Hausa Novels and Stories

My Lady Boss 15

Sponsored links

Shiru Hajiya Juwairiyya tayi tsawon lokaci kana ta buɗe murya da ɗan ƙarfi tana kirar Hajara ! Hajara!! Cikin sauri wacce aka kira Hajara ta fito tana zubewa gaban ta da cewa ” Na’am Hajiya Gani .

Ga sabuwar ma’aikaciya nan na ɗauka , ki nuna mata bedroom ɗin Son ta gyara . Tare da gabatar mata da duk aikin gidan da tsare tsare”. Anan zaki rinƙa kwana ko can gida zaki na rinƙa komawa?”. A’a gida zan rinƙa komawa da safe na rinƙa zuwa”.

To naji amma yau ki koma gobe idan kin zo bazaki koma ba sai jibi, saboda dawowar babban mutum Alh DR Abdullah yana hanya Khamal kuma zai taho yau!.

Wani irin dammm ƙirjin Sumayya ya buga a zuciyar ta tana cewa ” Wani Khamal ɗin , ohk na gode Hajiya Allah ya saka da alheri. Yowa kuje ,shine Amsan da Hjy Juwairiyya ta basu Hajara na gaba Sumayya na bin ta a baya’.

Tsayawa tayi tana kallon Hoton shi ,wanda take jin zazzafan So da ƙaunar shi a zuciyar ta , a hankali takai hannun ta tana sauke farin galashin idon ta , kana ta shafa hoton ɗan nata tana cewa ” I love You my lyf. Allah yaƙara karemun kai yayiwa Rayuwar ka Albarka. Hajiya Sarah ke maganan tana murmusawa kaman wanda Ɗan nata Fahad ke gaban ta. Shigowa Ma’aikaciya na ta tayi na hannun daman ta ,tana ƙarasowa gaban ta , wanda a zuciyar ta cewa take ” Wuuuu Ranan da aka wayi gari Fahad ya mutu ko wani Abu ya faru dashi ƙila Hjy Sarah zaucewa zatayi ko itama ta mutu ta bishi…kullum yana aikin kallon hoton shi , sai kace mara abinyi ? Don Allah yabaka ɗa ɗaya tilo ai bai kamata ki ɗauki son duniya ki ɗaura masa ba ,gashi yaron ma ba ji yakeyi ba , aikin sa kenan lalata ƴaƴan jama’a kuma kin sani amma kike take sani.

Barka da hutawa hjy Sarah, ga ƴan matan can an kawo maki a ƙasa”. Juyowa tayi a hankali hannun ta ɗauke da wani cup da Fahad ne yayi zanen kansa , kissing ɗin cup ɗin tayi tana cewa ” I love You mah Son , Ina sonka so Mai yawa yaro na ….

Tana maganan tana murmushi , kana tace ur Dad is own his way to come back ,zai dawo abroad ya kamata ka dawo gida Nigeria ohk? . Tana maganan kaman wanda aka ce mata ga Fahad a gaban ta. Ɗan tsaki Dije taja a zuciyar ta ,wanda kamin ta farga taji masifan Hajiya Sarah tana cewa ” Ke sau nawa zan faɗa maki Idan kin ganni tare da Yaro na ko Hoton shi kar ki rinƙa mun ko wanni magana sai na gama abin da nake yi? Wannan ai shashanci ne ! .

Kiyi hƙr Hajiya”. Mtswww tsaki taja a hankali tana juyawa tare da nufan Down stairs don ganin kyawawan ƴammatan da ta kawo mawa ɗan nata , a cewan ta Fahad baxai taɓa zama a Nigeria ba mata ba , wannan dalilin yasata sawa a nemo mata kyawawan ƴammata ta xaɓa nashi , bata damu da lalatan da yakeyi da su ba. Ita bata damu daga nan ya ga wata yace zai Aura ba ,burin ta kenan a rayuwa , taga ta ɗauki jikoki yaran Fahad da hannun ta.

Wani irin rantsatstsen material ta saka a jikin ta , mai launin jah da baƙi yana walwali fatar jikin ta a goge yake , abun ka ga farar mace , fuskar ta kuwa yasha makeup na zamani bakace ita ta haifo yaro saurayi ɗan shekara 30+ kaman Fahad ba.

Zama tayi akan royals ɗin falon masu masifan tsada tana bin ƴammatan dake ta aikin karkaɗa kaman wanda aka ce masu itace Fahad ɗin . Sunyi wani irin sexy shiga mai fidda tsaraici wai adole wannan shine wayewa….

Tun subahin fari Sumayya tana kimtsa wa kamin gari yayi haske ta nufo gidan su Sir Khamal wato gidan hjy Juwairiyya…yana yin yanda taji gidan shiru ya tabbatar mata da dawowan gogan ,don taji labarin halinshi da yanda kowa ke shiga taitayin shi idan ya dawo …sai dai ta matsu ita kanta ta ganshi taga waye shi da yake sa kowa na gidan tsorata?”. Sasan Hajiya Juwairiyya ta nufa kaman yanda ya kasance itace mai gabatar masu da abinci don karin kumallo….ba ta tadda kowa a falon ba , sai Tsirarun ƴan aiki biyu mata…gaishe su tayi tana nufar kitchen don da’alama hjy Juwairiyya bata fito ba….

 

 

 

 

 

 

 

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button