Hausa Novels and Stories

Buri Daya Complete Hausa Novel

Sponsored links

Iya lafiya kuke kakkamta kaya rana tsaka?

 

 

 

Harara iya talatu tafara watsawa dattiya dake tsaye har lokacin kafin tace,

 

 

 

Rashin hakurinsa yakaisa ga daukar takalmin ZAKI NEYO yasa yaje yawon maula aka hadosu da miyagun karnuka sukaiwa takalmin fatafata…..

 

 

 

Kallon babansu tayi cikeda takaicin Rashin danganarsa da ako yaushe baya jawo musu alkhairi sbd fargaba da tsoron masifar daya jawo musu basujiba basu ganiba ta turo baki tace,

 

 

 

Nikam baba meyasa bakason ko yaushe a zauna lafiya agidannan gashi yanzu mutum saiya kwana biyu bai wani dogon motsiba sbd tashin hankalin yaya neyo

 

Yanzu wlh ko mai neman aurena yazo qofar gidannan saiya gwammaci karo da mahaukacin matashin kare akan fushin wannan abin daka yi baba.

sake dosowa cikin gidan atake ya aje butar ya miqe sukai ido hudu da Nadia dake zaune tana kallonsa cikeda tausayin kanta na aikin daya data.

 

 

 

Cikeda borin kunya ya dauke Kai daga kallonta ya nufi dakinsa da iya talatu yashige bai tsaya wanke dayar qafarba tunanin qila Zaki ne yadawo duk da yasan Zaki Sam baya fito sbd tsabar mulkin dayake murzawa a dabanci Dan ko wani hakimin bai kaisa baza mulkiba atasa duniyar ta ‘yandaba Wanda shiyasa ake kiransa da sarki Zaki.

 

 

 

Itadai iya talatu Bata sake kallonsa ba sbd tana lureda duk hankalinsa duk ba kwance yakeba sbd abinda yayi din Saidai bazatayi masa mgn ba qyalesa zatayi ai zakin shine daidan kowane dan banza na gidan Dana waje.

 

 

 

Cigaba tayida hada garin kayan matanta tana daurawa a leda batareda ta kalli ko inda take zaune Yana qoqarin shafawa qafafuwan nasa Vaseline kamar Wanda zaije wani gurin.

 

 

 

Lalah ne yashigo gidan Yana fito daukeda wata baqar leda ta kayan neyo daya daya karbo masa guga sbd akwaisu da babbar hidima sbd AMBY DIKKO DILLA na gari Kuma zakinsu shine babban yaronsa dayafi yarda dashi da boyayyun ayyukansa.

 

 

 

Dakin zakin dake farkon shigowa ta zauren gidan ya shiga ya ajiye masa kayan kan katifa yafito ya jawo qyauren dakin.

 

 

 

Harzai fice ya dakata tareda juyowa da sauri ya kalli Nadia dake riqeda takalmin Zaki da aka siyo masa daga kaduna….

 

 

 

Baki ya sake cikeda mamaki da tantama ya dawo gabanta ya tsaya Yana kallon hannunta dake riqedasu Yana rawa alamar amatuqar tsorace take.

 

 

 

Cikin tsananin mamaki da muryarsa irinta riqaqqun yan ta’adda yace”

 

 

 

Wannan meyene a hannunki?? Yana nunawa da hannunsa sbd sanin ba magana takeyiba.

 

 

 

Jikinta har wani irin rawa yakeyi sbd tsananin halinda zuciyarta da gangar jikinta suke ciki hannu na rawa ta daga zata nuna qofar dakin babansu saita tuno da gargadinsa tayi saurin sauke hannu tana sake qanqame takalman.

 

 

 

Amasife yace”

 

 

 

Ke ubanwane yace ki shiga dakin sarki harki dauko wannan takalmin Dan……zaro manyan jajayen idanuwansa yayi sbd sai alokacin ya lurada yanda suke ya hadiye wani yawu cikin jinjina mata yace”

 

 

 

Wlh idan ko sunana yafito acikin Wainda suka gani saina qarasa mayarda maraji bayan Rashin magnar dakike fama dashi.

 

 

 

Ficewa yayi Yana jinjina mata Dan kuwa ba qaramin jarumtar tabama takalmin tayiba.

 

 

 

Yana fita qofar gidan atake ya tseguntawa Nanu Yana cewa”

 

 

 

Babahh yaufa akwai saukar aradu a cikin gida da anguwarnan mubi ahankali Dan kuwa yau antabo sarki inda ba’a tabowa.

 

 

 

Cikin gidan kuwa jiki a salube ta tashi ta sidada dakinsa ta ajiye daga ciki bakin qofa tadawo cikin gida taci gaba da aikin tuwon iya talatu na siyarwa da dare jikinta amatuqar sanyaye Dan har wani zazzabi takeji.

 

Mamuh

agaresu sunyi nasarar qwace mulkin shiga da fice na duk wani baqin mai ta hanyar ruwa Wanda yasa gobe sukeda babbar hidimar bikin murna Wanda alh dikko yasaki wasu mahaukatan kudi aka tsara shiyasa kawai yau baiyi wani daukar matakiba duk dai za’a Dan koyawa baban hnkali badan haka ba wlh da yau kowa saiyaji ajikinsa ko dukiyarsa.

 

 

 

Qarfe goma da arbain baba yataso daga gurin fira yayo gida Yana shigowa Kai tsaye ya nufi butar dake bakin gurin wanke wanke Yana juyowa yayi ido hudu da bingo Yana wani irin shesheka Yana zaro harshensa dake dalalar yawun dake nuna tsantsar ha’darinsa.

 

 

 

Butar saki cikin tsananin tashin hankalin dabai saniba yace”

 

 

 

Ya salamu,,,ya azzizu….Wai menake gani haka..ke talatu…ke talatu..Nadiya.. Nadiya Zaki fito kosainaci gidanku idan nasameki.

 

 

 

Wani irin tsalle bingo yayi

 

Bai direba baba yayi wurgi da buta ya nufi dakin Yana isa qofar yajita gam alamar iya talatu ta rufe Dan dama tasan wlh Zaki bazai bar babanba

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button