Hausa Novels and Stories

Daudar Gora Book 1 Page 8

Sponsored links

Daga roundabout ɗin ana iya hango ƙaton tambarin ƙosashen zaki da akayisa da gold na tambarin Masarauta. Iffah taja wani kakkauran tsaki da ɗauke kanta zuciyarta na mata zafi. Harta kusa tsallakawa ta hango wata tsohuwa dake riƙe da wani yaro da Uniform a jikinsa da alama titin take so su tsallaka amma sunata inda-inda. Karan farko murmushi ya suɓuce mata ganin yanda yaron ke jan hanun tsohuwar sai sun tafi kamar zasu tsallaka saita fisgo yaron su dawo baya tana masifa. Sallama tai musu, tsohuwar ta amsa mata. Ta gaisheta da girmamawa tare da faɗin, “Ammi kuna so ku tsalla ne?”.

Iffah ta sake murmusawa daga cikin niƙab ɗinta, kafin takai hannu ta riƙo na tsohuwar dake riƙe da yaron ita kuma. Suna gab da kaiwa tsakkiya yaron ya fisge hanunsa ya koma baya da gudu yana faɗin yabar abunsa a baya. Tsohuwar zata fisge itama tana masifa da kiran yaron ya dawo Iffah ta riƙeta gam suka karasa tsallakawa. “Ammi yi haƙuri barsa naje zan sake tsallako miki da shi. Rufe bakin Iffah yay dai-dai da taka wani bahagon birkin daya bada sautin ƙuuuuuu!!!. Sai sautin fitar ƙara mai razanarwa ta biyo bayansa.

Wani irin zabura Iffah tai na juyowa dan ƙarar har tsakkiyar kanta ta jita. Ai batama san sanda ta yaye niƙab ɗin fuskarta ba da waro manyan ƙyawawan idanunta waje gaba ɗaya ba tana mai ambaton sunan ALLAH ganin yaron nan tsaye cak a tsakkiyar titi hancin wata mota gab da shi allamar kaɗan ya hana ayi ɗanyen aiki. Kusan a tare suka isa kansa ita da tsohuwar data fashe da kuka da ƙwala kiran sunan yaron a matuƙar firgice.

Iffah da jikinta ke ɓari ta riƙo yaron jikinta tana duddubashi da sauke ajiyar zuciya a jajjere, ganin babu ko ƙwarzane a jikin nasa. Saurin sakin yaron tai ga tsohuwar tasha gaban motar ranta a ɓace ganin mai motar ko fitowa baiyiba ya ɗan leƙone kawai, ganin baima yaron komaiba ya maida kansa yanama ƙoƙarin barin wajen. A fusace ta buɗe murfin, ba saurayin daya kasance drivern motar ba hatta wanda ke gefensa hankalinsa akan lap-top dake saman cinyarsa sai da ya ɗago suka zuba mata idanu. Gaba ɗayansu ta haɗa ta dallama harara da manyan idanunta masu matuƙar haske tamkar madara.

 

“Kai malam baka san darajar mutane bane?….” Zazzaƙar muryarta mai taushi da nutsuwa a cikinta ta daki kunnuwansu cikin faɗa babu ko ɗigon tsoro a tare da ita. Batare data damu da yanda suka zuba mata ido ba ta murguɗa musu bakinta da sake dalla musu harara ta cigaba da masifarta, “Ka kusan bige yaro amma tsabar kanka ba’a daidai yake ba shine koka fito kaga yaya yake ma saboda ku masu kuɗin nan ɗaukar talaka kuke baida banbanci da titin da kuke gurza tayoyin banzayen motocinku da kuka saya da kuɗinmu”.

Drivern ya faɗa da maɗaukakin mamaki Iffah.

 

Harara ta sake dalla masa da zira hannunta ta zare key ɗin motar daya riga ya kashe tun ɓuɗe musu murfin da tayi.

 

“K! K! Dalla bani key kajimun fitsararriyar yarinya kinga mun taɓashi ne?”.

 

“Anƙi a bakun, wlhy duk sai kun fito kun dubashi kun bama kakarsa haƙuri zan baku key ɗin nan, inba hakaba sai dai mu kwana anan.”

 

Hannu saurayin ya kai da nufin warto key ɗin taja baya, sai dai duk da haka saida yaɗan taɓa skirt ɗinta kaɗan. Cikin matsanancin ɓacin rai ta jinjina yatsarta a kan fuskar matashin tamkar zata tsone masa ido. “Idan hanunka ya sake gigin taɓa koda hijjab ɗin jikina ne sai na karyashi, Sannan koda Shahanshan ne yay wannan aikin bai isa barin wajen nan ba balle kai shashasha driver”.

 

“K!!”.

 

Na gefensa ya faɗa cikin matuƙar waro idanu. A karan farko wanda ke hakimce zaune a sit ɗin bayansu lap-top a cinyarsa da tarin takardu a gefe da gefensa ya ɗago ƙyawawan idanunsa dake tattare da matsananciyar gajiya da ƙosawa yana yamutsa fuska. Baya ganin yarinyar, sai dai duk abinda take faɗa raɗam a kunensa zazzaƙar muryarta ke sauka. Baiko kalla yaran nasa ba ya sauke Lap-top ɗin dake cinyar tasa tare da kai hannu ya buɗe murfin. A tare suka zabura, sai dai kafin suyi wani yunƙuri harya fita a motar. Dolo suka fito suma da sauri………..✍

Sponsored Links

Leave a Reply

Back to top button