Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Hausa Novel Chapter 58

Sponsored links

Wani lissafi ya kumayi yaga alamun komai ze tafi masa daidai , abinda zeyi shine ya kai yarinyar gidansa ya ajye sai ya dawo ya renawa sameer hankali yace shi dayazo bega kowa ba…. “Yes” ya fada yana kokarin daukarta…..

Daukarta yayi kamar wata yar baby a zuciyarsa yana fadin gata dai a haka kamar a cike amma she’s weightless, kodai batacin abinci sosai ne?, tsaki yaja yana tamabayar kansa ina ruwansa?….

Carefully yake rike da ita gudin having body contact da ita amma duk da haka be tsiraba dan yanajin dumin jikinta sosai kamar wanda yake rungume da ita, haka ya daure ya karasa bakin mota da ita….

Bude gaban motar yayi ya zaunar da ita still tana nan a sumen da take, sannan ya kwantar mata da sit din sosai yanda zataji dadin kwanciyar ya kuma gyara mata zaman hijabinta…..

Bude gate yayi kasancewar babu me gadi a gidan tinda ba wani zama suke ba, ya fita da motar waje sannan ya kara dawowa ya rufe gate da gidan gabadaya ya nufi mota…..

Kamar a mafarki yaga mutum ya bude masa gaban mota harda zira hannu yana kokarin zaro ta…….

Saida jijiyoyin wuyarsa suka fito tsabar bacin rai, toh shikuma wannan dan rainin hankalin daga ina?….

 

Fincikosa yayi da karfi sannan ya hankadasa chan gefe, cikin bacin rai da takaici Deen yace;

 

“Who the hell are you da kake kokarin zaro min mata daga mota? You must be very stupid”….

 

Tasowa yayi da sauri yana kakkabe jikinsa, cikin jin haushi shima yace;

 

“Kai ya kamata in tambaya ina zaka kaimin mata, dagayin tafiyar kwana biyu shikenan saiku sata a gaba?, bame tabamin ita ya zauna lafiya wallahi!!!”….

 

“Ji wani shashasha mahaukaci, a masallacin ubanwa aka daura muku auren da zakace matarka ce, kai dalla ware dan wallahi ka bari na fusata sai na zubar maka da hakoran gaba duka, ba kunya ba tsoron Allah kazo kuna claiming matar mutane!”….

 

Deen ya fada yanajin kamar ya daddalla masa mari, saidai bata wannan yake ba, burinsa kawai ya gudu da yarinyar kafin sameer ya dawo, gashi wani dan iska yazo ze rena masa hankali ya bata masa lokaci …..

 

“Idan kana san rayuwarka ka bani matata mu tafi”…..

 

Deen besan sanda ya zabga masa wani wawan mari tsabar bacin rai jin ya kara maimaita kalmar matarsa ce, ko a gidan ubanwa aka daura musu aure oh……..

 

Wata muguwar dariya ya fashe dashi yace….

 

“Ni ka mara? Hhhhh karshen ka yazo yaro”…

 

Wani marin ya kara masa dan ba karamin haushin dariyar yaji ba, sannan cikin masifa yace;

 

“An kara maka wani, do your worst karamin dan iska kawai, now bani hanya!”….

 

Yana fadin haka ya shige mota yasa lock, kokarin tada motar yayi mota tace to tadani kagani, babu kalan dabarun da beyiba amma shiru mota taki tashi, jin yana juyo dariyar dan iskan chan ne yasasa whining glass dan yaga meyake yiwa dariya….

 

Yana bude glass din ko yajuyo shi yana fadin;

 

“Hhhhhh kai ka dauka zaka mareni har so biyu kaci bulus? Inaaa, ai in fadamaka kome zakayi motarnan bazata tashi ba, bama motar ba babu inda zaka iya motsawa daga nan inba bani matata kayi na tafi ba”…..

 

Wani agogon sameer me tsada da yake cikin motar Deen ya dauka ya cilla masa a goshi, a take goshin ya fara zubar da jini, murmushi Deen yayi yace;

 

“Ka kara kiranta matarka a gurin nan wallahi saina kasheka, na kuma kashe banza a banza! Wato kai shedani ko? Toh ko bude idonka da kyau kaga yanda zan bar gurinnan da ita akan idanunka, duk shaidancin da kakeji dashi na fika wallahi”……..

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button