewa, ta gwada kiran Iffah ya kai sau huɗu kenan amma tana fasawa, so take taji lafiyarta ko zata samu ƴar nutsuwa, amma wata zuciya na gargaɗarta da kalmar rashin dacewa….

“Mi wannan tsohuwar ke nufi wai shin? Ko itace abin neman mu kamar yanda barbushi ya sanar mana?”.

Miran Arshaan yaja numfashi ya fesar, kamar bazaice komai ba sai kuma ya kafe Miran Jasim da kallo yana girgiza kai. “Wlhy kaina ya kwance Jasim Akhi. Na kasa gane komai a wannan gaɓar, abinda na sani kawai shine mutuwar yarinyar nan a wannan gaɓar tamkar mutuwar cikar birinmu ce, dan na gama ɗora dukkan hope ɗinmu a kantane. Bai kamata ta mutu a yanzu ba har sai ta ƙarasa mana aikin da muka kwashi tsahon shekaru muna ginawa”.

“Miye mafita?”.

Cewar Miran Jasim a firgice, dan zantukan Arshaan ɗin kamar sun zaburar da shi ne abinda ke gabansu. Kai tsaye Miran Arshaan yace, “Ziyartar Barbushi a wannan daren, kafin waccan sankaran matar da ban san amfaninta a tafiyarmu ba tazo ta ishemu da tsarin banza”.

“Hakan yayi mun, babu amfanin ɓata lokaci kaje kayi shiri”.

Kai Miran Arshaan ya gyaɗa masa, tare da mikewa ya fice. Da banzan kallo Miran Jasim ya bisa, cikin ƙanƙance idanu da wani shu’umin murmushi a fuskarsa “Ba matar can bace kawai abin banza a cikinmu, har da kai Arshaan, daka gama mun amfani zan kawar da kai, dan ni kaɗai nake son mulkar daular ruman batare da ɗan uba ko ɗaya ba da zai zame min abokin gaba, nasan idan har na barka kaima zaka zamemin maƙiyi dan burinka wannan kujerar ne na sani shashasha”

Duk da akwai wani ɗan ɓurɓushin tsoro a ƙasan zuciyar Iffah ta matuƙar dakewa da addu’a ta shiga ɗakin bayan ta gama ƙarema bangon dogon corridor ɗin da suka biyo kallo, ta jinjina kai cikin jin matuƙar ƙuna da tausayin talakawan ƙasan ruman baki ɗaya. Tayi imanin akwai dubbunan mutane dake barci akan titi cikin yinwa da ƙishirwa da yawa. Amma abin mamaki yau ga bangon ɗakin barcin Shahan-shan yasha ado da zinari matsayin fenti, “Taya ma imani zai zauna a zuciyar mutanen nan har su ɗauka rai wani abun mai daraja?” ta faɗa a zahiri idanunta na cika da ƙwallar baƙin ciki da ƙara jin tsanar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed……….✍️

(😭Hikenan Iffahr mu an shigo ɗakin mutuwa😱🙆)

Ko miye dalilin Malikat Haseenat na kai Iffah turakar Shahan-shan kai tsaye haka? Miye dalilinta na canja abinda suka tattauna da su Malikat Bushirat? Shin ko dai malikat Haseenat ce T….😱🤫🤭?.

Yaya zata kasance tsakanin Iffah da Shahan-shan ne? Ta wani ɓangaren abinda ke kashe Zawjata-almilk kuna ganin zai ƙyale rayuwar Iffah a wannan dare kuwa?.

Gadai wasu ɓoyayyun maƙiya na sake fitowa. Irinsu Miran Arshaan (mijin Jasrah kuma ƙani ga Tajwar Haysam) da Miran Jasim (shima ƙani ga Tajwar Haysam). Shin wacece wai matar nan da suketa a ambata batare da sunanta ba?.

Hhhh tabbas yanzu ne wasan zai fara. Sai ku shirya ku sake shiri dan sai a yanzu ne muka kalmashe bakin shimfiɗar labarin dake cikin littafin DAUƊAR GORA… Wasan na asali yanzu ne filin yinsa ya kammala. Masoya sai mu antaya kawai😉🥱🏇🏇🏇🏇.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button