Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 42

Sponsored links

Shigowar daddy yayi daidai da faduwar khaleel… Kokarin taroshi yayi saidai ina yariga ya kai kasa,cikin tashin hankali daddy ya karasa inda khaleel yake zuciyarsa kamar zatayi tsalle ta fito tsabar tashin hankali,kowa na gidan yasan khaleel ne weak point din daddy,irin son da daddy yake nuna masa abin har tsoro yake bawa yan gidan…….

Ruwa ya shiga yayyafa masa amma abu kamar wasa khaleel yaki farkawa,hakannne yasa sukayi rushing dinsa zuwa asibiti… Ita kanta momma ba karamin rudani tashiga ba, ace daga magana?,wani irin abu ke shirin faruwa da khaleel ne? Gashi akan yarinyar data tsana? Kai inaaaa!!!…

Emergency aka nufa da khaleel while momma da daddy na reception suna jira,gabadaya sun kasa nitsuwa,ko zama sun kasayi sai kai da kawowa sukeyi……

Chan daddy ya kalli momma yace

“Meya samesa da har ya samu attack? Kuma yaushe ya dawo?….

“Shigowarsa part dina kenan,ko gaisawa bamu gamayi ba naga ya fadi,bansan yaushe ya dawo ba”

Momma ta fada tana marairaicewa…..

“Are you sure ba abinda aka masa? Dan nasan baya samun attack saida dalili”…

“Ba abinda aka masa”….

Shiru ne ya biyo baya a tsakaninsu sai kaikawon da suka cigaba dayi kowa da abinda yake yawo a ransa…

 

Ba karamin wahala likitoci sukasha ba kafin su samu bugun zuciyar khaleel ya daidaita,a hakanma zata iya birkicewa any time……..

Suna cikin wannan halin Doctor ya fito da sauri daga emergency ward din,da sauri suma suka nufesa, sai ya musu nuni da su biyoshi ciki kawai…..

Rige rigen karasawa gurin khaleel sukayi,karshe dai daddy ne ya fara zuwa,kama hannunsa daddy yayi yana masa sannu…….

“Dan Allah momma ki fadamin inda take plssss”

Suka tsinto khaleel yana fadin haka cikin muryar marasa lafiya….

Wani mugun kallo daddy yayiwa momma jin khaleel nata sambatu da alama kuma momma tasan komai duk da bai wani gane me yake nufi ba….

Sake ruko hannun khaleel yayi yace…..

“Son, it’s me your daddy, tell me what you want, I promise to get it a ko ina yake a duniyarnan, so tell me?”…..

Dan kallonshi khaleel yayi kamar me neman tantance waye… Chan kuma sai ya ruko hannun daddy sosai yana fadin….

“That pretty girl, meyin shara da daddare, inaso in ganta, momma tace bazan kara ganinta ba, daddy pls help me”……

Cikin rudani daddy ya kalli momma da alamar tambaya, a iya saninsa shi baisan wacce take shara cikin dare a gidanba, toh kodai gamo khaleel yayi ne?…..

Ganin kallon da daddy yake mata ya sata saurin cewa…

“Nima haka ya dinga damuna wai yanaso ya ganta, gashi ni bansan wa yake nufi ba,Allah yasa dai ba aljanu bane suka shafesa dan babu meyin shara cikin dare…….

Gyada kai daddy yayi dan shima yafi tinanin hakan, inko aljanune suka shafi khaleel to tabbas sun shiga uku, abun tashin hankalin kuma abun na taba ciwonsa wanda tashin ciwonsa kuma barazana ne ga rayuwarsa, su yanzu ta ina zasu fara toh?…….

Maganar khaleel ce ta dawo da daddy daga dan gajeran tinanin daya shiga….

“Ba aljana bace, mutum ce, momma tasanta kuma, kawai bataso ta fada ne kuma…….

Sai numfashinsa ya fara seizing,nan da nan likitoci suka rufu akansa,oxygen sukasa masa sannan suka masa allura….. Fashewa da kuka momma tayi tanajin kamar ta fadi gsky dan abin khaleel ya fara bata tsoro,daddy ko girgiza kai kawai yake ya rasa tinanin mai zaiyi, shidai yafi yadda da khaleel gamo yayi har yake tinanin momma tasanta……

Doctor ne ya umarcesu da su biyoshi office sannan anaso abar khaleel shikadai…….

Zama sukayi suna jiran abinda Doctor zaice….

Gyaran murya Doctor yayi ya fara musu bayani

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button