Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 47

Sponsored links

“K! Ubanwa ya kawoki nan?”.

Ta faɗa da zaton cikin hadimai ne irinta. A hankali iffah ta karasa takowa gabanta, tare da janye mayafin ta saka idanunta cikin nata jajaye marasa ƙyan gani. Sosai hadima banou ta rikice har rawar jikinta ya bayyana. Iffah ta janye idanunta daga kanta ta maida akan ramin,

“Mi kika binne?”.

“Ranki ya daɗe babu komai, w… W… Wani magani ne kawai da nake son yin amfani da shi…..”

“…..Shine kika shuka shi anan cikin rashin gaskiya? Wacece ke? Mi kike kullawa”.

Tambayoyin sunma Banou yawa da tsauri wajen bada amsa, a take ta sake gigicewa duk da tana ƙoƙarin ƙirƙirar jarumtar dole. Wuceta Iffah tai zuwa wajen ramin, ta tsugunna da daukar iccen datai tonan da shi ta shiga sake tone kasar da Bismillah. Firrr wani abu kamar tsintsuwa ya fito a ramin yay sama. Iffah ta mike da sauri ta bisa da kallo harya bace. Juyawa tai da sauri inda Banou take, dai-dai ko tayi shirin silalewa tabar wajen ta dakatar da ita.

Ƙasa tai da kanta jikinta na matukar rawa, Iffah ta kare mata kallo sama da kasa na wasu sakkani, sai kuma ta girgiza kai. “Wani asirinne haka bizne tsuntsuwa da ranta saboda son zuciya? Ko wani ya sakaki biznewar saboda ya isa? Kokuwa ke ɗin kina a cikin jinsin Mayu ne? Dan a cikin ukun nan dana lissafa dole ne a samu ɗaya tattare da ke tsohuwa”.

Kuka Banou ta fashe da shi gwuyawunta a ƙasa. “Ranki ya daɗe ban fahimci abinda kike nufi ba, nifa magani na shuka ki yarda dani”.

“Uhhm wato magani kika shuka, tsohuwa kalleni da kyau ki ganni banyi kama da wanda akema rufa ido ba, amma zan baki lokaci kije, zan nemeki a lokacin daya dace. Idan kika hangi gudu baki da wajen iya ɓoye min, idan cutar dani ne zagaye nake da kariyar UBANGIJINA, idan yunkurin salwantar da rayuwarkine idona biye yake dake tako ina. Shawara ya rage gamai shiga rijiya”.

Da wani irin mummunan kallo hadima banou tabi bayanta da shi, ta cije baki da rumtse jajayen idanunta da karfi……

Komai daya faru tsakanin Iffah da Hadima Banou akan idon Daneen Ammarah ne, dan itama tayi yunƙurin fitowar ne ganin Banou na tono a bayan windown Mamman sai ta hango Iffah na tahowa. Kasancewar ta ganta da rigar jikinta a ɗazun yasa kai tsaye ta ganeta. Da farko gabantane ya fara faɗuwa da tunani iri-iri, shiyyasa ta tsaya domin

ganema idanunta. Sai dai kalaman Iffah da yanayin Hadima Banou ɗin ya sata shiga ruɗanin tunani. Idan har zata auna da hankalinta matsayin babba itama Iffah taga Hadima Banou ne shiyyasa ta fito, a yanayin Banou kuma ya nuna akwai wani ɓoyayyen al’amari na rashin gaskiya tattare da ita. To amma su maiyasa a tsahon shekaru basu taɓa ganin wannan fuskar ta Banou ɗin ba? Wacece Iffah? Anya kuwa ba akwai abinda ya kamata ta sani dangane da yarinyar nan ba?……

★Iffah da al’amarin wannan masarauta ya fara ruɗama tunani tana shiga ɗakin dake matsayin nata yanzu ta murza key. A jikin ƙofar ta jingina da lumshe idanunta tana sauke numfashi. Ita kanta taga ƙarfin halinta yau, dan zata iya rantsewa bata san a ina ta samo wannan jarumtar ba. Idanun ta buɗe tare da riƙe ƙugu ta karyar da kai alamar nazari. In fa har ta canka dai-dai tabbas wannan hadimar mayya ce. Dan bata manta da wani labari da Iyyani ta taɓa basu ba na mayya yar Danƙo datai zamani a kauyen jumna shekarun baya. Babu banbanci da abinda taga matar nan tayi yanzu, dan da alama kurwar wani ta laso tazo ta boye a wajen. “Bahun ubancan, eh da gaske dai ashe lamushe ƴaƴan mutane ake a masarautar nan tunda ga alama harda su bayi an barbaɗa musu muguwar tambaya. Shi baƙin babban dodon nasu nacinye mutanen gari su kuma bayi nacinye junansu a cikin gida”. Tai maganar a fili cikin ƙankance idanu na alamar tunzuruwa…

 

Murmushi Daneen Ammarah dake bakin ƙofa tsaye ta saki, dan nutsuwar da zuciyarta ta kasa mata ya sata biyo bayan Iffah, har ta kai hannu zatai knoking sai kuma ta fasa da tunanin inhar Iffah nada wani mugun nufi a kansu to baro can zata samu wani abun take aikatawa a yanzu. Dan haka ta ɗan kara kunenta kaɗan jikin ƙofar, cikin Sa’a kuwa ta jiyo mi Iffah ta faɗa saboda yanda tai maganar da ɗan zafi sai ta fita da ɗan karfi kaɗan. Ƙofar ta fasa bugawa ta koma ɗakinta da baya. Itama dai ƙofar tata ta sanyama key duk da tasan babu wanda zai shigo mata. Kai tsaye wadrob ɗin ta ta nufa, a cikin wani akwatin ƙarfe karami mai ƙyau ta fiddo waya bayan ta danna madannan sirri ya buɗe. Wayar ta shiga ƙoƙarin kunnawa tana mai rufo windows ɗin ɗakin nata. Sai da tai danne-danne kusan na mintuna biyu alamar text ta tura. Kira ne ya shigo, sai a ring ɗin karshe ta ɗaga, batare da jiran wani gaisuwa daga wancan ba cikin bada umarni tace,

“Daga yanzu zuwa safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu ina buƙatar sanin komai akan Zawjata-almilk ta uku. Idan nace komai yana nufin komai da komai”. Kitt ta yanke kiran tana wani irin murmushi tun kan ma ta samu amsar data bukaci sani. Wayar ta kashe gaba ɗaya ta sake maidata inda ta dakkota……

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button