Hausa Novels Complete Documents

Daudar Gora Book 1 Page 41

Sponsored links

Kai kawai Kaka ya jinjina masa da faɗin, “ALLAH ya saka muku da alkairi, haka ake fatan zaman makwaftaka, domin ita makwaftaka tanada ƙarfin da zata iya fin ƴan uwantaka muhimmanci ma a wani ɓangaren. Yanzu gashi abu ya samesu, kafin mu muzo kun basu ɗauki, da bakwa zaman lafiya kuma hakan bazai yuwuba. Dan haka duk wani mutum na ƙwarai daya san kansa ya dace ya rayu da maƙwafcinsa lafiya da ƙaunar juna”. “Hakane Baba, ALLAH ya saka da alkairi. Bara na shigo da shi”. Murmushi Kaka yayi da jinjina masa kai. Koda suka shigo tare da ɗan uwan nasa shima ya gaida Kaka da girmamawa, hakama Iyyani da har yanzu ke faman sharar hawaye tana tofama Ummu addu’a. Damar duba Ummun Kaka ya bashi dan haka ya shiga aikinsa. Ya tabbatar musu jinin Ummu ya hau matuƙa, amma zai mata allurar barci ta samu nutsuwa dan barinta a ido biyu akwai haɗari komai zai iya faruwa. Sai da suka maida Ummu ɗaki sannan ya saka mata ruwa da allurai aciki, cikin sa’a kuwa babu jimawa barci yay awan gaba da ita. Sosai Kaka yay musu godiya da sanya albarka, dan ko sisi ɗan uwan nasa bai amsaba ma…….

An wayi gari da samun canji sosai a yanayin Iffah, dan zuwa yau kam Alhmdllh. Sai dai jikinta dake wani irin saɓa saikace wata macijiya. Sai kuma rauni data tsinci kanta a ciki sakamakon mummunan mafarkin datai akan su Babiy daya haddasa mata matsanancin faɗuwar gaba da akai-akai. Gata dai iya gata tana gani wajen tsohuwa Malikat Haseena duk da bata da lafiyar ƙafa sai a wheelchair take komai. Hakama Daneen Ammarah tsaye take kan Iffah, yanda take kula da ita yasa Iffah jin ƙaunarta batare data san dalili ba, ganinta take tamkar Ummu. Yanda ake tsaye kanta da gata da kulawa yasa ko damar yin ƙwaƙwaran tunani bata da shi, dan da tayi shiru Daneen Ammarah zata nuna damuwa taita jera mata tambayar mike damunta? Ko tamanin wani abu ne a jikinta har yanzu?. Dole take sassauta damuwarta, sai dai tayi matuƙar dagewa wajen ambaton UBANGIJI kamar yanda Babiy da Ummu suka dinga jaddada mata a nasiharsu ta ƙarshe gareta. Labarin mutuwar hadiman da suka kai mata rigar nan ta saka yazo kunenta itama, sai dai jin sanadin mutuwar tasu ya tsaya mata a rai matuƙa, harma ta rasa yaya zata fassara al’amarin…

 

Bayan idar da sallar isha’i tana zaune tayi tagumi gaba ɗaya hankalinta ya tattara ga tunanin iyayenta da mummunan mafarkin daren jiya a kansu Daneen Ammarah ta shigo hadimai uku biye da ita. A bakin gadon takai zaune tare da kai hannu ta janye tagumin da Iffah tai. Nannauyan nunfashi ta sauke da ɗan ɗagowa ta kalla Daneen Ammarah ɗin, sai kuma ta maida kanta ta risinar da mata sannu da zuwa. Daneen Ammarah dake kallonta cikin damuwa taja numfashi ta fesar batare data amsa ba. Dai-dai nan Hadiman da suke tare suka zube gaban Iffah bayan sun ajiye kayan hanunsu. Gaisheta suke da tsantsar girmamawar da ko iya ɗaga kawunansu basayi su dubi sashen da take. Sam Iffah batajin daɗin yanda suke matan saboda bata sababa, a ranta gani take kamar ƙasƙancine. Hannu Daneen Ammarah ta kaɗa musu alamar suje, zumut suka miƙe tamkar ƙyaftawar ido suka fice. Iffah ta bisu da kallo cike da jin raɗaɗi a zuciyarta.

“Ibnati!”.

“Na’am Mamy!”.

Iffah ta amsa cike da girmamawa ga Daneen Ammarah. Sosai sunan da Iffah ke kiranta da shi ke raunanata da sake jin ƙaunar yarinyar, dan a bakin mutum ɗaya tak take jinsa kafin ita. Taja numfashi da haɗiye hawayen da suka cika mata ido ta maye gurbinsu da murmushi.

“Ibnati bana son cigaba da ganin damuwar nan a fuskarki, ki kwantar da hankalinki insha ALLAHU babu abinda zai sake samunki. Wanda ma ya sameki ki ɗauka kaddararkice kinji, amma inaji a jikina insha ALLAH kece mabuɗin nasararmu, ke ce hasken da zata haska mana duhun da muke a ciki a Daular nan kinji”.

Kai Iffah ta jinjina a hankali, haka kawai take jin matuƙar nutsuwar kasancewa da wannan baiwar ALLAH, sam batajin irin zafi da tsanar da takema duk wani mai alaƙa da masarauta a kanta. Kallonta take tamkar wata katanga ta wani babban al’amari dake tunkarota. “Mamy bana tare da damuwa in har kina a kusa dani, duk abinda ya sameni kuma dama ALLAH ya ƙaddara sai ya sameni koda banzo nan ba. Ina tunanin su Ummu ne da jin tsananin kewarsu saboda mummunan mafarkin danai akansu jiya, ina tsoron kar wani abu ya samesu ne suma?”.

 

Cike da jin tausayita Daneen Ammarah ta shafa kanta, “Duk ɗa na gari dolene ya kasance cikin kewa a lokacin da yay nesa da ahalinsa, da ace inada dama da a yau sai na kaiki kinga su Ummunki. Amma dokar masarauta ce Zawjata-almilki tana fitane kawai bisa ƙwaƙwaran dalili, zuwa gidansu kuwa tana yinsa ne sau biyu tak a shekara, ɗaya a sirrance, ɗaya a bayyane tare da rakkiyar hadimai. Shiko mafarki ai na gaskiya bane Ibnati, MANZANNI ne kawai idan suka yisa yake gaskiya a garesu, amma mu namu yakanzo da wasu sigogi ciki harda sheɗanu”.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button