Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 33

Sponsored links

Wani irin ihu mama ta saki ta mike ta fita a guje,binta fatima zainab tayi itama,parlour mama ta nufa tana tafe tana sakin fitsari,imaan da husna na ganin mama ta fito a guje,suma suka mike,fita daga part din suka soyi gabadaya amma kafin su karasa fatima zainab ta rigasu,ta kuma sawa parlourn key,juyawa da sauri imaan da husna sukayi mama na biye dasu a baya suka nufi sama,binsu tayi a nitse har suka karasa bedroom din dake sama ita kuma ta rufe kofar parlourn sama,husna da imaan ne suka shiga bedroom din dake saman suka kulle,mama ko kafin ta karasa sun rufe kofar kasancewarta katuwa yasa bata iya gudu sosai,gashi dama bedroom daya ne a sama saitarasa inda zatayi… Bubbuga kofar dakin take tana fadin

“Husna kutaimaka ku budemin in shigo karta kasheni,wallahi fatalwa ce” Ta fada jiki na rawa tana kuka wiwi

“Mama kiyi hakuri bazamu iya budewa ba,dama ke take nema kar kuma ta hada damu”…

Mama tanajin haka tace “Wayyo Allah na mutu na lalace” Sai kuma ta zube a sume!!!

Ganin mama ta suma yasa tayi wani ball da ita,sai ga mama ta tafi wul wul wul sannan ta diro kasa,a take ta farfado daga suman datayi. Birgima mama ta hau yi tana fadin…….

“Aiko dole ki tafi inda kikaso aikani”……. Fashewa da kuka mama tayi a haukace tace

 

“nashiga uku dama baki mutu ba?”…

 

“Kin dauka zaki iya kasheni ne lokacina beyiba,toh idan naso yanzu yanzu sai na kasheki,kuma na kashe banza wallah”…….

 

 

“Wayyooo Allahna dan Allah kiyi hakuri karki kasheni sharrin shedan ne,wlh na tuba”……

 

Mama ta fada tana jan jiki,tana kallen kallen inda zata iya shigewa ta boye…..

 

“Ku mutane dama haka kuke,shedan na zaman shi a gefe sai ku kirashi ku sakashi a lamarinku alhalin ba ruwansa,toh ki bude kunnuwanki da kyau ki saurareni”…..

 

Fatima zainab ta fada tana zama akan kujera sannan ta dora kafa daya kan daya

 

“ Ashe ke mahaukaciya ce,dabbiya,mara hankali,mara tinani,shashasha wacce batasan meke mata yawo a brain ba? Toh ni bazan kasheki ba danni ba jahila bace irinki,amma ki sani dole zan dau mataki akan ki”….

 

 

Ta fada tanayiwa mama wani mugun kallo,ita ko mama sai kallon kofar kitchen take tana tinanin yanda zatayi wuff ta shige

 

“Badai saboda daddy kike duk wannan abun ba? Toh dole zaayi dayan biyu,ko daddy ya karasa tsige igiyar dayake tsakaninku inga babu alakar komai a tsakaninku ko kuma in auresa sai muyi zaman kishi da hujja,kiga yanda zansa ya wulakantaki san raina daga bisani kuma insa ya tsinke igiyarku gabadaya sannan ince ya sakeni in auri danku!”……

Mama ji tayi kamar an buga mata dutse a kokon zuciyarta,ai in daddy ya yanke duka igiyarsu tashiga uku,sannan ko a mafarki bazatayi kishi da fatima zainab ba dan wallahi tafi karfin tayi kishi da sa’ar ‘ya’yanta kome ze faru kuwa! Tunowa tayi da tariga ta gama da daddy yanzu,kuma sai abunda tace yasa ta yin wani murmushin azaba jin yadda jikinta ke mata ciwo,ita Allah yasa ma bata samu karaya ba,dan tindazu take kokarin shigewa kitchen amma takasa motsawa,nishi tayi tace

“Wallahi nafi karfin inyi kishi dake,kuma aurenmu nida alhaji mutuka raba takalmin kaza,baki da labarin sai yanda nayi da alhaji yanzu”

Mama ta fada tana fuzgo maganar cikin tsoro da fargaba…..

Wata muguwar dariya fatima zainab tayi tace

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button