Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 91

Sponsored links

Hawayen da take riƙewa ne suka ziraro, ta girgiza masa kai alamar bazata iya ba. Komai bai sake cewa ba, sai riƙo hanunta mai riƙe da kofin madarar yay cikin nasa tare da kofin, bakinsa ya kai ya sha madarar. Ta

 

masa matuƙar daɗi fiye da duk madarar da yake sha. Still dai hanunsa nakan nata da kofin ya sake kaiwa ya sha. Sai da ya sha kusan sau biyar sannan ya kai bakinta itama.

“Hhah”.

Ya faɗa a narke yana wani irin busa mata iskar bakinsa kan idanunta da suke mar-mar, gaba ɗaya neman daburcewa take.

“Kina so na buɗe da kaina?”.

Da sauri ta girgiza kai da buɗe bakin kaɗan ya ɗaura mata kofin. Kaɗan tasha ta janye, sake ɗaura mata yay. Babu yanda ta iya dole ta cigaba da sha. Bai barta ba har sai da ta shanye duka sannan ya ajiye kofin. Naman ya ɗauka shima ya shiga bata yana ci har suka cinye tare da shanye romon ma duka a tare.

“Sai mi kuma?”.

Ya faɗa yana riƙo hanunta a nashi. Fuska a shagwaɓe ta ce, “Barci”. Murmushi yayi tausayinta da ƙaunarta na sake mamaye shi, sannu-sannu ya kai hanunta kan lips ɗinsa, babu zato taji saukar kiss a tsakkiyar tafin hannun. Idanunta ta rumtse da ƙarfi tana matse jikinta dan har cikin ɓargo sumbar ta shigeta. A tare suka sauke ajiyar zuciya, tai ƙoƙarin zamewa zata kwanta ya riƙota jikinsa. Tsam-tsam ya rungumeta yana shinshinar wuyanta da busa mata numfashinsa da ke saka tsigar jikinta yamutsawa.

 

Luf tayi tana mai shaƙar daddaɗan kamshin turarensa mai saka zuciyar mai shaƙa nutsuwa, yanda yake hura mata iska a cikin kunne da murza yatsun hannunta dake cikin nashi tuni barcin da keta rinjayar idanunta ya fara tasiri kanta. Jin jikinta ya saki gaba ɗaya ya sashi ɗan sakin murmushin ta sake gyarata ta kwanta da ƙyau, cikin abinda bai wuce mintuna biyu ba numfashinta ya fara sauka a hankali alamar barcinta yay nisa. Numfashi ya ɗan furzar da gyara filos ɗin gadon ya kwantar da ita. Lumsassun idanunsa ya zuba mata batare da ya ɗago da ga ranƙwafawar da yay a kanta ba. Wasu kalamanta ne na jiya suka shiga dawo masa a rai, wani lallausan murmushi ne ya suɓuce masa ba shiri, ƙoƙarin haɗiye kayansa yay da sake matsawa da ƙyau jikinta ya sumbaci goshinta da hancinta da lips ɗin da sai da ya ɗan juya su a cikin nasa sannan ya saki. Bargo yaja ya lulluɓe ta da ƙyau ya miƙe…

Koda ya fito falon bai saurari abincin breakfast da aka shirya masa ba. Hakama Daneen Ammarah bata falon, sai amintaccensa kawai da ke dakon fitowarsa. Gaisuwar amintaccen hadimin nasa ya ke amsawa yana nufar lift.. yayinda shima yake biye da shi da hanzarinsa.

 

Fada ya fara nufa cikin takun nan nasa ɗaɗɗaya na izza da ƙasaita. Shigowarsa da aka sanar tun kafin ya iso ya sa duk wanda ke a wajen miƙewa kai a ƙasa har sai da ya kai zaune. Suma duk zaman sukai cike da girmamawa suka shiga miƙa gaisuwa suna satar kallonsa dan yay musu wani fayau da sake cikar kamala kamar wanda akaima wankan inji. Saɓanin ko yaushe kuma yau fuskar da ɗan sassauci duk da bawai dariya yake ba ko murmushi. Tana nan dai kadaran kadahan bata tsuke sosai ba bai kuma saketa ba. Kamar ko yaushe amintaccensa ne ya amsa da yawunsa. Da ga haka aka ɗanyi zaman fadanci masu ƙorafe-ƙorafe suka kawo yana saurarensu. Hakama masu shawara akan masarautar ko wani abu da ya faru harma da wajenta. Na masarautar dai duk sun samu rinjaye ne akan abinda ya faru tsakanin Miran Jasim da iyalansa.

Komai baice akai ba, yana dai jinsu da kunne bisa ra’ayinsu har gardama ma ta ɗan nema sarƙewa sai da Sayeed Anwarus-sadat ya tsawatar. Baice komai game da rashin ganin Miran Arshaan ba, shima kuma Miran Jasim ɗin da aka sanar masa ya matsa an sallamesa tun a daren jiya baice komai ba a kai. Zaman gaba ɗaya bai wuce na awa biyu ba lokacin sallar zuhur yayi….

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button