Hausa Novels and Stories

Idon Naira 14

Sponsored links

Yanda take tsananin so da kaunar Aqeel ahaka yake tsananin kaunarta Dan kuwa Sam yanda yake jinta Tunda baigama wayoba yasan son mahaifiya dabam yake shi Kai tsaye yafi jin Zainab din cikin ransa.

Sbd gurinta dayake barci yasa Dole aka siyawa Zainab din lafiyayyan gado aka sanya Mata a dakinta dan kada sanyi ya kamasa da kwanciyar qasa datakeyi ko kwanciyar katifa.

Albarkacinsa ta samu taci suke kwanciya abinsu akan lafiyayyan gado da beddings masu taushi da tsada.,

Ahankali ahankali sai gashi dakin nata an sauya komai an saka Mata AC harma dasu bedside fridge qarami da center carpet masu taushi da tsada duk akan sbd Aqeel dayake wuni gurinta tasamu albarkacinsa tanaci.

Kasancewar kusan daga Kansa Bata Kuma samun cikiba yasa kowa dangin dasu iyayen Aqeel din sonsa yake

Komai na wasa siya Masa ake shiyasa dakinta Dama daki na musamman din da aka cika da jeran tsadaddun furnitures da kayan yara koina kayan wasansa ne da abubuwan koyan karatunsa sbd yafara iya magana sai aketa siya Masa abubuwan koyan karatu Dan bakin nasa yafara qwarewa akan karatu maimakon surutun banza duk da shi din Sam ba yaro bane Mai surutu da rawar Kai Sam ko surutun ma bayayi idan kaji surutunsa to Yana tareda Zainab dinne a daki Tana Masa wasa haka.

Rayuwarta da Aqeel yashigo yasa takejin sassaucin kadaicin rayuwa da damuwar batada kowa da zata Kira nata,

Yaron qaunarta yakeyi sosai kaman itace ta haifesa,

Shaquwarsu tasa Sam baya neman mahaifiyarsa sbd kusan itama Bata zama ta zama maaikaciya sosai Dan haka gabaki daya komai na dawainiyarsa da rayuwarsa Takoma kacokan akan Zainab.

Alokacinda maganarsa ta fita ras Yana iya fadan komai daidai sunan Mami shine abinda yafi qwarewa a ambata Kuma shine Karan Kansa yake Kiran Zainab da hakan sbd Dadynsa da lokuta da Dama yake kiranta da Mamin Aqeel cikin ‘yar raha haka sai Kuma idan yacewa Aqeel din

Hakan yasa Aqeel din yakama sunan tun bai Gama tantance waye mahaifiyarsa a tsakanin Zainab din da Asalin mahaifiyarsaba sbd duk wata shaquwarsa da Zainab da tsananin kulawa da kaunar datake Masa ya wuce Wanda uwarsa ke Masa Dan haka Zainab ta shiga zuciyarsa sosai ta zauna.

A bangaren Zainab dinma Yana sake girma dawainiyarsa Tana sake Mata yawa sbd hatta nonuwanta dasuke tsaye qyam a girke duk sun fara Dan ranqwafawa sbd goyonsa

Gashi yayi nauyi da girma yanzu Amma haka yake hayewa bayanta sai anan yake bacci,

Haka take goyasa ta ringa ayyukanta dashi

Kafin tagama duk ta Gama fita hayyacinta Amma haka take daurewa.,

Haka Kuma Aqeel din yarone Mai matuqar qyanqyamin zabar abinda yake ci Dan kuwa ba komai yake ciba

Wani abin yanaci zai fara ciwon ciki da amai Dan haka ko anan bangaren saida Tasha wuya kafin ta fahimci da kyau abubuwan da cikinsa bayaso Dan haka kusan koyaushe abincin datasan yafi basa lafiya take Masa dabam Dana gidan.

Haka zalika Sam jikinsa bayaso sanyi sosai shiyasa kamar mace kullum qafafuwansa cikin safa masu taushi suke

haka dai ya zamar Mata kaman wani qwai Koda yaushe komai nasa lallabasa akeyi.

Wani sabon Al’amari daya sauya a rayuwarta sanadin renon Aqeel zatace ko riqonsa shine komai na rayuwarta ya sauya yanzu Dan kuwa Alh Asad sosai yake kokarin daidaita matsayinta data Aqeel a gidan sbd ya lura irin kaunar da Aqeel kewa Zainab din matuqar Basu inganta rayuwarta ba ya girma zai iya qullatarsu akan hakan sbd lokuta da Dama ko Aiki takeyi wani time din yakan Bata fuska akan bayaso tanayi din,

Gashi qarfi da yaji baya iya zama taredasu a bangarensu suyi Wasa da dariya irin ta iyaye da ‘da

Har gwara shi akwai shaquwa da kauna tsakaninsa da Dan nasa Amma Maryamah Sam Babu irin wannan shaquwar kaman yanda yake da Zainab.

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button