Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 101

Sponsored links

Kamar bazai tanka masa ba sai kuma ya amsa shi da faɗin, “Boss baya nan, ganinsa kuma abune bamai sauƙi ba dan bana jin ma yana ƙasar. Karka damu idan yana buƙatar magana da kai zai zo da kansa basai ka nema hakan ba”. Daga haka yay ficewarsa. Jiki a sanyaye Barrister ya bisa da kallo harya maida ƙofar zai rufe yay saurin faɗin, “Na roƙeka kota wayane ka haɗamu, da gaske maganar da zanyi da shi nada matuƙar muhimmanci, da kuma buƙatar yinta da gaggawa”.

Jimm saurayin yay yana kallon Barrister ɗin daga inda yake, sai kuma ya ɗan rausayar da kansa da faɗin, “Okay duk yanda mukai zan dawo”.

Baifi mintuna biyar da fita ba sai gashi, har lokacin Barrister na zaune a inda ya barsa. Ya miƙa masa wayar hannunsa. Cikin jin daɗi Barrister ya amsa. Shi ya fara sallama da gaisuwa batare da la’akari daya girmi boss ɗin nasu ba. Amsa masa akai daga can a taƙaice, nan ma bai nuna ya damu ba cikin tashin hankali ya fara maganar dake cimasa rai..

 

“Alhmdullah na cika umarninku, sai dai sakamakon dana samo ya matuƙar rikita tunani na. Dan wannan case ɗin case ɗin da nake yine, kuma a dalilinsa naje ƙauyen Lufana. Yanzu kuma sun bani aiki akan kaina, Ina cikin ruɗani sosai, dan na gagara fahimtar manufarku ku da su, shiyyasa gaba ɗaya ruɗani ya kasa barina na fahimci abinda ya dace na fahimta….”

 

“Karka damu kanka da son sai ka fahimta Barrister. Kai dai kai musu aikin da suka buƙata, basu bayanai akan naka da case ɗin kawai”.

“Idan nai haka zan saka rayuwar bayin ALLAH ne a haɗari, wlhy mutanen na mutanen kirki ne komai an shiryashi garesu ne bisa wata manufa. Ina matuƙar jin tausayinsu, an rabasu da ƴaƴansu har uku, an kuma biyo ta wata hanyar rusasu da shine nake son ma san dalili, yanzu kuma ace nine da hannuna zan miƙasu, idan nai hakan bazan taɓa yafema kaina ba”.

“Baka da wani zaɓi bayan hakan Barrister. Idan kuma ka shirya rasa iyalanka ne fine”. Kitt aka yanke wayar. Barrister dake jin hajijiya na ɗan kwasarsa ya dafe bango da sauri yana mai ambaton sunan ALLAH domin neman ɗauki…

Yau kwanaki huɗu kenan da rashin ganin Sayyid Khairul-Bashar, kwana shidda kuma cur da kai Iffah sashen Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed. Sosai masarautar a harmutse take, yayinda ƙananun magana da rikice-rikice ke neman tashi a dalilin fitar zantukan da Sayeed Khairul-Bashar ɗin yayi kan Tajwar Eshaan a daren da za’a rasashi.

Nan fa kowa ya shiga yima al’amarin fashin baƙi da ga ɓangaren masu faɗa ajin gidan, wanda kai tsaye kusan mafi yawansu sun karkata zarginsu ne da kalaman da Tajwar Eshaan yayi shi kuma..

Duk abinda ke faruwa sarai yana isa kunensa, sai dai abin mamaki yayi biris kamar yanda ya saba. Yayinda shirun nasa ke ƙara wutar al’amarin matuƙa a tsakanin ahalin gidan baki ɗaya. Rashin daɗin maganganun da ke neman kawo bore ga mulkin Shahan-shan ɗin kai tsaye ne ya tada hankalin Malikat Bushirat matuƙa ta nema ganawa da ɗan nata, dan tun ana yi iya su ahali har abu ya zagaye masarauta yana neman fara fita waje.

 

 

Bayan mintinan da basu gaza talatin ba amsa daga Tajwar Eshaan ta dawo ga Malikat Bushirat cewar baya buƙatar ganawa da kowa. Ranta ya matuƙar ɓaci da wannan amsa, dan take ta kori dukkan hadimanta ta shiga Safa da marwa. Tasan kota kirashi bazai ɗaga ba, kuma tunda yace bai buƙatar ganawa da kowan ta san halinsa har zuciya baya bukatar hakan. A kaikawon nata Iffah ta faɗo mata a rai, babu ɓata lokaci a karo na biyu ta bukaci ganinta duk da kuwa sune sukai mata katanga da sake baro sashen Tajwar Eshaan tun a waccan fitar acewarsu har sai ta cika kwanakin bakwai ciff.

 

Iffah na zaune a ƴar barandar da takan sha iska da nazarin littattafan data maida hankali saƙon na Malikat Bushirat ya risketa, ta ɗanji mamaki, amma sai ta shanye a ranta kawai, dan tun washe garin kwananta na biyu Malikat Haseenat ta kirata a waya da kanta ta sanar mata karta sake cewa zata baro sashen Tajwar ɗin har sai kwanakin bakwai sun cika. Haƙuri ta bada bisa kuskurenta, daga ranar kuma ta haƙura duk da a takure take matuƙa da zaman, ganin ranta zaita ɓaci ma a banza sai ta maida hankalinta ga nazarin littattafan nan data ɗibo a books room, ko shi Tajwar Eshaan ɗin ma sai ta ƙulla wasan ɓuya da shi, dan tun faruwar tashin bomb ɗin nan ta riƙesa a rai, sai kuma maganar ɓatan Sayeed Khairul-Bashar da a yanzu aketa dangantashi da shi ya ƙara tabbatar mata da shi mutumin banza ne….

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button