Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 58

Sponsored links

Malikat Haseena ce ta cigaba da faɗin, “Zamu fara ne da matakai da hanyoyin dinga haɗuwarku daga nan zuwa wani lokaci, fatanmu ki zama mai saka ido a dukkan wani motsinsa, a karan kansa, da duk wasu wanda zasu mu’amulancesa har a cikin hadimai. Kiyi takan tsantsan, dan mutum ne shi mai wayo matuƙa, sannan mai wahalar sha’ani da fahimta. Ba’a gane mi yake nufi ko minene a ransa akan fuskarsa, kar ki yarda ki bashi wata damar da zai iya zargi a kanki. Fatanmu dai ki zama jaruma a dukkan al’amuransa dama na kowa dake a wannan masarauta, duk abinda kikaci karo da shi ba dai-dai ba kiyi maza ki sanar da ɗaya daga cikinmu”.

Zantukan nasu ya saka zuciyar Iffah dinga tsalle-tsalle a kan dalilai biyu

……..Na farko ji a ranta UBANGIJI ya amsa mata addu’ar ta akan burin data shigo da shi Daular ruman. Na biyu minene dalilin waɗan nan mutane na buɗe mata cikinsu?. Na ƙarshe da yafi kowanne razani da ban

mamaki a ƙwaƙwalwarta dama suma sun san shike aikata kisan kenan? Amma suka zaɓi yin shiru saboda ba ƴaƴansu ake halakawa ba kokuwa suma tsoronsa sukeji? A ɗan ƙaramin tunaninta tanaga zasu iya yin amfani da ƙwanji wajen sanin mi Shahan-shan ɗin ke aikatawa musamman Malikat Haseena da Malikat Bushirat. Amma miyasa suka zaɓi yin amfani da ita? Kodai sun gama gane manufarta ne a kansa…..?

“Ibnati!”.

Daneen Ammarah ta katseta daga nisan da tai a tunani ta hanyar kiran sunanta da taɓata. Firgigit kuwa ta kawo ajiyar zuciya. “Karki kasance a dogon nazari, manufarmu ta sakaki a wannan sabgar tana da nasaba ne da dalilai biyu. Na farko juriyarki ta bamu ƙwarin gwiwar kallonki a jaruma. Na biyu jinki wata abu mai muhimmanci da muke fatan nasara ta dalilinta kodan tsallake tarkon masu aikata wannan ɓarna da kika tsallake a harin farko da muke jin shine lagon da aka dinga ɗanawa a farko wajen salwantar da rayukan da suka gabata….”

“Mamy nima zata yuwu bana tsallake bane dan nafi ƙarfinsu, maybe na tsallake ne saboda tsayawarku da fatanku akan ganin na tsallake ɗin. Amma tabbas zan iya sadaukarwa, zan kuma iya bin umarninku badan inajin ƙarfina ya kai ba sai dan kun isa ku bani umarni”.

Su dukansu kalamanta sunyi wani tasiri na musamman a zukatansu tare da ƙawatata a cikin idanunsu. A wani gefen sunyi amanna irinta ɗansu ya dace ya samu tun farko, dan ƙarfin gwiwarta sunyi dai-dai da Zawjata-almilk da akafi buƙata ga kowane Shahan-shan. Sannan Malikat da sukema kansu fata.

“ALLAH yay miki albarka”.

Suka faɗa kusan a tare su duka huɗun. A kan laɓɓanta ta amsa da amin.

Sun cigaba da tattaunawar da gaba ɗaya ta saka Iffah cikin ƙagara, ƙagara mai nasaba da shiga ruɗanin wani furici daga Daneen Ammarah. Wai jiya Shahan-shan ne wanda ya ziyarcesu a wannan falon, tana buƙatar samun filin tunani dan zuciyarta da ƙwaƙwalwarta fa gaba ɗaya sun kulle, ruɗani ya gama mamaye duk wani hangenta da dama bai wuce iya tsayin ƙafafunta da shekarunta ba….

A hankali ta maida ƙofar ta rufe tare da jingina a jikinta ta lumshe ido da sauke numfashi tamkar mai kokawar jawosa. Shin murna zatayi a wannan gaɓar ko kuwa shiga ruɗani?. Idan ance Shahan-shan ne a jiya ta yarda, shi kuma wanda tai gamo da shi a mabanbanta wajeje kafin shigowarta masarauta wanene shi?. Wannan tambaya tafi kowace tambaya girma da girgiza zuciyarta a duk abubuwan dake cin ranta. “Kai nifa nama ruɗe wlhy”.

 

Ta faɗa a zahiri tana zamewa cikin sarewa ta zube ƙasa. Ta jima a wajen cikin halin shiru da ambaton hasbinallahu wa ni’imal wakil ko zata samu dai-daiton komawa cikin hankali dan da gaske komai na halittarta mai motsi ya raunana da rauni mafi ban tsoro da shiga ruɗani. Tsahon lokaci ta kwashe a wajen tana kokawa da raunin zuciyarta da rashin ƙarfin gudanar jini. Fahimtar wancan tunanin na buƙatar lokaci ya sata turesa ta maida hankali akan tattaunawarsu da su Malikat. Tabbas wannan shine babban ƙudirinta dayin ƙundunbalar juriya na tunkarar rayuwar da bata da tabbacin tsallakewa. Duk da tasan anfi ƙarfinta, dama duk wani mai ƙarfi da take kallon ƙarfinta ta zaɓi fuskantar mutum mafi girman iko da tsaro domin ɗaukar fansa. A kwanakin da suka gabata na kasancewarta cikin wannan daula ta fara fidda ran samun cikar burinta saboda dalilai masu yawa. Ciki harda rashin samun koda ƙanƙanuwar ƙofar sanin minene ma daular ruman ɗin ta ƙunsa balle Shahan-shan da kansa. Sai gashi a yau cikin sauƙi an buƙaci kaita inda zuciyarta ta fara raya mata zuwansa ba ƙaramin tsalle bane da ba’a da tabbacin fita idan an shiga, aka kuma sanar mata wani yanki na sirrin daular ruman mai girman gaske da ko na ciki basu san da shi ba ƙila. “Anya babu wani abu a ran mutanen nan saɓanin abinda suka faɗa?” bakinta ya furta a zahiri cikin sake dulmiya a ruɗani. (Koda akwaisa yardar ki dasu ce zata baki ilimin sanin hakan) zuciyarta ta faɗa cikin ƙarfafata da ture raunin dake neman rinjayarta….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button