Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 2 Page 15

Sponsored links

“Nafi buƙatar ganin murmushin akan ƙyaƙyƙyawar fuskar Ammie-na a kowace daƙiƙa ta numfashi na. Akasinsa kan ƙona zuciyata fiye da yanda wuta ke narkar da kitse.”

Kalamansa koda a taƙaice suke zinarai ne a zuciyarta, shi ɗin yafi hasken diamond walwali da ƙyalli a cikin idanunta a duk sanda take dubansa, ta so abubuwa da yawa kafinsa ciki harda mahaifinsa sai dai shi tamkar shafine dake shafe dukanin fejin sauran fejikan baya a littafin rayuwarta. Kafin ka buɗe a bangonta shine, a shafin farko da shi take shimfiɗa, tsakkiya da ƙarshe shine mafi girma a ababen yabonta da ƙaunarta. Ta sake sakin murmushi zuciyarta na sake risina da ga fushin da ta baro sashenta a ciki.

Malikat Bushirat wata irin mace ce da gane halinta sai wanda ya santa, tana da abubuwan ban mamaki ta na da kuma na ban tsoro harma dana ban sha’awa da suka kasance mafi rinjaye a yimata ado. Hamshaƙiyace ta gasken gaske dan ko’a cikin manyan matan dole a kirata *_ZAKANYA UWAR ZAKIN ƘASAR RUMAN_*. A yanzun ma halin dattakon nata ta nuna, ta hanyar shanye dukan tarin abubuwan bakin nata ta cigaba da bama ɗanta magajin mijinta mai amsa suna shugaban sarakunan ƙasarta kulawa har zuwa lokacin data gamsu zata iya magana da shi babu fushi a harshenta. Ta tsatstsaresa da idanunta masu kaifi irin na uwa, yayinda shi nashi ke a rissine gareta risina irin ta ɗa a gaban mahaifiya.

“Na kasa gane komai da ga Mammah dangane da al’amarin yarinyar, a sanina ita ke fara hukunta duk wanda ya zaɓi cutar da kai koda da mummunar magana ne, kuma koda ni da na haifeka ce. Amma a wannan lokaci sai ta zaɓi bama mai son kawar da numfashinka kariya batare da fahimtar da ni kaina hujjarta akan hakan ba. Shin taya ake tunanin zan iya haɗa numfashi a ƙarƙashin runfa ɗaya da wadda ta shirya kawarmin da abinda bani da madadinsa ko samin madadinsan ba har abada? Taya ake tunanin zan iya kawaicin barinta da cigaba da kallonta a matsayin Zawgatu al-ibn duk da yunƙurinta na son ganinta ta tarwatsani da tai? Idan har igiyar aurenka da ke kanta ne katangar da ake iya min nuni da ita bango gareta ina son ka rusheta, ka yanketa, yankewa ta har abada ibn Haysam Abdul-majeed. Dan hakan shine kawai zai iya bani nutsuwa na manta da komai”.

Da ɗan ƙarfi ya matse idanunsa yana mai sakin numfashi a harɗe, sai dai mai kallo da ido bai isa fassara kamilar fuskarsa ma’abociyar annuri da kwarjini ba hatta ita dake amsa sunan mahaifiya a garesa…..

“Yanke hukunci cikin fushi da rashin haƙuri akan bincike ba itace ɗabi’ar shugaba nagartacce ba”. Daneen Ammarah ce dake tsaye mai maganar tana ƙoƙarin shigowa ɗakin, da alama ta ji dukkan kalaman Malikat Bushirat ɗin. Bai motsa ba, hakama bai buɗe idanun nasa ba harta ƙarasa shigowa garesu, sai dai ya sauke wata irin ɓoyayyar bahaguwar ajiyar zuciya acan cikin maƙoshinsa. Jin shiru ya ratsa ɗakin ya sashi buɗe idanun sannu-sannu. Dukansu cikin ɓacin rai suke kallon juna kowa najin ya isa yana kuma da ƙarfin iko akan yaƙin. Abune da babu wanda zai ce ya taɓa gani a tsakaninsu sai a wannan lokaci, ciki kuwa harda shi kansa. Daneen Ammarah ta sake katse yanayin nasu ta hanyar ɗora hannunta a kafaɗar malikat Bushirat da alamu suka nuna ta gama kaiwa maƙura a fusata..

“Úht!”.

(sunan data kan kirata da shi wani lokacin)

“Ban sanki da garaje ba, ban sanki da kasa fahimta ba, ban sanki da munana zato ba. Ban sanki da dagiya ba. Ina roƙonki ki danne, ki jure, ki zama mai ƙarfafa gwiwar mai ƙarfin da ba ƙarfin akafi son ya gwada ba kai tsaye, saboda amsa sunansa na shugaba. Bazan musa miki sunan Fareedah matsayin mai laifi ba, amma zan so ki kasance a yanda na sanki wajen tabbatar da gaskiya akan kowane ne kafin zartar da hukunci. Muma ba burinmu hana a hukunta ta ba, ko fifitata sama da gudan jininmu kuma shugabanmu ba, so muke kawai abi tsarin da ya dace da dokar shari’a da muke fata bayan ita za’a iya tono waɗan da ma suke aikata ɓarnar baya mai barinma gudan jininmu baƙin fenti da tabo a rayuwarsa da rayuwar mulkinsa. Ki fahimci Mammah ba fifita Fareedah take sama da abinda ta cancanci fuskanta bane, kariya take bata matsayinta na tamkar makamin da zai iya zama zaren da zai jamu ga duk ɓoyayyun masu laifin da muke fatan kamawa a cikin hannayenmu. Shin baki ji a ranki wanda suke aikata ta’asar baya nada nasaba da na yanzu ba? Baki ji a ranki yanke mata hukunci a kallonta ita kaɗai mai laifin tamkar basu ƙwarin gwiwar cigaba da aikatawar bane koda kuwa a yanzu basu da hannu kan abinda yarinyar ta aikata? Shin baki tunawa shi shugaba ne ba mai azaba ba?. Da yawan mutane gani suke sakacinsa da ƙin bama abu muhimmanci koda mai muhimmancin ne halayyarsa, sai dai yanda yake yi shine cikar zama cikakken duk wani shugaba.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button