Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 18

Sponsored links

Fareedah!”.

Da sauri ta juyo jin muryar Sir Fawzan daya sauke numfashi da dafe kansa na tabbacin ya jima yana nemanta. “Ina kika shigane wai? Tun ɗazun sai faman zagaye garden ɗin nan nake ni da securitys nemanki, ga wayarki ma taƙi shiga sam”. Maimakon ta bashi amsa sai ta zube a kujerar dake a kusa da ita ragwaf. A wahale tace “Sir ka bani ruwa nasha Please”.

Sosai yanayinta ya sake neman firgitashi, amma fahimtar ruwan tafi buƙata ba tambaya ba ya sashi barin wajen da ɗan hanzari. Mintuna ƙalilan ya dawo da robar ruwa. Miƙa mata yay bayan ya ɓalle murfin. Tunda ta kafa kai bata koja numfashi ba sai da ta sha fin rabi, ta sauke robar tare da dafe goshinta tana sauke ajiyar zuciya a jajjere. Lokaci ya bata sosai ta samu nutsuwa kafin ya kai zaune a kujerar dake facing ɗinta.

“Fareedah miya faru wai? Ina kika shiga? Duk kin tadamin hankali saboda security sun tabbatar min kin shigo”.

A hankali ta ɗago manyan idanunta da launin farinsu ya sirka ta zuba masa. Sai kuma ta janye da sauri tana girgiza kanta dan fuskar mutumin nan kawai ta gani a tare da shi saboda ta sakama ranta aljani ne. Idanunta rumtse tare da yakice tunanin ta sake buɗesu akansa. “Sir lokaci ya ƙure ina abokin naka?”.

Ya fahimci bata son bashi amsa, sai kawai ya girgiza mata kai. “Rashin ganinki ya sakani a ruɗanin da har ya kira waya ban sani ba, sai daga baya na lura na kirashi shima kuma bai ɗaga ba”.

“Ya ALLAH, shike nan itama wannan damar ta kufce min!”.

“Bazamuce haka ba sai munji ta bakinsa, a yau ne dai kawai nake ganin bazai yuwu ba gaskiya, kodan ke a karan kanki ma. Kinga saura baifi mintuna arba’in ayi magrib ba. Kije gida, insha ALLAHU zanbi duk hanyar data dace domin ganin kin haɗu da shi”.

Kallonsa take kamar zatai kuka. Sai dai saka zantukansa a ma’aunin hankali ya sata kasa cewa komai.

“Kiyi haƙuri”.

Ya faɗa cikin sake sanyaya murya yana mata wani lallausan kallo. Kauda nata idon tai daga kansa, taja iska ta fesar da jinjina masa kanta kawai. Dan ta tabbatar inhar tai magana kuka ne zai iya ƙwace mata ma…..

Gurfane take a gaban Uwa kamar yanda dokar take ga duk wanda ke binta. Duk da matsayinta da girmanta a cikin daular ruman a gaban uwa ita ba komai bace face mai neman biyan buƙata (Wa’iyazubillah). Kamar ko yaushe tsohuwar da suke kira uwa sanye take cikin jajayen kaya, sai dai saɓanin waccan ranar yau inuwarta kawai ake iya gani a jikin bangon ɗakin. Amma abin mamaki babu tsoro ko wata shakkar hakan a idanun hamshaƙiyar matar. Inuwar uwa ta kece da mumunar dariyarta mara daɗin saurare, kai kace za’a iya jinta a duk faɗin masarautar, sai dai abin mamaki iya ita ɗin kawai take jinta. Sai da tayi mai isarta kafin ta tsagaita tamkar ba’ita tayin ba.

 

“Ta-ƙurya alƙawarina ya cika, zaku iya tunkarar kowa a yanzu da maganar auren Malik-alMuluk babu mai musa miki hatta Malikat da shi a karan kansa balle duk wani mai faɗa masa yaji. Sai dai akwai banbanci a wannan karon da baya. Hhhhhhhh!!”.

 

 

“Umarninki shine abin jira Uwa mai share kukan mai kuka”.

 

“Hhhhh Ta-ƙurya shiyyasa bana baƙin cikin taimakonki, zan kuma cigaba da taimakonki kiyita na sara keda duk mabiyanki. Ragamar kasancewar gida a hanun wasunki bashine zai sa su zama masu ƙarfin ikoba sama da naki. Ki shiga ki fita a haɗa gagarumin aure na bajinta tsakanin wannan yarinya da Malik-alMuluk. Hakan zaisa su shagaltu da tunanin komai ya canja musamman shafe watanni tara da Zawjata-almilki da suka rage suka kwashe gidan nan batare da ko ciwon kai ba. Ina son ki nuna bajinta irin wadda ko Malikat bazata yiba, Daular ruman zata cigaba da kasancewa a tafin hanunki a baɗini koda a zahiri kinada wanda suke nuna sunfi ƙarfinki. Ranar mako zata zama ranar sa’a Hhhhhhhh!!!”.

 

Sautin dariyar ya cigaba da nesa da kunuwanta har inuwar uwa ta ɓace. Nannauyan numfashi ta sauke tare da murmushi mai nuna tsantsar farin ciki. Ta dubi ƙyaƙyƙyawan farin tafin hanunta da jini keta kaikawo tana sake maimaita kasantuwar daular ruman a tafin hanunta da uwa ta ambata mata. Tabbas ita ɗin mai sa’a ce, sa’ar da zata iya nunata a gaban duk wasu sa’ointa koma wanda suka ɗarata. Fatanta kawai ALLAH ya kaita ranar cikar burinta gaba ɗaya domin tabbatarma kowa dake cikin Ruman ma ba daular ruman kawai ba *Saka ƙwan kaza bashi ke nufin mallakar akurki ita ɗaya ba* sannan zuwan *mai guri bashi ke tabbatarda naɗewar mai tabarma ba*…….

Kwanaki biyu kenan Iffah bata sake neman sir Fawzan ɗinta ba, ta kuma kashe wayarta ta yanda shima koya nemeta bazai sametan ba. Ita tasan dalilin zaɓar yin hakan, duk da yanayinta ya nuna tana da damuwa dan babu walwala tattare da ita sam tun baro garden ɗin da tayi. Yau ma data kasance bazataje makaranta ba kamar yanda ta saba ta tashi taya Ummu aiki, sai dai yanda take komai kamar mara laka a jiki yasa Ummu nutsuwa a nazartar ta..

 

“Wai lafiyarki kuwa Iffah? Tun dawowar fitar da kikai shekaran jiya duk kin wani canja. Ko jikin naki ne?”.

 

 

“A’a Ummu, kawai dai kaina na ɗan mun ciwo ne ƙasa-ƙasa. Amma na san barci ne da bai isheni ba”.

 

“Barci kuma? To miya hanaki barcin?”.

 

In’ina ta fara na rashin sanin abinda zata faɗa. Sai kuma tai ƙasa da kanta ganin yanda Ummu ta kafeta da idanu. Ummu mace ce mai yawan tsantseni wajen tarbiyyar ƴaƴanta. Komai tana binsa a sannu babu garaje ko gaggawar akan tafida yaranta tun kafin sukai haka, shiyyasa cikin sauki take iya sanin matsalolinsu da saurin fahimtar sabuwar hanya da suka ɗauka saɓanin wadda ta sansu da shi. Yanzu ma dai ɗauke kai tai ga Iffah ta cigaba da hidimar gabanta batare data sake magana ba. Daga baya ma saita ƙirƙiri jan Iffah da sabuwar hira da bata da alaƙa data farko. Tun Iffah na ɗararewa har ta saki jikinta…

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button