Hausa Novels and Stories

Wace Ce Ita Book 2 Chapter 68

Sponsored links

“Bawani abinda ta dauka, dududu yaushe muka shigo gidan? Kuma ko kwaso kaya ba’ayi a mota ba haryanzu, kawai muguntarsa ce, ai babu abinda baze iya ba”…..

Unbelievably umm ta kalli Deen tace;

“Saif dagaske kai kama yatsunta daya bayan daya ka ciza?”…..

Dagowa yayi yana kallon baby tee mamakinta na kara kasheshi, shi ya rasa gane meke damunta, wauta ce ko makirci ne, wato bazata kyale ba shine taje ta fadawa mami ya cijeta sai kace yaro karami, ita kuma mami dake ta riga ta masa bakin penti ta hau ta zauna akai, girgiza kai yayi yace;

“Umm I have no idea what she’s talking about, nida nake bacci anan”….

“Nima abinda nagani kenan, I met him sleeping here, yanzu nace ya tafi ma”…

Umm ta fada tana kallon mami….

Karap baby tee tace;

“Kafin ya fara bacci fa ya cijeni, tundazu fa nashigo”…..

“Umm karya takeyi ni ban cijeta ba”….

“Wallahi ya cijeni, har a kafa ma”….

“Ta ina ake cizan mutum a kafa?”…

“Ta inda kabi ka cijeni mana”….

Tsawa umm ta daka musu tace;

“Dalla kuyiwa mutane shiru! Wa kuka maida shashasha daze zauna yana sauraron shashancinku, sa’anki ne da zakina masa rashin kunya? Yana fada kina fada a gabanmu? Kai kuma jiya kazo kace ta fita munje munga tana bacci, ke kuma yau kinzo kin fadi abinda hankali baze dauka ba, wai ya cijeki a duka yatsu da kafa, toh duk ku kama kanku wallahi sannan daga yau zan baku last warning, kar wanda ya sake zuwa ya tunkaremu da shirmensa, ku wuce ku bawa mutane guri, marasa da’a kawai!”…..

Barin parlourn sukayi dukansu, Deen yayi hanyar waje ita kuma baby tee ta haura sama sai kumbure kumbure take……

“Gaskiya ki dena min haka umm, yarinya da gaskiyarta zakiyi disregarding abu”…..

Mami ta fada tana zama gefen umm….

“Bawani gaskiya a maganarta, ki dena biyemusu dan Allah, wayen’nan biyun sai su sawa mutum hawan jini”…..

“Bawani nan, ni dai ina bayan namesake”….

Mami ta fada tana dariya…..

Murmushi umm tayi tace;

“Au abun hakane? Nima sai in koma bayan saif dina”…..

“Hahaha dama ai a bayansa kike tintini, jiya daya kawo kara ai kin binshi kingani, sai yau za’a gwale min ya”…..

“Lamarin baby tee ne harda rashin kunya mami, ni kuma banasan haka shiyasa kikaga ina tsawatar mata, kuma shima saif din ai na hada dashi”…..

“A duki mutum a hanashi kuka ba, wani rashin kunya tayi? In shi be zubar da girmansa ba ai bazata renashi ba”…..

Umm zatayi magana kenan wayarta ya fara ringing…..

“Ameen ne ke kira, ko sun karaso ne”…

Ta fada tana amsa wayar…..

Sauke wayar tayi da farinciki a fuskarta ta kalli mami tace;

“Sun karaso fa, amma sunyi transit a kano, yanzu zasu karaso abuja”…..

Dariya mami tayi tace;

“Masha Allah, yau anna zataga dan autanta”…..

“Wallahi kuwa, bari ince saif ya fara shirin daukosu kafin su karaso”…..

“Eh yaje ya jirasu kawai”….

Kiranshi umm tayi a waya ta sanar masa, amsawa yayi da toh sannan ta kashe wayar….

Tana kashe wayar kiran Abby ya shigo mata, silencing wayar tayi ta sakata a do not disturb batareda mami ta sani ba…..

Saida umm da mami suka kara inspecting gidan suka tabbatar komai is in place kafin suka tafi shiryawa, saida mami ta biya ta bedroom din baby tee tace ta sake wanka ta shirya itama dake lokacin ankawo kayanta daga fashion house din mami….. Wanka tayi ta shirya cikin wani newly designed abaya daya burgeta, sosai kayan suka amsheta kuwa kamar dan ita akayi…….

Saida Deen ya kira umm ya sanar da ita kafin ya tafi, kamar tace su tafi da baby tee wata zuciyar tace kar suje suyita rigima, kawai ta mishi Allah ya kiyaye hanya ta kashe wayar…..

Tinda suka kira Deen yace musu sun shigo layin gidan suka fito suna jiran isowarsu a harabar gidan, dake yan maiduguri sai bayan isha zasu karaso, kana kallon fuskar kowannensu kasan suna cikin madaukacin farinciki har da baby tee da ranar zata fara ganinsu itama, gwarama umm dake ko last year sunje gurinta a England, mami ko tafi 5 years bata gansu, anna da bappa har sun gaji da complain din ameen yaki zuwa da iyalinsa…

Horn akayi me gadi ya tashi ya bude gate da sauri, tun kafin Deen ya daidaita parking suka karasa parking space, fitowa sukayi su twins sukayi kan baby tee suka rungumeta kamar sun santa, rungumesu tayi itama tanajin sonsu aranta tashin farko….

Hada umm da mami uncle A yayi ya rungumesu, cikin zolaya yace;

“Bari in fara rungume yan kannena tinda twins sun kanainayemin ya”….

Mintsininsa mami tayi tace;

“Dan rainin hankali zakaga kannenka kuwa, ni sakeni mu gaisa da ruwaida”….

Sakesu yayi sukaje suka rungume kyakkyawar matarsa ruwaida suna mata sannu da zuwa….

Sultan da yake kaninsu twins, shekara daya taakaninsu ya janye su twins daga jikin baby tee sannan ya rungumeta yana fadin;

“Ku kadai zakuyi hugging dinta ne, I miss you so much sis”…..

A take baby tee taji ya shiga ranta shima, rungumeshi tayi itama tana dariya tace;

“I miss you too bro”….

Dariya duka yan gurin suka sa ganin yanda sukayi kamar sun dade da sanin juna, banda deen daya rintse ido ya shige ciki…..

“Come hug me too baby”….

Uncle A ya fada yana bude mata hannu…

Sakin sultan tayi ta tafi ta rungemeshi…

“Nifa daughter?”….

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button