Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 74

Sponsored links

Sautin ƙarar takun takalman ƙafarta da mayataccen ƙamshin tiraren da shi kaɗai aka sani da shi ya sashi tsayawa cak daga ƙoƙarin kai hannu a abincin da aka gama haɗawa gabansa. Fararen idanunsa tar-tar tamkar madara ya ɗago ya sauke a kanta. Hakama hadiman dake a tsaye ta gefe da gefensa kawunansu a ƙasa cikin yanayin mutuwar tsaye data rikesu suka zube ƙasa kan gwiyawunsu illahirin jikkunansu na ƙyarma akan dalilai guda biyu. Na farko ganin tabbatar da wadda suka gama fidda rai da jiran tsammanin ganin an shigo fidda gawarta tamkar Zawjata-almilk na baya dai na raye ɗin kamar yanda Hadimar ta gano. Na biyu ƙamshin turaren jikinta da ga mutum ɗaya tak ake iya jinsa a duk faɗin ƙasar ruman ma bawai a daular ruman ba…

Tamkar Iffah bata fahimci halin da suke a ciki ba ta ƙaraso cikin katafaren falon batare data dubi ko ɗaya a cikinsu ba balle mai gayya mai aikin. Cikin sauri ɗaya daga cikin hadiman ya miƙe ya gyara mata kujera, zaune ta kai tana mai dubansa a karo na farko. Tuni shi kuma ya maida kansa ga abinda yake yi tamkar bai san da zuwan tan ba. Ta taɓe baki da juya idanunta ta maida ga hadimar dake ƙoƙarin fara haɗa mata abincin. Nunin abinda take buƙata tai mata da ɗan yatsa. Hadimar na kammalawa ta koma cikin ƴan uwanta ta tsaya itama kanta a rirrine.

Gaba ɗaya jinta take a takure, kwarjininsa ya cika ko’ina a falon. Cikin dakewa da kaucewa gizago sa ta ɗan ɗago ta ɗan saci kallonsa da nufin gaishesa idanunta suka shige cikin nasa da ya ɗago da nufin kallon nata…

“Who are you?”

Ya fara faɗa cikin basarwa yana kaɗa idanusa da har yanzu ke cikin nata tamkar bashi yay maganar ba. Badan a idanunta tausasan lips ɗinsa suka motsa wajen ambaton wacece itan ba zata iya gaddamar hakan. Kaifin idanunsa sun neman sage duk wani ƙwarin gwiwarta. Ƙoƙarin fara sassauta nata idanun tai yunƙurin yi cikin ƙanƙance su sannu a hankali. Shima sai ya kankance nasa kamar yanda takeyi, fuskarsa na sake tsukewa babu alamar sassauci tattare da ita. Nata ta fisga da ƙarfi ta lumshe su, sai kuma ta buɗe a kansa tana mai sake tsuke tata fuskar itama, bazata iya jure salon nasa ba dake neman ƙone ƙudirinta, dan haka ta kauda kanta gefe babu alamar zata bashi amsar da yay yunƙurin ji daga garetan..

“Barka da safiya”.

alamar zata bashi amsar da yay yunƙurin ji daga garetan..

“Barka da safiya”.

Ta faɗa a ƙoƙarinta na basar da tambayarsa ta farko.

Bai motsa ba, babu alamar kuma zai amsa ta. Hakan sai ya sake sukar zuciyarta harta ɗan saci kallonsa, da sauri ta kauda idanunta, dan da gaske fuskarsa ruguza mata lissafi take, da gasken gaske shi ƙyaƙyƙyawa ne, irin ƙyawun dako a cikin ƙasar tasu ake yabawa da shi, koda yake batai mamakin hakan ba, dan Malikat Bushirat ba’a magana, duk da girma ya fara zuwa gareta tsantsar ƙyawunta a bayyane yake. Hakama Malikat Haseena dake matsayin kakarsa data haifi babansa tunda ita dai bataga baban nasaba ko’a hoto har yanzun, amma zubin Malikat Haseena dana Daneen Ammarah ya tabbatar mata shima ɗin dai zai kasance ƙyaƙyƙywan ne……

“What is your goal in life?”.

Kalmomi guda shida suka katse mata tunani a bazata. Ta kallesa tana ƙoƙarin danne mamakinta kan waɗan nan tambayoyi da yake faman yanko mata kai tsaye. Ganin yanda ya zuba mata ƙasaitattun idanunsa masu firgita mara gaskiya ta janye nata tana yamutse fuska. (Damarki ce wannan) wata zuciya ta ayyana mata. Cike da gamsuwa ta sake kauda kai gefe dan har yanzu tanajin kaifin idanunsa a kanta. “Ni ban kasance kowa ba sai talakar dake a ƙarƙashin mulkinka ranka ya daɗe. Abinda nake son cimmawa kuwa a rayuwata irin abinda shugaba ke fatan cimmawa ga talakawan ƙasarsa ta hanyar mulkarsu da fuska biyu ne”.

Yanda tai maganar kanta tsaye babu ko ɗar ya sashi jin mamakinta. (Tabbas wannan abar ba mutum bace) zuciyarsa ta tabbatar masa. A zahiri sai ya ɗauke kansa cike da basarwa. Shiru babu alamar zai sake tankawa har Iffah tama fidda rai ta cigaba da tsakurar abincinta kamar yanda yakeyi shima.

“Wasa da rayuwarki kuskurene ga ƙarfin halinki, ƙin kasancewar ki tarihi a wannan safiyar bashi ke tabbatar miki nasarar tsallakewa ba”.

A yanzun kam zantukansa sun zama masu matuƙar tasiri a fitarsu da saurarensu gareta, jin bazata iya dannewa ba ta amsa batare data ɗago ta kallesa ba,

“Hakane shugabana, sai dai fa _Fate is some thing undeniable”_

Ya basar babu alamar yanzu ma zai amsa, shayin sa ya kai baki cike da ƙasaita. Itama sai bata sake cewa komai ba ta cigaba da cin abincin tana mai kallonsa ta gefen ido, sannu-sannu tabi sautin motsa plate ɗin gabansa da kallo har kan lallausan farar fatan hanunsa masu ɗauke da tsaftatattun fararen dogayen farce, baya tai ƙoƙarin jan jikinta batare data yarda idanunta sun wuce kallon hanun nasa ba. Yanda ya basar da ita ɗin kuma sai yay matuƙar sukar zuciyarta, dan bata buƙatar tattaunawar tasu ta tsaya iya haka. Amma sai bata yarda fuskarta ta nunaba. Sai ma mamakin ƙasaita da tsantsar izzar wannan bawa da zuciyarta ke faman yi. A wani ɓangaren ita kanta dakewa kawai take, amma kwarjininsa da gizago na firgita ta matuƙa. Tana ƙara tsarkake sunan ALLAH akan yarda da jinin mulki gaskiya ne. Duk da ta shigo daular ruman da wani ƙudiri a ranta hakan bazai hanata girmamashi ba, koda ace tayima yunƙurin hakan kwarjinsa bazai bata damar yin saɓanin girmamawar da kowa ke masan ba. So take taji tsanarsa a ranta kamar yanda takeji kafin ganin wannan fuskar matsayin shi amma zuciyarta taƙi bata haɗin kai. Numfashi taja a hankali ta fesar a ƙasan maƙoshinta.

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button