Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 60

Sponsored links

★Iffah ta daka tsallen murna bayan ficewar Daneen Ammarah, harda ƴar rawarta. Duk wani tunani da kaikawon da zuciyarta ke mata akan Shahan-shan zuwan wannan waya da lap-top ya kauda mata shi. Domin a ganinta dama biyu ce tazo mata a lokaci guda kuma zata damata ta yanda dole sai Shahan-shan ya shata. Yanzu dai abu na farko da zata fara shine malam Fawzan. Ta tura masa saƙo bayan nemansa da tai shi da abokinsa wayar Arfa dake hanunta ta mutu ba caji, tana buƙatar tasan ko yaga saƙon? Ya kuma iyayenta suke?.

Samun wayar da caji yasa tun a daren ta haɗata, duk da taga akwai sim card batai amfani da shi ba ta cire na Arfa ta sanya. Tamkar jira saƙon Malam Fawzan ne ya fara shigowa, jikinta har tsuma yake wajen buɗewa. Batako kai ƙarshen karantawa ba kira ya shigo. Gabanta ne ya faɗi ganin baƙuwar lamba, amma tsabar ƙarfin hali sai ta ɗaga.

“Sir!”.

Ta faɗa cikin gwalalo idanu da nufar ƙofa da sauri ta saka key. Daga can aka amsa mata da “Na’am Fareedah. Ina kika shiga haka? Tun bayan ganin saƙonki na kasa samunki, har zuciyata ta karaya da ko wani ya gano ki ne?”.

“Babu wanda ya gano ni Sir, akasi aka samu wayar ta mutu, na kuma rasa ta yanda zanyi cajinta dan na manta da cajan a gida”.

“Ayya. Kin ganni akoda yaushe cikin gwada wayarki nake koza’a dace. Saboda ke na samar da wannan layin na sirri. Yanzu ma gwadawa kawai nake amma banyi tunanin samunki ba sam”.

 

Iffah ta share hawayen da suka silalo mata tana ɗan murmushi. “Nagode Sir, koda banyi nasara ba bazan taɓa mantawa da kai ba. Ina fatan ka bincika min su Ummu. Dan sam na kasa samun kwanciyar hankali na rashin jin su”.

 

Ɗan jimm yay kamar mai tattaro abin faɗa, sai kuma yay ɗan murmushin basarwa. “Suna lafiya dan har gida naje, sai dai ban samu shiga ba kasancewar suna tare da tsaron dakarun masarautar har yanzu. Amma nayi ƙoƙari mun haɗu da Hanash….”

 

“Amma miyasa wayoyinsu basayi?”.

 

Ta katsesa a ƙagauce. Da ƙyar ya iya tattaro abin faɗa a wannan gaɓar ma. “Shi Babiy wayarsa ta samu matsala ne. Hanash kuwa network ne dan yace min shima yasha nemanki amma baya samunki”.

 

“Bani da lafiya ne, ba koyaushe kuma wayar ke kunne ba. Amma yanzu zan sake nemansa insha ALLAHU dan ina matuƙar bukatar son naji muryoyinsu kozan samu nutsuwa”.

“Hakan yana da ƙyau. ALLAH kuma ya ƙara lafiya. Kinyi waya da abokina kuwa?”..

“Eh nayi, amma kamar yanda na sanar maka a text message an ɗaga amma ana mun wani shirmen banza. Daga ƙarshe ma akace wai na saɓa lamba”.

Karan farko malam Fawzan yay ƴar dariya. “Taku ne kawai irin na masu iyawa. Amma a yanzu na tabbatar zai saurareki”.

Iffah ta ɗan taɓe baki kamar tana gabansa. “Ni ALLAH harna ɗauka ko ka yaudareni ne ka bani number daba itaba ma”.

Iffah koda abin wasa kikazo da shi bazan masa riƙon banza ba balle wannan mai matuƙar muhimmanci da ma’ana. Yanzu dai ina fatan wayar taki akwai caji?”.

“Ai bama waccan bace, sabuwa fil aka bani a kwali yau harda lap-top”.

Jimm yay na wasu ƴan sakkani. Sai kuma ya cire wayar a kunnensa ya duba. Tuna ashema shine ya kirata ya sashi sake maidawa. “Amma baƙya zargin akwai wani dalili a baki wayar? Mutanen nan fa sunada haɗari sosai Iffah. Bazan ɓoye miki ba inajin tsoron ƙarfin ikonsu”.

“Nice zan baka wannan labarin Sir kasancewata a cikinsu yanzu. Sai dai kuma wanda suka bani wayar yanki ne na mutanen kirkin cikinsu. Kasan a ko ina akwai ƙyakykyawa akwai kuma mummuna”. Tsaf ta kwashe yanda sukai ta sanar masa saboda ta matuƙar yarda da shi. Shine kuma takema kallon wanda zai taimaka mata a wannan yaƙin kamar yanda tai fata. Ya jimanta al’amarin matuƙa, ta wata fuskar kuma yayi murnar ganin hanyar samun nasararsu ce tazo.

 

“Lallai mun samu hanya ta jifan tsuntsu biyu da dutse ɗaya Iffah. Sai dai dole kiyi taka tsantsan da waɗan nan wayoyin. Ki buɗe account da duk kike ɓuƙata da layin da suka sanya miki, shi kuma wannan nakin watsap kawai zaki buɗe da shi, sai dai karki barsa akan wayar, da kuma kinyi magana da Ajmaal da shi ki goge watsap ɗin ki cire layin sai zaku ƙara ki maida. Akoda yaushe wayarki ta kasance da security na idanunki bana wayar ba. Dan inada tabbacin suma zasu saka ido a kanki. A daren nan ki buɗe watsap ɗin ki sake ma Ajmaal magana

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button