Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 54

Sponsored links

A ɓangaren Malikat Haseena ma yanda Iffan ta kusan raba dare tana juya al’amura a ranta haka itama ta raba dare wasiwasi akan abinda ta fahimta da wanda ta nazarta. Data kasa cigaba da riƙe abinda ke mata kaikawo tana idar da sallar asubahi ta bukaci ganin Daneen Ammarah.

A ɗan rikice ta shigo da tunanin ko ta kwana babu lafiya ne. Ganinta zaune sumul ya sata sauke ajiyar zuciya takai zaune kusa da ita.

“Wlhy Mamma hankalina har ya tashi, nayi zaton ko kin kwana babu lafiya ne”.

Ɗan murmushi tai batare datace mata komai ba. Sai dai ta miƙa mata maganin da ake shafa mata a kafafu. Amsa tai babu musu ta fara shafa mata itama tana murmushin.

“Ammarah mi kika fahimta?”.

Ta jeho tambayar tata kai tsaye ga Daneen Ammarah. Cikin rashin fahimta Daneen Ammarah ta ɗago.

“Mamma akan mi?”.

“Haɗuwar Malik da Zawjata-almilk”.

“Mammah har kin sakani dariya, Miya kawo wannan maganar kuma?”.

“Ke dai amsa mini ita”.

“Ban san mi kike son sani ba Mammah, amma nidai nasararmu da dacewarsu matsayin ma’aurata na hanga tattare da su”.

Murmushi Malikat Haseena ta saki da kauda kanta. “Ni kuma ba hakan kawai na hanga ba”.

Idanu Daneen Ammarah ta tsura mata batare da tace komai ba. Malikat Haseena datai shiru itama kamar bazata cigaba da cewa wani abu ba ta nisa. “A nazarin danai musu tamkar akwai sanayya tsakaninsu kafin haɗuwar jiya”.

“Sanayya kuma Mammah? Idan da na fahimta sun san juna kenan kike nufi?”.

“Haka”.

“Haba Mammah a ina to zasu san juna? Karki manta Abni ba fita yake ba. Ƙaddara ma yana fita, wanda ke zagaye da tsaro ta ina sani da mu’amula mai ƙarfi irin wadda kike hasashe zasu ƙullu tsakaninsa da yarinya mai matsayinta. Karfa ki manta ko’a cikin gidan nan ba kowa ya san fuskarsa ba balle talakawan dake rayuwa a waje”.

“Wannan shine abinda ya ɗaure kaina nima. Sai dai azuciyata na faɗamin akwai abinda yake ba daidai ba da saninmu tabbas”.

“Kamar mi kenan Mammah?”.

“Nima amsar da nake nema kenan”.

Babu wanda ya iya sake cewa komai sukai shiru kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa……

Alhamdullah Barrister yaci nasarar gano inda su Babiy suke, sai dai ba’a jiya ba kamar yanda ya faɗama su kaka har suka zauna zaman jira sai da sukaga yamma tayi babu wani bayani sannan suka haƙura suka wuce. Bai ɓata lokaci ba kuwa yay kiran Abu Zainab ya sanar masa. Shima cike da zumuɗi ya nufi gidan Babiy domin sanar ma Kaka. Sai dai kuma ya tarar yaje masallaci kasancewar lokacin sallar zuhur yayi. Dole ya shanye zumuɗin nasa shima ya tafi masallacin. Bayan an idar da salla ƙofar masallaci ya fito ya tsaya yana kallon duk mai fitowa.

Daga can ciki kuwa Kaka dake a cikin mutanen da suke sahun farko sai a karshe suka sami damar miƙewa suma. Ya ɗaga zai miƙe mutumin dake a kusa da shi ya bashi hannu alamar suyi musabaha. Babu musu ya miƙa masa nasa yana ɗan murmushi. Mutumin da shima murmushin yake ya tsaida kwayoyin idanunsa a tsakkiyar na kaka, hakan yasa shima Kaka cigaba da kallonsa dan ya fahimci akwai wani abu…

“Nasan kasan girman alkairi tsoho. To karka yarda ka maida shi da sharri ga wanda yay maka. Dan haka ina baka shawarar hana waɗan can mutanen biyu cigaba da shiga abinda bai shafesu ba. Inba hakaba kuwa kai da su kuna gab da zuwa inda surukinka da jikanka suke yanzu. Na Barka lafiya”.

Mutumin ya kare maganar da zare hanunsa a cikin na Kaka ya miƙe. Da kallo kawai kaka ya bisa harya ɓacema ganinsa. Kafin yaja numfashi ya fesar tare da miƙewa zuciyarsa na faman kaikawo tamkar zata fito. Koda ya fito da Abu Zainab ya fara cin karo, ya tsira masa ido na wasu sakanni kafin ya karasa garesa. Abu Zainab da shima ya hangosa cike da zumuɗi ya tarbesa, ko gaisawa basuyi ba ya rankwafa dai-dai kunnen kaka ya gwargwaɗa masa saƙon Barrister…

Murmushi kaka ya saki na ƙarfin hali, sai kuma ya jinjina kansa da ambaton Alhamdullah a hankali. Abu Zainab da bai gama fahimtar yanayin kakan ba cike da zumuɗi yace, “Baba muje Barrister na jiranmu yanzu haka”.

Idanu kaka ya tsira masa tamkar zai ce a’a. zuciyarsa na tuna masa girman alkairinsu garesa, tabbas bazai so saka rayuwarsu a gariri su da iyalansu ba, idan ma yaga wani zai zama sanadi zai bada karfinsa wajen karesu. Kalaman wancan mutumin sun sake tabbatar masa akwai lauje cikin naɗi game da kama su Babiy, hakama ƙin amsar Ummu a asibiti waccan ranar. Hakan na nufin kuma duk kaikawon da suke ana biye da su…….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button